Tafiyar Gawuna ADC Ta Fara Lahanta APC a Kano, Shugaba a Jam'iyya Ya Bi Ubangidansa
- Jamiyya mai mulki ta APC ta ƙara rasa jagora a siyasar Kano, Bashir Maisango, wanda tuni aka hano jam'iyyar da zai koma
- Maisango, wanda shi ne Sakataren jin kai na jam’iyyar APC ya yi murabus kwanaki kadan bayan Nasiru Yusuf Gawuna ya koma ADC
- Nasiru Yusuf Gawuna ya haɗe da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso a ADC bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya koma APC
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Sakataren jin kai na jam’iyya mai mulki ta APC a jihar Kano, Bashir Maisango, ya ajiye mukaminsa tare da ficewa daga jam’iyyar,
Wannan gagarumin sauyi ya zo wa jam'iyyar a lokacin da tsohon ɗan takarar gwamnanta, Nasiru Yusuf Gawuna ya bar jam'iyya.

Source: Facebook
Daily Nigerian ta wallafa cewa ana kallon Maisango, wanda a baya ya taba rike mukamin mataimakin sakatare a jam’iyyar, a matsayin jigo mai tasiri da kuma gogaggen mai hada kan jama’a a matakin kasa a Kano.
Abin da Maisango ya rubuta wa APC
A cikin wasikar murabus dinsa mai taken “murabus daga APC da son ransa,” wadda ya aikewa Shugaban jam’iyyar na jihar, Maisango ya bayyana cewa ya gode wa jam’iyyar bisa damar da ta ba shi a lokacin da yake cikinta.
Ya rubuta cewa:
“Ni, Bashir Tijjani Maisango, ina sanar da murabus dina daga jam’iyyar APC bisa raɗin kaina, wanda zai fara aiki daga ranar 1 ga Afrilu, 2026."'
Ya kara da cewa:
"Ina gode wa jam’iyyar bisa damar da ta ba ni, kuma ina yi mata fatan alheri.”
Maisango zai bi Gawuna zuwa ADC
Rahotanni sun nuna cewa matakin da Maisango ya dauka ba ya rasa nasaba da ficewar tsohon Mataimakin gwamnan Kano, Nasiru Gawuna, wanda ya bar jam’iyyar APC a ranar 30 ga Maris, 2026.

Source: Facebook
Majiyoyi kusa da Maisango sun bayyana cewa ya dauki wannan mataki ne domin nuna goyon baya ga Gawuna, wanda shi ma ya sauya sheka daga jam’iyyar mai mulki.
Haka kuma, ana sa ran Maisango zai yi rijista da jam’iyyar ADC a mazabarsa ta Dakata da ke cikin jihar Kano, a wani mataki da ake ganin zai kara sauya yanayin siyasar jihar.
Ficewar Maisango na zuwa ne a wani lokaci da ake ci gaba da samun sauye-sauye a cikin jam’iyyun siyasa a Kano da ma kasa baki daya, lamarin da ke iya yin tasiri ga yadda harkokin siyasa za su kasance a nan gaba.
Gawuna ya bar APC zuwa ADC
A wani labarin, kun ji cewa Nasiru Yusuf Gawuna ya yi rajista da jam'iyyar ADC a mazabarsa dake karamar hukumar Nassarawa tare da karbar katin jam'iyya.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ne ya karbi Gawuna zuwa sabuwar jam'iyyar tasa bayan taron sirri da suka yi a gidansa dake Kano kwana daya bayan ya bar NNPP.
Gawuna ya yi murabus daga shugabancin bankin FMBN domin bin umarnin Shugaba Bola Tinubu ga masu neman takara a babban zaben 2027 da ke kara matsowa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

