Dan Kwankwaso Ya Fadi Canjin da za a Kawo wa Kano bayan Sauya Sheka zuwa ADC

Dan Kwankwaso Ya Fadi Canjin da za a Kawo wa Kano bayan Sauya Sheka zuwa ADC

  • Tsohon Kwamishina a Kano, Mustapha Rabi'u Musa Kwankwaso ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar NNPP bayan nazari
  • Ya ce yana kan hanyar kammala shigarsa jam’iyyar hamayya ta ADC domin fara sabuwar tafiyar siyasa a jihar Kano
  • Ya bayyana cewa ADC na da damar kawo sauyi mai ma’ana a Kano da Najeriya bayan mahaifinsa ya koma can

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano –Mustapha Rabiu Kwankwaso, ɗan tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, zai bi sawun mahaifinsa.

Ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar NNPP, yana mai nuna shirin komawa jam’iyyar ADC domin kawo canji a Kano

Mustapha Kwankwaso ya ce suna son kawo canji a Kano
Gwamna Abba Kabir Yusuf, Mustapha Rabi'u Musa kwankwaso Hoto: Mustapha Rabi'u Kwankwaso
Source: Twitter

Mustapha Rabi'u Musa kwankwaso ya sanar da sauya sheƙar a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Litinin, 30 ga watan Maris 2026.

Kara karanta wannan

Bayan shiga ADC, Kwankwaso ya aika sako ga 'yan Najeriya kan zaben 2027

Ɗan Kwankwaso ya bar NNPP

Mustapha Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce ya ɗauki wannan mataki ne bayan dogon nazari da tunani kan makomar siyasar sa da kuma yadda zai fi bayar da gudunmawa ga al’umma.

Ya ce:

“Ina sanar da al’umma cewa daga yau na fice daga jam’iyyar NNPP.”

Wannan sanarwa tasa ta zo a daidai lokacin da ake ci gaba da sauye-sauyen siyasa a jihar Kano da ma Najeriya baki ɗaya.

A halin yanzu, manyan ‘yan siyasa ke sauya jam’iyyunsu domin neman damar ci gaba da tasiri a harkokin siyasa da ƙoƙarin canja gwamnatin Bola Tinubu

Ɗan Kwankwaso zai koma ADC

Mustapha, wanda ya kasance ɗaya daga cikin fitattun ƴan Kwankwasiyya, ya jaddada cewa wannan mataki ba kawai sauyi ba ne na jam’iyya, wata sabuwar hanya ce da yake ganin za ta ba shi damar cimma manufofin da ya sanya a gaba.

Mustapha Kwankwaso zai koma ADC don a kawo canji
Tsohon Kwamishina a gwamnatin Kano, Mustapha Rabi'u Kwankwaso a ofis Hoto: Mustapha Rabi'u Kwankwaso
Source: Facebook

A cewar Mustapha Kwankwaso, a halin yanzu yana kan hanyar kammala shigarsa cikin jam’iyyar ADC, yana mai bayyana kwarin gwiwa a kan sabon matakin da zai ɗauka a fagen siyasa.

Kara karanta wannan

Kwankwaso, Atiku, Obi sun hade kai, sun shirya kayar da Tinubu a zaben 2027

Ya bayyana cewa shawarar komawa ADC ta samo asali ne daga imanin da yake da shi cewa jam’iyyar na da kyakkyawar dama wajen kawo sauyi mai ma’ana a Najeriya, musamman a jihar Kano.

A cewarsa, hangen nesa da manufofin jam’iyyar ADC suna samar da ingantaccen dandali da zai taimaka wajen tabbatar da shugabanci nagari, bunƙasa tattalin arziki, da kuma inganta rayuwar al’umma gaba ɗaya.

Mustapha ya kuma bayyana cewa yana da niyyar yin aiki tare da masu ruwa da tsaki masu ra’ayi iri ɗaya, domin cimma muradun ci gaba na bai ɗaya, tare da tabbatar da cewa an samar da mafita ga matsalolin da ke addabar al’umma.

Kwankwaso ya zama ɗan DC

A baya, mun wallafa cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi rajistar zama 'dan jam'iyyar ADC a hukumance tare da karbar katin ɗan jam'iyya a birnin Kano.

Manyan 'yan siyasa kamar Peter Obi da David Mark da Aminu Tambuwal sun halarci taron karbar Kwankwaso zuwa jam'iyyar 'yan adawa gabanin zaben 2027.

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa ya bar jam'iyyar NNPP ne domin samar da sabon tsarin siyasa da zai tafi da kowa a 2027 yayin da ake tunkarar babban zaɓe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng