APC, ADC ko PDP?: Kungiyoyin Arewa, Yarbawa Sun Dauki Matsaya kan Zaben 2027

APC, ADC ko PDP?: Kungiyoyin Arewa, Yarbawa Sun Dauki Matsaya kan Zaben 2027

  • Kungiyar Yarbawa ta Afenifere ta sanar da komawa tafiyar jam'iyyar SDP a wani taro da ta gudanar ranar Talata a garin Ilesa na jihar Osun
  • Shugabannin Afenifere sun bayyana cewa tsarin jam'iyyar SDP ya yi daidai da manufofinsu na adalci da walwalar al'umma a fadin Najeriya
  • Sai dai, kungiyar Arewa ta musanta rahotannin cewa ta marawa SDP baya, inda ta ce wakilinta ya halarci taron ne a matsayin mai sanya ido

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Osun - A wani gagarumin sauyi na siyasa gabanin zaɓen 2027, babbar ƙungiyar kare muradun Yarabawa, Afenifere, ta sanar da amincewa da SDP a matsayin jam'iyyar da za ta marawa baya.

Wannan shawara ta fito ne yayin babban taron ƙungiyar da aka gudanar a ranar Talata, 31 ga Maris, 2026, a garin Ilesa dake jihar Osun.

Kara karanta wannan

INEC ta goge sunayen shugabannin ADC, tafiyar hadaka za ta iya rushewa

Kungiyar Afenifere ta zabi SDP a matsayin jam'iyyar da za ta mara wa baya a 2027.
Kungiyar Afenifere da wasu wakilan ACF sun yi taron mara wa SDP baya a Osun. Hoto: Thisdaylive
Source: Facebook

Afenifere za ta goyi bayan SDP a 2027

Ana ganin wannan mataki a matsayin yunƙurin fito da martabar jam'iyyar SDP kamar yadda ta yi nasara a zaɓen 1993 ƙarƙashin marigayi Chief MKO Abiola, in ji rahoton Tribune.

Shugaban ƙungiyar, Oba Oladipo Olaitan, ne ya jagoranci taron wanda ya samu halartar jiga-jigai irin su Senator Bucknor Akerele, Dele Farotimi, da kuma wakilan ƙungiyoyin Arewa.

Afenifere ta jaddada cewa ta zaɓi SDP ne domin akidun jam'iyyar sun yi daidai da nata na samar da adalci, daidaito, da kuma tsarin mulki da ya haɗa kowa da kowa.

An hango wakilan ACF a taron Afenifere

Wannan amincewa na zuwa ne a daidai lokacin da sauran manyan ƴan siyasa kamar Peter Obi da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso suke ƙoƙarin haɗa ƙarfi a ƙarƙashin jam'iyyar ADC.

Wani abu da ya dau hankali a taron shi ne yadda aka ga wakilai daga Arewacin Najeriya, kamar Dr. Usman Bugaje da kuma Salisu Nuhu Mohammad.

Kara karanta wannan

2027: Abubuwa 3 da za su iya faruwa idan Peter Obi ya rasa tikitin takara a ADC

Hakazalika, taron ya samu halartar Malam Murtala Aliyu (tsohon ministan makamashi) da dai sauran wasu jiga jigan kungiyar Dattawan Arewa ta ACF.

A bangaren Yarbawa kuwa, manyan shugabannin kungiyar Afenifere, irinsu Chief Supo Shonibare, Justice Faloye, sun halarci wannan taron, a cewar rahoton This Day.

Afenifere ta ce ta zabi jam'iyyar SDP ne don riko da manufofin marigayi Chief MKO Abiola.
Tambarin jam'iyyar SDP, wadda kungiyar Yarbawa ta ce za ta goya wa baya a 2027. Hoto: @officialsdp1
Source: Twitter

ACF ta nesanta kanta da batun SDP

Bayan yaɗuwar labarin cewa ƙungiyar ACF ma ta marawa jam'iyyar SDP baya, ƙungiyar ta fito ta yi ƙarin haske a yau Alhamis, 2 ga Afrilu, 2026.

Kakakin ƙungiyar ACF na ƙasa, Farfesa Tukur Muhammad Baba, ya fitar da sanarwa inda ya bayyana cewa Sakataren ƙungiyar, Malam Murtala Aliyu, ya halarci taron ne kawai a matsayin mai sanya ido.

"Muna son bayyana cewa Malam Murtala Aliyu ya halarci taron ne bisa gayyatar Afenifere domin ƙarfafa dangantaka tsakanin ƙungiyoyin Afenifere, ACF, da NEF, ba wai don ya zama wakilin wata jam'iyyar siyasa ba," in ji sanarwar.

ACF ta buƙaci jam'iyyar SDP da ta daina amfani da sunan ƙungiyar wajen yaƙin neman zaɓe, tana mai jaddada cewa burinta kawai shine zaman lafiya da haɗin kan yankuna.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Gawuna ya shiga sabuwar jam'iyya don karawa da Abba a 2027

SDP ta hango nasara a zaben 2027

A wani labari, mun ruwaito cewa, SDP mai adawa ta bayyana cewa ga dukkan alamu ita za ta lashe zaɓen shugaban kasa mai zuwa a shekarar 2027.

Mataimakin shugaban SDP na Arewa ta Tsakiya, Abubakar Dogara ya ce idan Allah ya yarda za su kwace mulki daga hannun Bola Tinubu.

Dogara ya yi kira ga ƴan Najeriya da su marawa SDP baya kuma su yi rijistar zama cikakkun ƴan jam'iyya a mazaɓunsu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com