Siyasar Kano: Gawuna Ya Shiga Sabuwar Jam'iyya don Karawa da Abba a 2027
- Nasiru Yusuf Gawuna ya yi rajista da jam'iyyar ADC a mazabarsa dake karamar hukumar Nassarawa tare da karbar katin mamba
- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ne ya karbi Gawuna zuwa sabuwar jam'iyyar tasa bayan taron sirri da suka yi a gidansa dake Kano
- Gawuna ya yi murabus daga shugabancin bankin FMBN domin bin umarnin Shugaba Bola Tinubu ga masu neman takara a 2027
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kano - A wani mataki da ya girgiza fagen siyasar Kano, tsohon ɗan takarar gwamna na jam'iyyar APC a zaɓen 2023, Nasiru Yusuf Gawuna, ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar ADC a hukumance.
Tsohon mataimakin gwamnan ya kammala rajista tare da karɓar katin zama mamba na jam'iyyar a ranar Talata a mazaɓarsa ta Gawuna dake ƙaramar hukumar Nassarawa a birnin Kano.

Source: Twitter
Gawuna ya bi Kwankwaso zuwa ADC
Wannan taro ya samu halartar manyan jiga-jigan siyasa, ciki har da jagoran ƙungiyar Kwankwasiyya, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, da kuma tsohon mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo, in ji rahoton Punch.
Gawuna ya bayyana cewa a karan kansa ne ya yanke shawarar ficewarsa daga jam'iyyar APC, kamar yadda ya bayyana a cikin wasiƙar murabus ɗinsa mai kwanan wata 29 ga Maris, 2026.
A cikin wasiƙar tasa, Gawuna ya gode wa jam'iyyar APC bisa damar da ta ba shi na yin hidima da kuma ba da gudunmawa ga ci gaban jam'iyyar a tsawon lokacin da ya yi cikinta.
"Ina godiya ga magoya bayana da shugabannin jam'iyyar, kuma ina tabbatar muku da jajircewa ta wajen ƙarfafa jam'iyyar ADC a jihar nan tamu," in ji Gawuna.
Haduwar Gawuna da Kwankwaso a Kano
Kafin ya yi rajista a hukumance, Gawuna ya gana da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a gidansa dake birnin Kano, inda Kwankwaso da kansa ya wallafa hotunan taron a shafinsa na X.
Kwankwaso ya bayyana cewa yana fatan alheri ga abubuwan dake tafe nan gaba sakamakon wannan sabon kawance.
Idan za a iya tunawa, Gawuna ne ya zo na biyu a zaɓen gwamnan jihar Kano na 2023 inda ya samu ƙuri'u 890,705, yayin da Gwamna Abba Kabir Yusuf na NNPP ya samu ƙuri'u 1,019,602.

Source: Twitter
Martanin Kwankwaso kan sauya shekar Gawuna
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya wallafa a shafinsa na X cewa:
"A yau, muna farin cikin karbar Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, tsohon mataimakin gwamnan Kano, kuma tsohon dan takarar gwamna na APC, zuwa jam'iyyar ADC."
Da yake magana gaban dubunnan magoya baya, wanda a cewarsa yake nufin irin karfin da Gawuna yake da shi, Kwankwaso ya ce sauyin shekar ta nuna cewa akwai babban abu da ke shirin faruwa a siyasar Kano.
"Na kuma yi amfani da wannan damar wajen yin gargadi ga masu shirin ruguza tsarin zabukan da ke tafiya, za mu nuna turjiya ga duk wanda ya yi yunkurin murde zabin al'umma."
- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Karanta sakon a nan kasa:
Kwankwaso ya shiga ADC a hukumance
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi rajistar zama 'dan jam'iyyar ADC a hukumance tare da karbar katin mamba.
Manyan 'yan siyasa kamar Peter Obi da David Mark da Aminu Tambuwal sun halarci taron karbar Kwankwaso zuwa jam'iyyar 'yan adawa.
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa ya bar jam'iyyar NNPP ne domin samar da sabon tsarin siyasa da zai tafi da kowa a 2027.
Asali: Legit.ng


