2027: Jerin Ministoci da Manyan Jami’an Gwamnatin Tinubu 7 da Suka Yi Murabus don Takara

2027: Jerin Ministoci da Manyan Jami’an Gwamnatin Tinubu 7 da Suka Yi Murabus don Takara

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya riga ya bai wa daukacin masu rike da mukaman siyasa umarnin yin murabus kafin ranar 31 ga Maris, 2026
  • Wannan mataki ya biyo bayan tanadin sabuwar dokar zabe ta shekarar 2026 wadda ta bukaci masu neman takara su sauka daga kujerunsu
  • Daga cikin wadanda suka yi murabus har da ministoci uku da shugabannin hukumomin tarayya hudu dake hararar kujerun gwamna da sanata

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

FCT, Abuja - Yayin da wa'adin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya diba wa masu neman takara ya cika, wasu manyan jami'an gwamnati sun mika takardun murabus dinsu domin fuskantar kalubalen zaben 2027.

Wannan sauyin yana zuwa ne daidai lokacin da jam'iyyun siyasa ke shirin gudanar da zabukan fitar da gwani na takarar Gwamna da na majalisun dokoki gabanin babban zaben 2027.

Kara karanta wannan

APC na shan matsin lamba kan takarar 2027, an yi gargadin rikici zai barke

Ministoci 3 da manyan jami'an gwamnatin tarayya sun yi murabus don shiga zaben 2027
Hagu zuwa dama: Yusuf Tuggar (tsohon ministan waje), Sa'idu Ahmed Alkali (tsohon ministan sufuri) da Nasiru Gawuna (tsohon shugaban FMBN). Hoto: @SenAlkali, @YusufTuggar, @KwankwasoRM
Source: Twitter

Ministoci 3 da suka yi murabus

Ga jerin sunayen ministoci da manyan jami'ai da suka riga suka sauka daga mukamansu a hukumance, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito:

1. Yusuf Tuggar (Ministan waje)

Tuggar shi ne minista na farko da ya fara mika takardar murabus dinsa a ranar Litinin, 30 ga Maris, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

Tsohon jakadan na Najeriya a kasar Jamus yana hararar kujerar Gwamnan jihar Bauchi ne a karkashin jam'iyyar APC.

2. Sa'idu Ahmed Alkali (Ministan sufuri)

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa, ministan sufuri, Sanata Sa'idu Alkali, ya gana da Shugaba Bola Tinubu a ranar Talata inda ya sanar da murabus dinsa.

Rahoto ya nuna cewa Sanata Sa'idu Alkali yana son ya gaji kujerar gwamnan jihar Gombe daga hannun Gwamna Inuwa Yahaya a zaben 2027.

3. Yusuf Sununu (Ministan jin-kai)

Dr. Yusuf Sununu ya bar kujerarsa ta karamin minista a ma'aikatar jin kai da yaki da talauci. Sununu zai koma jiharsa ta Kebbi domin tsayawa takarar Sanata (Kebbi ta Kudu), kamar yadda muka ruwaito.

Kara karanta wannan

Mamaki ya kama Isra'ila da makaman Iran suka lalata dakunan kariyarta

Kafin yanzu ya wakilci yankinsa na Shonga/Yauri/Ngaski a majalisar wakilan tarayya.

Jami'an gwamnati da za su tafi takara

4. Rauf Olaniyan (FCE Special, Oyo)

Tsohon mataimakin gwamnan jihar Oyo, Rauf Olaniyan, ya yi murabus daga mukaminsa na shugaban hukumar gudanarwa ta kwalejin ilimi ta tarayya (FCE Special) dake Oyo.

Olaniyan ya sauka ne domin ya shiga takarar neman tikitin Gwamnan Jihar Oyo a karkashin jam'iyyar APC, kamar yadda rahoton TVC News ya nuna.

5. Nasiru Yusuf Gawuna (FMBN)

Nasiru Gawuna ya ajiye mukaminsa, kuma ya shiga ADC don yin takarar gwamnan Kano a 2027
Tsohon mataimakin gwamnan Kano, Nasiru Gawuna yana daga katin shaidar zamansa d'an jam'iyyar ADC. Hoto: @KwankwasoRM
Source: Twitter

Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, Nasiru Gawuna ya yi murabus daga shugabancin Bankin Lamunin Gidaje (FMBN).

Legit Hausa ta ruwaito cewa, Gawuna ya riga ya koma jam'iyyar ADC inda ake sa ran zai sake tsayawa takarar Gwamnan Jihar Kano.

6. Ahmed Aminu (PTDF)

Shugaban hukumar bunkasa fasahar man fetur (PTDF), Ahmed Aminu, ya bi sahun sauran jami'an wajen yin murabus domin tsayawa takarar Gwamnan Jihar Adamawa a zabe mai zuwa, in ji rahoton Punch.

Kara karanta wannan

2027: Minista na 3 ya mika wa Tinubu takardar murabus, zai tsaya takarar gwamna

7. Abdulrazak Namdas (NDDC)

Tsohon dan majalisar wakilai, Abdulrazak Namdas, ya yi murabus daga mamba a hukumar raya yankin Neja-Delta (NDDC). Namdas ma yana son zama gwamnan jihar Adamawa a 2027.

Ministoc da manyan jami'an gwmanati sun yi murabus ne don bin umarnin Shugaba Bola Tinubu.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu a dakin taron majalisar zartarwa ta kasa da ke Abuja. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Me dokar zabe ta ce?

Sashe na 88(1) na sabuwar Dokar Zabe ta shekarar 2026 ta tanadi cewa dole ne kowane mai rike da mukamin siyasa da aka nada shi ya yi murabus kafin ya shiga zaben fitar da gwani na jam'iyya.

Wannan dokar tana nufin tabbatar da cewa babu wani jami'i da zai yi amfani da ikon ofishinsa ko dukiyar gwamnati wajen yakin neman zabe don samun fifiko kan sauran 'yan takara.

Tinubu ya yi sababbin nade-nade

A wani labari, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi sababbin nade-nade a gwamnatinsa, inda ya zakulo mutane daga jihohi daban-daban.

Mai girma Bola Tinubu ya dauko tsohon sanata daga jihar Katsina ya ba shi mukamin shugaban hukumar yi wa kamfanoni rajista (CAC).

Hakazalika Shugaban Najeriya ya nada kwamishinoni bakwai a hukumar kididdigar jama'a ta kasa watau NPC.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com