Gwamna Zulum ya maye gurbin kwamishinoni 19 da ya tsige daga muƙamansu

Gwamna Zulum ya maye gurbin kwamishinoni 19 da ya tsige daga muƙamansu

  • Gwamnan Borno ya ba sabbin kwamishinoni 19 rantsuwar kama aiki watanni biyu bayan rushe majalisar zartarwar gwamnatinsa
  • Farfesa Babagana Umaru Zulum ya roki waɗan da Allah ya ba muƙaman su taimaka masa wajen sauke nauyin da ke kansa
  • Ya bukaci su rinka mutunta lokaci da yin aikin da ya dace don zama abun misali ga ma'aikatan da ke ƙasa da su

Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum, ya ba sabbin kwamishinoni 19 rantsuwar kama aiki ranar Litinin, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wannan cigaban na zuwa ne watanni biyu bayan gwamna Zulum ya rushe baki ɗaya mambobin majalisar zartarwa ta jihar Borno gabanin fara zaɓen fidda gwanin jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

A Shirye Nake In Jagoranci Yaki da 'Yan Bindiga a Jihata, Gwamnan Bauchi

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum.
Gwamna Zulum ya maye gurbin kwamishinoni 19 da ya tsige daga muƙamansu Hoto: Bello Ibrahim Gwari/facebook
Asali: Facebook

Shugaban Alkalan jihar Borno, mai shari'a Kashin Zanna, shi ya shaida ratsuwar fara aiki ga sabbin kwamishinonin bisa wakilcin Alkalin Babbar Kotu, Mai Shari'a Fadawu Umaru.

Haka zalika taron ya shaida rantsuwar kama aiki ga sabon sakataren dindindin, Alhaji Abu Abadam, babban darakta a ma'aikatar Albarkatun ruwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zulum ya roƙi sabbin jami'am gwamnatin su yi koyi da jagoranci mai kyau da kwazo wajen tafiyar da harkokin gwamnati da aka ɗora musu nauyi.

Gwamnan ya yi kira gare su kada su ga girmansa ko suji kunya su rinƙa ba shi shawari masu kyau waɗan da zasu ɗaga jihar Borno zuwa mataki na gaba.

Ku haɗa kai da Sakatarori - Zulum

Farfesa Zulum ya shawarci kwamishinonin su ƙulla kyakkyawar alaƙa da Sakatarorin dindindin na ma'aikatin su.

Ya ce, "Ku rika gudanar da taro a kai a kai da masu ruwa da tsaki na ma'aikatun ku, sannan ku turo mun matsaya da shawarwarin da kuka cimma ta ofishin SSG."

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya ba 'yan bindigan jiharsa wa'adin kwana 10 su miƙa wuya ko a tura su Lahira

Daga ƙarshe ya nemi kwamishinonin su zama a sahun gaba wajen yin aikin da ya kamata, ya tuna musu lokutan aiki daga 8:00 na safe zuwa 4:00 na yama ban da ranar Jumu'a da ake tashi 12 na rana.

A wani labarin na daban kuma Hadimin gwamnan APC ya yi murabus daga muƙaminsa, ya nemi a ba shi miliyan N77.2m

Wani rikici ya ɓarke a gwamnatin jihar Imo yayin da mai ba da shawari na musamman kan harkokin siyasa ga gwamna ya aje aikinsa.

Batos Nwadike, ya bayyana cew a ya ɗauki matakin ne bisa tilas saboda an watsar da ofishinsa ba'a tura masa kasafin kuɗi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel