JAMB
Majalisar Wakilan tarayya ta yanke shawarar gudanar da bincike kan tangarɗar na'ura da aka samu yayin tantance sakamakon dubban ɗaliban da suka zana UTME 2025.
Sakamakon kura-kuran fasahar na'ura da aka samu, sama da dalibai miliyan ɗaya da rabi suka kasa samun sama da maki 200 a UTME 2025. JAMB ta dauki mataki.
Gwamnatin Kano ta kashe sama da N3bn domin daukar nauyin jarrabawar WAEC, NECO, NABTEB da NBAIS ga dalibai 141,175 da suka ci jarrabawar tantancewa a Kano.
JAMB ta saki sakamakon UTME 2025. Fiye da dalibai miliyan 1.5 sun samu kasa da 200, 420,415 sun samu sama da 200. Ana iya duba sakamako ta yanar gizo ko SMS.
JAMB ta fitar da sakamakon UTME 2025, ta riƙe na dalibai 39,834 saboda kura-kurai. Ana binciken dalibai 80 bisa maguɗi, inda Anambra na kan gaba a wadanda ake zargi.
Hukumar JAMB mai.shirya jarabawar samun gurbin shiga jami'a a Najeriya, ta yi wa tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi, kan zargin ana wahalar da dalibai.
Peter Obi ya bayyana cewa, akwai rashin tunani wajen bayyana yadda ake tura dalibai rubuta jarrabawar JAMB da sassafe duk da yanayi da ake ciki na tsaro.
Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta ce za ta zakulo daliban da suka yi hazaka a jarrabawar JAMB din da ta dauki nauyi, domin a zaba masu wasu manyan makarantu.
Hukumar shirya jarrabawar JAMB da UTME ta bayyana yadda ta samu tattaro N9,013,068,510.69 daga daliban kasar nan, inda aka tura akalla Naira biliyan 6 zuwa gwamnati.
JAMB
Samu kari