Tinubu: Arewa Ta Tsakiya Ta Gama Shiri, Ta Fitar da 'Dan Takarar Shugaban Kasa a 2027
- Jam'iyyar APC ta yankin Arewa ta Tsakiya ta amince da Bola Ahmed Tinubu a matsayin ɗan takararta a babban zabe mai zuwa
- Manyan jam'iyya, gwamnoni da shugabannin jam’iyya ne suka yanke wannan shawara bayan an yi zama na musamman
- Sun bayyana dalilansu na sake neman Bola Tinubu ya nemi kujerar da ya ke kai a yanzu duk da hadakar yan adawa
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Jam’iyyar APC ta yankin Arewa ta Tsakiya ta hakura da batun a fafataa cikin gida kafin fitar da dan takarar Shugaban kasa a 2027.
Jam'iyyar ta bayyana cewa ta riga ta cimma matsaya wajen amincewa da wanda suke fatan zai fafata da sauran jam'iyyun adawa a zabe mai zuwa.

Source: Twitter
Jaridar Punch ta wallafa cewa manyan shiyyar sun amince da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sake neman kujerar da ya ke kai.
'Yan Arewa sun goyi bayan takarar Bola Tinubu
Leadeship ta wallafa cewa jagororin yankin sun amince da cewa akwai kwararan dalilai da suka sa su amincewa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake neman koma wa ofis.
An cimma wannan matsaya ne a ranar Laraba, 25 ga watan Maris, 2026 a taron jam’iyyar na yankin da aka gudanar a dakin taro na Aliyu Akwe Doma da ke gidan gwamnati a Lafia, jihar Nasarawa.
Taron ya haɗa da gwamnoni, sanatoci, tsofaffin ministoci da sauran masu ruwa da tsaki daga dukkannin jihohin yankin.
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, wanda shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin yankin, ya mara wa wannan kudiri baya.
Ya bayyana cewa sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin Tinubu ke yi ne suka sa gwamnoni ke goyon bayan sake tsayawarsa takara.

Kara karanta wannan
Tsohon mataimakin gwamna na kwance, wani ya rasu a haɗarin da ya rutsa da wakilan APC
Dalilan 'yan APC na sake aminta da Tinubu
Abdullahi Sule ya bayyana cewa wasu daga cikin gwamnoni sun samu damar gudanar da ayyukansu ba tare da karɓar rance daga bankuna ba, sakamakon manufofin Tinubu.

Source: Facebook
Haka kuma ya bayyana cewa yawan gwamnonin APC ya kai 31, abin da ya nuna ƙaruwa da karɓuwar jam’iyyar a faɗin ƙasar.
Tsohon shugaban majalisar dattawa kuma Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, shi ne ya gabatar da kudirin amincewa da Tinubu.
Bayan gabatar da kudirin, dukkanin wadada ke taron sun amince. Akume ya jaddada muhimmancin yankin Arewa ta Tsakiya ga nasarar APC a ƙasa baki ɗaya.
Akume ya bukaci ‘yan jam’iyya da kada su yi sakaci duk da wannan goyon baya, yana mai cewa dole ne a yi aiki tukuru domin samun nasara a zaɓen 2027.
Ya kuma lura cewa APC ce ke mulkin dukkannin jihohin yankin, ciki har da Benue, Kogi, Niger, Nasarawa, Plateau da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja.
Shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ta bakin wakilinsa, ya yaba wa yankin bisa biyayya da goyon bayan da yake bai wa jam’iyyar da kuma manufofin Tinubu.
Wakilan jam'iyyar APC sun yi hadari
A baya, kun ji cewa taron shiyya na APC ya bar baya mara dadi sakamakon mummunan hadarin mota da ya rutsa da wasu daga cikin wakilan jam'iyya.
Rahotanni sun tabbatar da cewa wani mutum ya rasu,a hatsarin da ya rutsa da tsohon mataimakin gwamna a Katsina a lokacin da suke shirin halartar taron APC.
Lamarin ya rutsa da wakilan APC da ke kan hanyarsu zuwa taron yankin Arewa maso Yamma wanda aka yi a Kaduna, wadanda suka rasu suna kwance a asibiti.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

