ADC Ta Kara Karfi a Kano, Tsohon Gwamna Ya Bi Sahun Kwankwaso bayan Barin APC
- Jam'iyyar APC mai mulki a jihar Kano ta samu koma baya bayan ficewar wani tsohon sanata daga cikinta
- Sanata Kabiru Gaya wanda ya taba wakiltar Kano ta Kudu ya sanar da yin murabus daga APC a cikin wata wasika da ya aika
- Tsohon sanatan ya bayyana dalilan da suka sanya ya raba gari da jam'iyyar APC wadda ke mulki a tarayyar Najeriya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Tsohon sanatan da ya wakilci Kano ta Kudu a majalisar dattawa, Sanata Kabiru Ibrahim Gaya, ya yi murabus daga jam'iyyar APC.
Sanata Kabiru Gaya ya sanar da komawarsa jam'iyyar ADC bayan ficewa daga APC mai mulki.

Source: Facebook
Kabiru Gaya ya yi murabus daga jam'iyyar APC
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa wasiƙar murabus ɗinsa na dauke da kwanan wata 5 ga watan Afrilu, 2026.
An aika wasikar ne zuwa ga shugaban APC na gundumar Gaya da ke ƙaramar hukumar Gaya ta jihar Kano.
Tsohon ɗan majalisar ya bayyana cewa matakin nasa zai fara aiki ne nan take, jaridar Daily Nigerian Hausa ta kawo rahoton.
Kwankwaso, Gawuna sun hade a APC
A ranar 30 ga Maris, ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a zaɓen 2023 a jihar Kano, Nasiru Yusuf Gawuna, shi ma ya fice daga jam’iyyar a hukumance.
Daga baya Gawuna ya koma jam’iyyar ADC, inda ya gana da jagoran ƙungiyar Kwankwasiyya, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso.
Meyasa Kabiru Gaya ya bar APC?
Kabiru Gaya ya bayyana cewa ya ɗauki wannan matakin ne bayan "natsuwa da shawarwari masu faɗi," yana mai cewa barin APC ya dace da muradun mutanen da yake wakilta da kuma ra'ayinsa na kansa.
"Ina miƙa godiya ta ga jam'iyyar saboda damar da ta ba ni, da kuma haɗin kai da zumuncin da aka nuna mini tsawon shekaru."
- Sanata Kabiru Gaya
Shugaban APC a gundumar Gaya Arewa, Adam A. Adam, ya tabbatar da karɓar wasiƙar tasa.
Gaya na da alaka mai kyau da Kwankwaso
Kabiru Gaya ya tabbatar da komawarsa ADC, yana mai ƙara da cewa yana da kyakkyawar alaƙa da Kwankwaso da Gawuna.

Source: Facebook
"Na kwashe shekaru takwas masu kyau a wannan jam’iyyar, kuma na kasance Sanatan Kano ta Kudu inda mutane suka ga irin rawar da muka taka. An kafa APC ne a kan kyawawan ƙa’idoji, amma yanzu ta kauce."
"Tsawon shekaru takwas APC tana kan turba. Amma yanzu rashin tsaro ya mamaye ko'ina. A lokacin mulkin Buhari, rashin tsaro yana yankin Arewa maso Gabas ne kawai, amma yanzu ya bazu a daukacin ƙasar nan.”
- Sanata Kabiru Gaya
Kwankwaso ya magantu kan takara a 2027
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa a 2023, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi magana kan neman kujera a zaben 2027.
Kwankwaso ya ce yanzu ba maganar takara ne a gaban manyan jagororin ADC ba, abin da suka fi mayar da hankali a kai shi ne waye zai zo ya kawo sauyi a kasar nan.
Ya ce ko bai samu takara ba, zai cigaba da zama a jam'iyyar ADC domin ya shiga jam'iyyar ne don ba jama'a damar taka rawa a siyasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

