Siyasa Ta Dauki Zafi, Minista na 2 Ya Mika Wa Tinubu Takardar Murabus cikin Awanni 24

Siyasa Ta Dauki Zafi, Minista na 2 Ya Mika Wa Tinubu Takardar Murabus cikin Awanni 24

  • Karamin Ministan Jin Kai da Yaki da Talauci, Hon. Yusuf Tanko Sununu ya yi murabus daga kujerarsa domin neman takarar sanata a 2027
  • Tsohon 'dan majalisar tarayya, Yusuf Sununu ya tabbatar da hakan ne yayin da aka tuntube shi kan lamarin a ranar Litinin, 30 ga watan Maris, 2026
  • Hakan na zuwa ne sa'o'i kadan bayan Ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Tuggar ya mika takardar ajiye aiki saboda zai nemi kujerar gwamnan Bauchi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da .kullum

Jihar Kebbi - Karamin Ministan Harkokin Jin Kai da Rage Talauci, Yusuf Tanko Sununu, ya yi murabus daga mukaminsa a gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu..

Yusuf Sununu ya mika takardar murabus dinsa daga matsayin minista ne a yammacin yau Litinin, 30 ga watan Maris, 2026.

Sunusu.
Karamin ministan harkokin jin kai da yaye talauci, Yusuf Tanko Sununu Hoto: @ImranMuhdz
Source: Twitter

Karaminin ministan Tinubu ya yi murabus

Kara karanta wannan

Domin biyayya ga umarnin Tinubu, minista ya yi murabus daga mukaminsa a Najeriya

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa ministan ya yi murabus ne domin biyayya ga umarnin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.

Hakan na zuwa ne sa'o'i kadan bayan an samu labarin cewa Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Yusuf Tuggar ya mika takardar murabus ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Yusuf Tanko Sununu ya zama minista na biyu da ya ajiye aiki bayan Yusuf Tuggar cikin 'yan sa'o'i kadan a yau Litinin.

Tun farko shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya umarci ministo da jami'an gwamnatin tarayya da ke da burin tsayawa takara a zaben 2027 su yi murabus a ko kafin ranar 21 ga watan Maris, 2026.

Me yasa Yusuf Sununu ya ajiye aiki?

Domin biyayya ga wannan umarni na Shugaba Tinubu, Yusuf Tanko Sununu ya sanar da cewa ya yi murabus daga kujerarsa ta Karamin Ministan Harkokin Jin Kai da Rage Talauci.

Sununu ya tabbatar da murabus dinsa ga manema labarai, inda ya ce ya dauki wannan mataki ne bisa dokokin kasar nan da ke bukatar masu neman mukamin siyasa su ajiye mukamansu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun farmaki wurin taron bikin aure, an yi barna mai girma

Lokacin da aka tambaye shi ta hanyar tura masa sakon waya kan ko ya yi murabus, ya amsa da cewa eh, ya bar mukaminsa a gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Rahotanni sun nuna cewa, Yusuf Sanusu, tsohon dan majalisar wakilai na tarayya, wanda ya wakilci mazabar Shanga/Yauri/Ngaski, na shirin tsayawa takarar Sanata mai wakiltar Kebbi ta Kudu a zaben 2027.

Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a wurin taro a Abuja Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Gudummuwar da ya bayar ga yan Najeriya

Kafin nadinsa a ma’aikatar jin kai, Sununu ya taba rike mukamin Ministan Ilimi kafin daga bisani a mayar da shi zuwa ma’aikatar jin kai na tarayya, cewar rahoton Leadership.

An bayyana shi a matsayin jagora da ya aiwatar da ayyuka masu tasiri a bangarorin da ya rike, musamman wajen tallafa wa al’umma da rage radadin rayuwa ga jama’ar jihar Kebbi.

Mutane da dama na ganin cewa matakin da ya dauka na shiga siyasa zai ba shi damar ci gaba da hidima ga al’umma.

Yusuf Tuggar ya ajiye mukaminsa na minista

A wani labarin, kun ji cewa Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Tuggar, ya yi murabus daga mukaminsa a gwamnatin Tinubu.

Kara karanta wannan

Malaman Musulunci sun yi wa Tinubu saukar Kur'ani sama da sau 100

Rahotanni sun tabbatar da cewa Tuggar ya ajiye aiki ne domin ya nemi kujerar gwamnan Jihar Bauchi a babban zaɓe na 2027 mai zuwa.

Ma'aikatar harkokin wajen Najeriya ta tabbatar da murabus din Yusuf Tuggar ta hannun mai magana da yawunta, Kimiebi Ebienfa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262