Gwamna Zulum Ya Rusa Majalisar Zartarwa, Ya Kori Dukkan Kwamishinonin Jihar Borno

Gwamna Zulum Ya Rusa Majalisar Zartarwa, Ya Kori Dukkan Kwamishinonin Jihar Borno

  • Gwamna Babagana Umara Zulum ya amince da rushe majalisar zartarwar jihar Borno nan take yayin da ake tunkarar babban zaben 2027
  • Gwamnatin jihar ta umarci dukkanin kwamishinoni da su mika ragamar ma'aikatunsu ga manyan sakatarorin kafin ranar 3 ga Afrilu
  • Wannan mataki yana da alaka da shirye-shiryen babban zaben da ke tafe, wanda zai ba masu mukamai damar tsayawa takara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ba da umarnin rushe daukacin majalisar zartarwar jiharsa.

A yau Litinin, Gwamna Babagana Zulum ya umarci dukkan kwamishinonin jihar Borno da su sauka daga muƙamansu nan take.

Gwamna Babagana Umara Zulum ya tsige dukkan kwamishinonin Borno.
Mai girma gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum yana jawabi a wani taro. Hoto: Prof. Babagana Umara Zulum
Source: Twitter

Zulum ya kori dukkan kwamishinonin Borno

Wannan umarni ya fito ne ta hannun sakataren gwamnatin jihar Borno, Bukar Tijani, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yakin Iran: Koriya ta yi gwajin injin makami mai linzami da zai iya kaiwa Amurka

Bukar Tijani ya bayyana cewa matakin ya fara aiki ne ba tare da ɓata lokaci ba gwamnati damar gudanar da garambawul ga majalisar zartarwa.

Sakataren ya bayyana cewa:

"Gwamna Babagana Umara Zulum ya amince da rushe Majalisar Zartarwa ta jihar nan take domin share fage ga masu burin yin takara a 2027."

Umarni ga kwamishinonin da aka kora

Gwamna Zulum ya bayyana cewa wannan mataki zai samar da yanayi mai kyau ga 'yan majalisar zartarwar dake da burin tsayawa takara a 2027.

Gwamnan ya umarci dukkan kwamishinonin da su miƙa ragamar ayyukan ma'aikatunsu ga manyan sakatarori daga nan zuwa ranar Juma'a, 3 ga Afrilu, 2026 ko kafin nan.

Zulum ya jinjina wa kwamishinonin bisa jajircewa da gudunmawar da suka bayar yana mai cewa:

"Ina godiya gare ku bisa kwazo da sadaukarwar da kuka nuna wajen yi wa al'ummar jihar Borno hidima."
Gwamna Babagana Zulum ya ce rushe majalisar zartarwa zai ba mambobin majalisar damar tsayawa takara a 2027
Taswirar jihar Borno, inda Gwamna Babagana Umara Zulum ya rusa majalisar zartarwa. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Zulum ya bi sahun sauran gwamnoni

Gwamnan jihar Borno shi ne na baya-bayan nan cikin jerin gwamnonin da suka umarci masu riƙe da muƙaman siyasa dake son takara da su yi murabus daga ofisoshinsu, in ji rahoton Channels TV.

Kara karanta wannan

An rage mugun iri: Cikin jimami, ISWAP ta sanar da mutuwar babban kwamandanta

Sauran gwamnonin da suka ɗauki irin wannan mataki sun haɗa da Monday Okpebholo na Edo, Bassey Otu na Cross River, da kuma Sheriff Oborevwori na jihar Delta.

Haka kuma, Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa da takwaransa na jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, duk sun bayar da irin wannan umarni ga hadimansu dake son takara.

Gwamnatin jihar Borno ta tabbatar da cewa za a ci gaba da gudanar da ayyukan gwamnati ba tare da tangarɗa ba yayin da ake jiran naɗa sababbin mambobin majalisar.

Gwamnan Borno ya tabo batun magaji a 2027

A wani labari, mun ruwaito cewa, Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya yi magana kan wanda zai gaje shi a zaben shekarar 2027.

Farfesa Babagana Zulum ya bayyana cewa har yanzu bai san wanda zai gaje shi ba bayan karewar wa’adinsa a watan Mayun shekarar 2027.

Mai girma gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa ta maida hankali ne wajen ƙarfafa tsaro da kuma samar da ci gaban da al’ummar jihar ke buƙata.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com