Domin Biyayya ga Umarnin Tinubu, Minista Ya Yi Murabus daga Mukaminsa a Najeriya

Domin Biyayya ga Umarnin Tinubu, Minista Ya Yi Murabus daga Mukaminsa a Najeriya

  • Yayin da wa'adin da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayar ke dab da cika, Yusuf Tuggar ya yi murabus daga kujerar ministan harkokin waje
  • Tuggar ya dauki wannan mataki ne domin maida hankali ga burinsa na neman zama gwamnan jihar Bauchi a babban zaben 2027 da ke tafe
  • Tun farko, Shugaba Tinubu ya umarci ministoci da duk wani jami'in gwamnati da ke shirin tsayawa takara ya yi murabus a ko kafin 31 ga Maris, 2026

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Tuggar, ya yi murabus daga mukaminsa a yau Litinin, 30 ga watan Maris, 2026.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Tuggar ya ajiye aiki ne domin ya nemi kujerar gwamnan Jihar Bauchi a babban zaɓe na 2027 mai zuwa.

Kara karanta wannan

An rage mugun iri: Cikin jimami, ISWAP ta sanar da mutuwar babban kwamandanta

Yusuf Tuggar.
Ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Tuggar Hoto: @YusufTuggar
Source: UGC

Yusuf Tuggar ya ajiye kujerar minista

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa ministan, wanda mamba ne a jam'iyyar APC mai mulki, ya mika takardar murabus daga mulaminsa ga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.

Ya dauki wannan matakin ne sa'o'i 24 kafin cikar wa'adin da shugaban kasa ya bada ga duk wani mai rike da mukami da ke fa burin neman talara a babban zabe mai zuwa.

Umarnin da Shugaba Tinubu ya bayar

Idan baku manta ba, ya umurci duk wani jami’in gwamnatinsa da ke da niyyar tsayawa takara a zaɓe mai zuwa ya yi murabus xaga mukaminsa a ko kafin ranar 31 ga Maris, 2026.

Wannan umarni na Bola Tinubu ya fito ne daga ofishin Sakataran Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume.

Hakan ya yi daidai da sashi na 88(1) na Dokar Zaɓe ta 2026, da kuma jadawalin da Hukumar Zaɓe ta Kasa (INEC) ta fitar na zaben fitar da yan takara da jam’iyyun siyasa za su gudanar gabanin 2027.

Kara karanta wannan

Tinubu ya cika shekaru 74 a duniya, ya aika muhimmin sako ga 'yan Najeriya

Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yana aiki a ofishinsa Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Dalilin murabus din Yusuf Tuggar

Ma'aikatar harkokin wajen Najeriya ta tabbatar da murabus din Yusuf Tuggar ta hannun mai magana da yawunta, Kimiebi Ebienfa, a wata sanarwa da ta fitar yau Litinin.

Tuggar na daya daga cikin mimistocin da suke da niyyar neman kujerar gwamna a jihohinsu karkashin inuwar jam'iyyar APC mai mulki, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Tare da wannan ci gaba, ana sa ran samun karin murabus daga wasu ministoci da jami'an gwamnatin tarayya a kwanaki masu zuwa yayin da suke kokarin biyayya ga wa’adin da shugabann kasa ya ƙayyade.

Gawuna ya ajiye wa Tinubu mukaminsa

A wani rahoton, kun ji cewa Nasiru Yusuf.Gawuna, ya yi murabus daga mukaminsa na shugaban kwamitin gudanarwa na Bankin Lamunin Gidaje na Ƙasa (FMBN).

Wannan na zuwa ne yayin da ake rade-radin Gawuna, wanda ya yi takarar gwamnan Kano a inuwar APC a zaben 2023, na shirin sauya sheƙa zuwa jam’iyyar ADC tare da Kwankwaso.

Gawuna ya bayyana cewa murabus ɗin nasa ya fara aiki nan take, yana mai cewa matakin ya yi daidai da umarnin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262