NNPP Ta Gaza Hakura da Jagoranta, Za Ta Yi Haɗaka da ADC bayan Kwankwaso Ya Sauya Sheka

NNPP Ta Gaza Hakura da Jagoranta, Za Ta Yi Haɗaka da ADC bayan Kwankwaso Ya Sauya Sheka

  • Jam’iyyar adawa ta NNPP ta bayyana shirin haɗin gwiwa da ADC domin a yi wa APC rubudgu a babban zaɓe mai zuwa
  • Duk da jagoran jam'iyyar na ƙasa, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bar NNPP, har yana an nuna ana tare da shi
  • Jim kadan bayan Kwankwaso ya yanki tikitin zama halastaccen ɗan ADC, NNPP ta bayyana irin tattaunawarsu game da 2027

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Tsagin jam’iyyar NNPP ta bayyana cewa za ta shiga haɗin gwiwa da ADC domin tunkarar zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

Mai magana da yawun tsagin jam’iyyar na ƙasa, Ladipo Johnson, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin jim kadan bayan jagoran NNPP ya sauya sheka.

Kara karanta wannan

Manyan 'yan siyasar adawa da suka je Kano domin karbar Kwankwaso cikin ADC

NNPP da ADC za su yi aiki tare a zaɓen 2027
Ahmed Ajuji Shugaban NNPP tare da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso a wajen wani taro Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Da ya ke bayani a hira da ya yi a gidan talabijin na Channels ta cikin Morning Brief, Johnson ya ce magana tsakanin ADC da NNPP ta yo ƙarfi sosai.

Jam'iyyar NNPP za ta shiga takara

Jaridar Punch ta wallafa cewa Ladipo Johnson ya ce duk da cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a 2023, Rabiu Musa Kwankwaso, ya fice daga NNPP, hakan ba zai hana jam’iyyar ci gaba da shiga zaɓe ba.

A cewarsa:

"NNPP za ta ci gaba da tsayawa takara a dukkanin zaɓuɓɓuka. Duk da haka, a matakin shugaban ƙasa, za mu yi aiki tare da ADC, kuma watakila a wasu zaɓuɓɓukan ƙasa, amma za mu fitar da ‘yan takara a sauran matakai.”

Johnson ya ƙara da cewa an gudanar da tattaunawa mai yawa tsakanin shugabannin adawa kafin Kwankwaso ya yanke shawarar komawa ADC.

Dalilin NNPP na shiga haɗaka da ADC

Ladipo Johnson ya bayyana cewa manufar wannan haɗaka ita ce samar da wata hanya ta daban ga ‘yan Najeriya a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Bayan shiga ADC, Kwankwaso ya aika sako ga 'yan Najeriya kan zaben 2027

Ya ce:

"Shugabannin adawa sun fahimci cewa haɗuwa a karkashin inuwa guda zai fi amfani ga burinsu da kuma muradun ‘yan ƙasa.”
NNPP ta ce an yi tattaunawa kafin Kwankwaso ya koma ADX
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso tare da shaidar jam'iyyar NNPP Hoto: NNPP
Source: Facebook

Ficewar Rabiu Musa Kwankwaso daga NNPP ta biyo bayan makonni na tattaunawa da shawarwari da ya yi da jagororin ƙungiyar Kwankwasiyya da manyan jiga-jigan ADC.

Rahotanni sun nuna cewa ya gudanar da ganawa da fitattun ‘yan siyasa domin gina wata babbar gamayya da za ta iya kalubalantar jam’iyyar APC mai mulki a matakin tarayya.

Daga cikin waɗanda ya gana da su akwai sakataren ƙasa na ADC, Rauf Aregbesola; tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na Labour Party, Peter Obi; gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde; da sanatan Bayelsa ta Yamma, Seriake Dickson.

Nasiru Gawuna zai shiga jam'iyyar ADC

A baya, mun wallafa cewa ɗan takarar gwamnan Kano karkashin jam'iyyar APC a 2023, Nasiru Yusuf Ganuwa ya ziyarci gidan Rabiu Musa Kwankwaso.

Hakan na zuwa ne bayan ya sanar da ficewar shi daga jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya a shirin haduwa da 'yan adawa a ADC domin tunkarar 2027.

Kara karanta wannan

A ƙarshe, Kwankwaso ya yanki katin zama ɗan jam'iyyar ADC, ya haɗe da su Atiku

Daya daga cikin jagororin Kwankwasiyyya, Dr Yusuf Kofarmata ya sanar da lokacin da za a karbi Gawuna zuwa ADC a jihar Kano ana tsaka da sauya fasalin siyasar Kano.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng