Wata Sabuwa: Uban NNPP Ya Yi Magana Mai Zafi kan Ficewar Kwankwaso daga Jam'iyya
- Uban NNPP na kasa, Boniface Aniebonam ya ce mambobin jam'iyyar na asali ba za su bi tawagar Kwankwaso zuwa ADC ba
- A jiya Lahadi ne tsohon dan takarar shugaban kasa, Rabiu Kwankwaso ya sanar da ficewarsa daga NNPP a hukumance
- Sai dai a martaninsa, Aniebonam ya yi maraba da matakin da Kwankwaso ya dauka, yana mai cewa ba za su sake hada hanya da shi ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Wanda ya kafa NNPP, Boniface Aniebonam, ya bayyana matsayarsa bayan ficewar tsohon dan takarar shugaban kasa, Sanata Rabiu Kwankwaso daga jam’iyya.
Ya tabbatarwa 'yan Najeriya cewa mambobin NNPP ba su cikin shirin komawa sabuwar jam’iyyar da Kwankwaso ya nufa.

Source: Facebook
Tribune Nigeria ta ce Aniebonam ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, jim kadan bayan Kwankwaso ya sanar da ficewarsa daga NNPP a hukumance.
Kwankwaso ya bayyana dalilin barin NNPP
Kwankwaso, wanda ya tsaya takarar shugaban kasa a inuwa NNPP a zaben 2023, ya ce ya bar jam’iyyar ne domin yin “sabon tsari na siyasa” a halin da ake ciki.
Ya kuma ce zai koma jam’iyyar ADC a ranar Litinin, 30 ga Maris, 2026, lamarin da ya girgiza siyasar Najeriya musamman a yankin Arewa.
Jam'iyyar NNPP ta nesanta kanta da Kwankwaso
Da yake mayar da martani, Aniebonam ya jaddada cewa NNPP ba za ta bi Kwankwaso zuwa ADC ba.
Ya ce:
“Ba za mu shiga ADC ba, yawancin mambobinmu a Kano sun riga sun koma APC. Sai dai mabiyan tafiyar Kwankwasiyya ne kawai za su iya binsa."
"Ba za mu karɓe shi ba kuma ba za mu bari ya sake tsayawa takara a ƙarƙashin jam’iyyarmu ba.”
Ya kuma yi watsi da wata sanarwa da aka danganta ga Ahmed Ajuji, yana mai jaddada cewa an jima da korarsa da wasu ‘yan Kwankwasiyya kamar Buba Galadima daga NNPP.
Ya kara da cewa rikice-rikicen shari’a a jam’iyyar NNPP sun sa mambobi da dama sun koma APC, kamar yadda jaridar Punch ta kawo.

Source: Facebook
Shirin da NNPP ke yi kafin zaben 2027
Duk da haka, Aniebonam ya ce jam’iyyar ta fara tuntubar 'ya'yanta a duka sassan kasar nan domin fara shirye-shiryen zaben 2027, inda ya ce duk masu neman takara za su bi tsarin zaben fidda gwani.
"Ba za mu sake yin kuskuren baya ba,” in ji shi, yana mai zargin Kwankwaso da cin amanar jam’iyyar bayan an ba shi tikitin takara ba tare da ya sha wahala ba.
Ya kuma kara da cewa kofar jam’iyyar NNPP a bude take ga hadin gwiwa da sauran kungiyoyin siyasa masu ra’ayi iri daya gabanin zaben 2027.
Kwankwaso ya gana da sakataren ADC
A baya, kun ji cewa tsohon ministan cikin gida kuma sakataren jam'iyyar ADC na kasa, Rauf Aregbesola ya ziyarci Sanata Rabiu Kwankwaso a gidan shi da ke Abuja.
Hakan na zuwa ne yayin da rahotanni suka tabbatar da cewa Sanata Rabiu Kwankwaso zai fita daga NNPP zuwa jam'iyyar hadakar 'yan adawa ta ADC.
Baya ga haka, wasu shugabannin jam'iyyar ADC a jihar Kano sun gana da Rabiu Musa Kwankwaso domin tattauna lamuran siyasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

