2027: Abubuwa 3 da Za Su Iya Faruwa idan Peter Obi Ya Rasa Tikitin Takara a ADC

2027: Abubuwa 3 da Za Su Iya Faruwa idan Peter Obi Ya Rasa Tikitin Takara a ADC

Abuja - Yayin da fafutukar neman tikitin takarar shugaban ƙasa na 2027 a jam'iyyar ADC yake ƙara zafi, masana sun fara hasashen abubuwan da za su iya faruwa idan har Peter Obi ya gaza samun tikitin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

A halin yanzu, jam'iyyar ADC ta zama matattarar zaratan 'yan adawa kamar Atiku Abubakar, Rotimi Amaechi, da sauransu waɗanda duka suke hararar kujera ɗaya.

Masu sharhi sun fara hasashen abubuwan da za su iya faruwa idan Peter Obi ya rasa tikitin takara a ADC.
Peter Obi, tsohon dan takarar shugaban kasar Najeriya. Hoto: Mr. Peter Obi
Source: Facebook

Rahoton jaridar Premium Times ya nuna cewa Peter Obi, ya shiga jam'iyyar ADC ne a Disambar 2026, kuma ya fito fili ya ayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a 2027.

Ga manyan abubuwa uku da ake fargabar za su faru idan Peter Obi bai zama ɗan takarar ADC ba:

Me zai faru idan Obi ya rasa tikiti?

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Gawuna ya shiga sabuwar jam'iyya don karawa da Abba a 2027

1. Bore daga kungiyar 'Obidients'

Ƙungiyar nan ta 'Obidient movement' wadda take biyayya ga Peter Obi tana da matuƙar ƙarfi da kishin ganin jagoran nasu ya jagoranci Najeriya.

Idan har aka ki ba shi tikiti, ana fargabar cewa magoya bayan nasa za su iya fita daga jam'iyyar ADC su koma wata inuwar ko kuma su daina goyon bayan tafiyar gaba ɗaya.

Kamar yadda suka biyo shi daga jam'iyyar LP zuwa ADC, hakan na iya sake faruwa idan suka ji an maida su saniyar ware, a cewar rahoton binciken jaridar Punch.

2. Rasa tasiri a tsakanin matasa

Babban tasirin da Peter Obi yake da shi shine farin jini a tsakanin matasan Najeriya da kuma mazauna birane, musamman a Kudancin ƙasa da yankin Arewa ta tsakiya.

Ba tare da shi a matsayin mai riƙe da tutar jam'iyya ba, ADC na fuskantar barazanar rasa waɗannan ƙuri'un da suke da karsashi, wanda hakan zai rage wa jam'iyyar ƙarfin takara a matakin ƙasa.

Kara karanta wannan

2027: Minista na 3 ya mika wa Tinubu takardar murabus, zai tsaya takarar gwamna

Rashin shigar matasa zaɓe zai zama babbar nasara ga jam'iyyar APC mai mulki.

A wata hira da Arise News, tsohon gwamnan Ekiti, Ayo Fayose, ya yi gargadi cewa, kin ba Obi tikiti a ADC zai kawo karshen tasirin jam'iyyar, don ba wanda zai zabe ta.

"Kowa ya ga tasirinsa a zaben 2023, lokacin da jam'iyyar LP, wacce babu wanda ya san da ita kafin ya koma cikinta, ta zo ta lashe kujerun majalisar tarayya har da gwamna a Abia."
Ana ganin cewa bangaren adawa za su samu rauni idan Peter Obi ya gaza samun tikitin ADC
Peter Obi, tsohon dan takarar shugaban kasar Najeriya. Hoto: Mr. Peter Obi
Source: Twitter

3. Rushewar sabon karfin hamayya

Rashin bai wa Obi tikiti na iya janyo sababbin matsalolin siyasa inda zai iya komawa cikin wata babbar jam'iyyar adawa, kamar misalin PDP, ko kuma ƙirƙirar wani sabon kawancen, misali jam'iyyar NDC ta Sanata Dickson.

Wannan zai raunana burin ADC na zama jam'iyya ta uku mai ƙarfin gaske da za ta iya kayar da APC da PDP.

Jaridar Vanguard, ta rahoto Ayo Fayose ya nuna shakku a kan ko Peter Obi zai yarda ya zama abokin takarar wani a ADC ganin cewa Kwankwaso ya shiga jam'iyyar.

Kara karanta wannan

APC da ADC sun kece raini yayin da 'yan majalisar tarayya 27 suka sauya sheka

"Yau, Kwankwaso ya koma jam'iyyar. Atiku zai iya samun tikiti. Obi zai yarda ya zama abokin takara, matsayin mataimakin shugaban kasa? Wannan ita ce tambayar."

- Ayo Fayose.

ADC: Kwankwaso, Atiku, Obi sun hade kai

A wani labari, mun ruwaito cewa, manya-manyan 'yan takarar shugaban kasa na 2023 sun hadu a jam'iyyar ADC domin kalubalantar APC a zaben 2027 da ke tafe.

Masu sharhin siyasa na ganin cewa rashin hadin kan Atiku Abubakar, Peter Obi, Rabiu Kwankwaso a zaben baya ne ya ba Shugaba Bola Tinubu damar lashe zaben.

Yanzu da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya koma ADC, ana ganin cewa hada takararsa da Peter Obi ita za ta ba jam'iyyar nasara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com