Jihohin Arewa 6 da Jam'iyyar APC Ta Karbe Ikon Majalisarsu daga 2025 zuwa 2026

Jihohin Arewa 6 da Jam'iyyar APC Ta Karbe Ikon Majalisarsu daga 2025 zuwa 2026

Jam’iyyar APC ta samu gagarumin ƙarfi a majalisun dokokin wasu jihohin Arewacin Najeriya tsakanin shekarun 2023 zuwa 2026, sakamakon sauya sheƙar gwamnoni da ‘yan majalisa daga wasu jam’iyyu zuwa APC.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Sauye-sauyen shekar 'yan majalisu zuwa APC ya sanya jam’iyyar ta karɓi ikon majalisun jihohi shida, kamar yadda wannan rahoto zai yi bayani a kai.

Jam'iyyar APC ta kwace ikon majalisar dokokin wasu jihohi a Arewa.
Majalisar dokokin jihar Kano (hagu), da tutar APC (tsakiya) da majalisar dokokin jihar Plateau (dama). Hoto: Naanlong Gapyil Daniel, Hon Jibril Ismail Falgore, Nentawe MEDIA Advocates
Source: Facebook

Karfin jam'iyyar APC a jihohin Najeriya

Tun da fari, wani rahoto na jaridar The Nation ya nuna cewa sauya shekar Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara daga PDP zuwa APC ta sanya jam'iyyar ta zama mai iko a jihohi 31.

Yayin da aka samu wannan sauyi, PDP yanzu ta koma mai iko a jihohin Oyo da Bauchi kawai, kuma har ana jita-jitar cewa shi ma Gwamna Bala Mohammed zai bar jam'iyyar zuwa APC ko ADC.

Kara karanta wannan

APC ta karbe ikon majalisa gaba daya da mamban PDP tilo ya koma jam'iyyar

A wannan rahoto, Legit Hausa ta yi nazari kan jihohin Arewacin Najeriya da jam'iyyar APC ta karbe ikon majalisar dokokinsu bayan sauya shekar 'yan majalisu.

Jihohin da APC ta karbe ikon majalisun su

Ga jerin jihohin da abin ya shafa:

1. Jihar Kano

APC ta samu rinjaye a majalisar Kano bayan 'yan majalisa 21 sun sauya sheka daga NNPP.
Zauren majalisar dokokin jihar Kano. Hoto: Kamal Ibrahim Hotoro
Source: Facebook

A jihar Kano, ‘yan majalisar dokokin jihar 22 sun sauya sheƙa daga jam'iyyar NNPP zuwa APC, lamarin da ya sauya yanayin siyasar majalisar gaba ɗaya.

‘Yan majalisar sun sanar da sauyin ne a watan Janairun 2026, kwanaki kaɗan bayan gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, ya sanar da ficewarsa daga NNPP, in ji rahoton Punch.

Da wannan sauyi, Legit Hausa ta ruwaito cewa APC ta samu rinjaye mai ƙarfi tare da karɓar cikakken iko a Majalisar Dokokin Jihar Kano.

2. Jihar Zamfara

A Zamfara kuma, a watan Maris, 2026, kakakin majalisar dokokin jihar, Bilyaminu Moriki, tare da wasu ‘yan majalisa 12, suka sauya sheƙa daga jam'iyyar PDP zuwa APC.

Moriki ya sanar da matakin ne a zaman majalisar da aka gudanar a Gusau, inda ya gabatar da wasiƙun ficewa daga PDP a madadin ‘yan majalisar.

Kara karanta wannan

Jerin 'yan siyasar da suka shiga ADC bayan sauya shekar Kwankwaso

Sauyin ya zo ne jim kaɗan bayan gwamnan jihar, Dauda Lawal, ya sanar da sauya jam’iyyarsa daga PDP zuwa APC, abin da ya bai wa APC damar karɓar iko gaba ɗaya a majalisar dokokin jihar, in ji rahoton daily Post.

3. Jihar Adamawa

A Adamawa, APC ta zama jam’iyyar da ke da rinjaye a majalisar dokokin jihar bayan ‘yan majalisa 15 daga PDP suka sauya sheƙa zuwa APC a watan Fabrairun 2026.

Daga cikin wadanda suka sauya shekar har da kakakin majalisar, wanda ya karanta wasiƙar ficewar su daga PDP a zaman majalisar, a cewar rahoton TVC News.

‘Yan majalisar sun bayyana cewa rikice-rikicen cikin gida da ke addabar PDP ne ya sa suka yanke shawarar sauya sheƙa, lamarin da ya bai wa APC damar samun rinjaye a majalisar dokokin jihar.

4. Jihar Gombe

A jihar Gombe, Legit Hausa ta ruwaito cewa APC ta ƙara ƙarfafa ikonta a majalisar dokokin jihar bayan ɗan majalisar adawa na ƙarshe ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar.

Hon. Yakubu Daniel, wanda aka fi sani da Shetiman Bare, mai wakiltar mazabar Billiri East, ya sauya daga PDP zuwa APC a watan Afrilun 2025, in ji rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

"Najeriya za ta kama da wuta," Timi Frank ya fito da kuskuren INEC gabanin 2027

Sanarwar da daraktan yaɗa labaran gidan gwamnati, Ismaila Uba Misilli, ya fitar ta ce sauyin wani ɓangare ne na jerin sauye-sauyen da wasu ‘yan majalisar adawa suka rika yi zuwa APC, wanda ya sa majalisar dokokin jihar ta kasance ba tare da wata jam’iyyar adawa ba.

5. Jihar Taraba

A Taraba, APC ta karɓi ikon majalisar dokokin jihar bayan kakakin majalisar, John Bonzena, tare da manyan shugabannin majalisar da sauran ‘yan majalisar PDP suka sauya sheƙa zuwa APC.

Sauyin ya faru ne a watan Nuwamban 2025, inda ‘yan majalisar suka danganta matakin da rikice-rikicen cikin gida da ke addabar PDP a matakin ƙasa, in ji rahoton Business Day.

Bayan sauyin, majalisar dokokin jihar mai mambobi 24 ta zama gaba ɗaya karkashin APC, abin da ya tabbatar da cikakken iko ga jam’iyyar a majalisar.

6. Jihar Plateau

APC ta kwace ikon majalisar dokokin jihar Filato bayan sauya shekar kakakin majalisa, Gabriel Dewan
Zauren majalisar dokokin jihar Plateau. Hoto: Naanlong Gapyil Daniel
Source: Facebook

A jihar Plateau, APC ta samu iko a majalisar dokokin jihar bayan kakakin majalisar, Gabriel Dewan na jam’iyyar YPP, ya yi murabus daga mukaminsa a ranar 2 ga Yuli, 2025.

Bayan murabus ɗin, ‘yan majalisar suka zaɓi Hon. Nanloong Daniel na APC, wanda a baya ya rike mukamin shugaban masu rinjaye, a matsayin sabon kakakin majalisar, in ji rahoton AIT Live.

Kara karanta wannan

APC na shan matsin lamba kan takarar 2027, an yi gargadin rikici zai barke

Zaɓen ya ƙara tabbatar da rinjaye da ikon APC a majalisar dokokin jihar mai mambobi 24, musamman bayan hukuncin kotu da ya soke nasarar ‘yan majalisar PDP a baya.

Jihohi fiye da 30 sun koma hannun APC

A wani labari, mun ruwaito cewa, Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP zuwa jam'iyya mai mulki ta APC a ranar Juma'a, 27 ga Fabrairu, 2026.

Sauya shekar Fintiri ta sanya jam'iyyar APC ta kara samun rinjaye a Najeriya, inda a yanzu take da iko kan jihohi 31 yayin jam'iyyun adawa suka tsira da jihohi biyar kacal.

Wannan na zuwa ne yayin da wasu 'yan adawa ke ci gaba da jefa zargi ga gwamnatin Bola Ahmed Tinubu na cewa tana kokarin mayar da Najeriya a kan tsarin siyasar jam'iyya daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com