Watakila ADC Ta Gyara Zama a Sokoto, Sanatan APC na Tunanin Sauya Sheka

Watakila ADC Ta Gyara Zama a Sokoto, Sanatan APC na Tunanin Sauya Sheka

  • Majiyoyi sun tabbatar da cewa Sanata daga yankin Sokoto na shirin ficewa daga jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya
  • An tabbatar da cewa hakan bai rasa nasaba da sabanin da ke tsakaninsa da shugabancin jam’iyya wanda ya yi kamari a yanzu
  • Magoya bayansa da dama sun fara barin APC, ciki har da tsohon shugaban jam’iyya a Goronyo, Kabiru Shehu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Skoto - Wasu majiyoyi sun ce akwai alamun cewa sanatan da ke wakiltar Sokoto ta Gabas, Ibrahim Lamido, na daf da ficewa daga jam’iyyar APC.

Wannan na zuwa ne sakamakon sabanin da ke tsakaninsa da shugabannin jam’iyyar a jihar wanda ya ke neman raba ta gida biyu.

Sanatan APC a Sokoto ya shirya barin jam'iyyar
Sanata Ibrahim Lamido yayin zama majalisa a Abuja. Hoto: The Nigerian Senate.
Source: Facebook

Magoya bayan sanata suna guduwa daga APC

Majiyoyi kusa da sanatan sun bayyana wa Daily Trust cewa wannan mataki na iya tabbata cikin kwanaki kadan, musamman bayan wasu daga cikin magoya bayansa sun fara sauya sheka daga jam’iyyar.

Kara karanta wannan

A karshe: Gawuna ya tafi gidan Kwankwaso zuwa shiga ADC bayan barin APC

Daga cikin wadanda suka riga suka fice akwai Kabiru Shehu, tsohon shugaban APC a karamar hukumar Goronyo kuma tsohon shugaban riko na karamar hukumar.

Kabiru Shehu ya taba zama shugaban bangaren APC da ke goyon bayan Lamido a jihar Sokoto, kamar yadda shafin 'I Stand with ADC' ya wallafa a Facebook.

Wani babban mai taimaka wa sanatan, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da cewa ficewar da ake shirin yi wani bangare ne na tsari da aka tsara tare da magoya bayan Lamido.

A cewarsa:

“Dukkan magoya bayansa suna shirin barin APC, har da shi kansa sanatan. Abin jira kawai lokaci ne.”
Rigimar APC a Sokoto na neman jawo mata matsala
Taswirar jihar Sokoto da APC ke mulki karkashin Gwamna Ahmed Aliyu. Hoto: Legit.
Source: Original

'Abin da ya jawo rigimar APC a Sokoto'

Duk da haka, ba a bayyana a hukumance dalilin ficewar ba, amma majiyoyi sun danganta hakan da tsohon rikici da ba a warware ba a cikin tsarin jam’iyyar a Sokoto.

Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya kara tsananta bayan bangarorin da ke goyon bayan Sanata Lamido sun gudanar da nasu zabukan shugabannin jam’iyya a matakai daban-daban.

An ce bangaren ya zabi shugabanni daga matakin mazaba zuwa kananan hukumomi da kuma matakin jiha, abin da ya kara raba kan jam’iyyar.

Kara karanta wannan

An fara watsewa daga APC, tsohon ministan Najeriya ya raba hanya da Tinubu

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, babu wata sanarwa a hukumance daga Ibrahim Lamido ko shugabannin APC a jihar kan wannan lamari.

Duk da haka, ana yada jita-jitar cewa ya kammala shirin barin jam'iyyar duba da yadda magoya bayansa suka fice da ake ganin kamar sharar fage ne domin biyo su daga baya.

Hadimin gwamnan Kaduna ya koma jam'iyyar ADC

A wani labarin, an ji cewa jam'iyya mai mulki ta APC na ci gaba da rasa wasu 'ya'yanta yayin da ADC ke shirin tunkarar zaben 2027.

Daya daga cikin hadimin Uba Sani na Kaduna Hon. Yusuf Umar Garkuwa ya yi murabus daga mukaminsa na mai ba gwamna shawara.

Garkuwa ya fice daga jam’iyyar APC tare da mika shaidarsa na zama dan jam'iyya yayin da ya ke shirin hade wa da 'yan adawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.