Kwankwaso Ya Magantu kan Takarar 2027 da Zama Mataimakin Obi a ADC
- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi hira ta musamman game da rikicin da ya bulla jam'iyyar ADC bayan sauya sheka daga NPPP
- Rabiu Musa Kwankwaso ya yi magana kan takarar zaben 2027, inda aka masa tambayoyi kan yiwuwar zama mataimakin shugaban kasa
- Hakan na zuwa ne yayin da 'yan siyasa da dama ke shirye-shirye domin samun nasara a zaben 2027 a matakai daban-daban a kasar nan
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - A wata hira ta musamman da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi bayan sauya sheka zuwa ADC, ya yi magana kan makomar siyasar Najeriya.
Kwankwaso ya bayyana cewa yana yi wa 'yan Najeriya, musamman 'yan Arewa da Kano da ke shiga jam'iyyar tun bayan sauya sheka da ya yi fatan alheri.

Source: Facebook
Legit Hausa ta tattaro bayanan da Kwankwaso ya yi ne a wata hira da aka yi da shi da DCL Hausa ta wallafa a shafinta na Facebook.
Rabiu Kwankwaso zai zauna a ADC
Sanata Rabiu Kwankwaso ya bayyana cewa abin farin ciki ne yadda 'yan Najeriya ke cigaba da rajistar shiga jam'iyyar ADC bayan sauya sheka.
Kwankwaso ya sanar da cewa wasu na gani kamar ba zai iya hada kai da wasu 'yan siyasa ba, amma yanzu sun zama tsintsiya madaurinki daya.
Yayin da ya ke fatan kafa gwamnatin ADC a 2027, Kwankwaso ya ce:
'Ina kira ga masoya dimokuradiyya su shiga cikin wannan jam'iyya tamu."
Kwankwaso ya sanar da cewa zai cigaba da zama a ADC duk da rudanin da ake samu, inda ya ce 'yan Najeriya INEC take yi wa aiki kuma za ta gyara abin da ta fada kan ADC.
Ya bukaci wadanda suka sauya sheka da su hada kai da shugabanni domin gudanar da taron jam'iyya lami lafiya cikin nasara.
Kwankwaso zai yi takara a 2027?
Sanata Rabiu Musa Kwnakwaso ya yi karin bayani game da batun takarar 2027 duk da cewa ya hadu da wasu masu son takara kamar Peter Obi da Atiku Abubakar.
A kan takara, Kwankwaso ya ce yanzu ba maganar takara ne a gabansu ba, abin da suka fi mayar da hankali a kai shi ne waye zai zo ya kawo sauyi a kasar nan.
Da aka tambaye shi ko zai zama mataimakin Peter Obi, sai ya ce:
"Me ya sa ba ka ce Ameachi ba, me ya sa ba ka ce Atiku Abubakar ba, sai ka ce Peter Obi?"
Ya kara da cewa su dai fatansu kawai shi ne a samu kawo cigaba ba wai bata lokaci wajen cewa wane shi ne kaza ko kaza ba.

Source: Facebook
Ya ce ko bai samu takara ba, zai cigaba da zama a jam'iyyar ADC domin ya shiga jam'iyyar ne don ba jama'a damar taka rawa a siyasa.
Abba na zawarcin Ibrahim Shekarau
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya fara zawarcin tsohon gwamnan jihar, Malam Ibrahim Shekarau.
A 'yan kwanakin nan wasu manyan APC sun fara nuna alamun Malam Ibrahim Shekarau zai koma jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.
A farkon makon nan ne Ibrahim Shekarau ya gana da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a jihar Legas a hutun Easter da ya ke yi a can.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


