Gawuna Ya Yi 'Batan Dabo yayin da Tinubu ke Neman Hana Shi Komawa Kwankwasiyya

Gawuna Ya Yi 'Batan Dabo yayin da Tinubu ke Neman Hana Shi Komawa Kwankwasiyya

  • Tsohon dan takarar Gwamnan Kano Nasiru Yusuf Gawuna ya fara tayar wa da hankalin APC a matakin kasa
  • Rahotanni 'yan kwanakin nan sun fara nuna yadda Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da Gawuna ke 'dasawa sosai
  • Sai dai Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya shiga ya fara neman hana 'kara karfin alaka a tsakanin Kwankwaso da Gawuna

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano kuma ɗan takarar gwamna na APC a 2023, Nasir Yusuf Gawuna, yana neman tayar da jam'iyyarsa tsaye.

Wannan ya biyo bayan umarnin Shugaba Bola Tinubu ga wasu manyan shugabannin jam’iyyar da su dakatar da shirinsa na sauya sheka zuwa tafiyar Kwankwasiyya.

Gawuna ya tashi APC tsaye
Tsohon dan takarar gwamnan Kano Nasiru Yusuf Gawuna, Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: Nasiru Yusuf Gawuna/Bayo Onanuga
Source: Facebook

A labarin da ya kebanta ga jaridar Daily Nigerian, ana hasashen sauya sheka zuwa Kwankwasiyya zai kai Gawuna jam’iyyar ADC.

Kara karanta wannan

'Falle 1 ce,' Shirin da Kwankwaso ya fara yi na kifar da gwamnatin Abba a 2027

Ana tsoron Gawuna zai hada kai da Kwankwaso

Rahoton ya ce ana ganin cewa shirin Gawuna na haɗa kai da Sanata Rabiu Kwankwaso domin kayar da Gwamna Abba Kabir Yusuf a zaɓen 2027 yana samun karɓuwa sosai a Kano.

Yayin da wannan mataki ke haifar da ce-ce-ku-ce a cikin APC, a ɓangaren Kwankwasiyya kuwa ana farin ciki da wannan yiwuwar sauya sheka.

Har ila yau, wata ƙungiya ƙarƙashin jagorancin limamin masallacin Gawuna, Ahmed Sabo Usman, ta kai masa gaisuwar Sallah ga Kwankwaso a gidansa da ke Miller Road a Kano.

Gawuna na kokarin hade wa da Kwankwaso
Gawuna tare da Kwankwaso da suka hadu a filin jirgi Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Majiyoyi daga cikin jam’iyyar sun bayyana cewa an kasa samun Gawuna a ‘yan kwanakin nan, abin da ke ƙara jawo hasashe cewa yana gudanar da tattaunawar siyasa a wajen ƙasar.

An ce ya tafi ƙasar Saudiyya a lokacin Ramadan domin yin Umrah, kuma bayan kammala watan bai dawo ba, sai ma aka ce ya wuce hutu a wata ƙasa ta Arewacin Afrika.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya yi magana kan shirin hada tafiya da Nasiru Gawuna a Kano

Gawuna ba ya samuwa a waya

Rahoton ya bayyana cewa Gawuna ya sanya wayarsa a yanayin “Do Not Disturb” domin kauce wa matsin lamba daga shugabannin jam’iyyar da ke ƙoƙarin hana shi sauya sheka.

Wannan yunkuri na Gawuna ya girgiza APC a Kano, har ta kai ga gwamna Abba Yusuf ya nemi taimakon shugaban ƙasa domin shawo kansa kada ya fice daga jam’iyyar.

Rahotanni sun nuna cewa an tura wani Sanata mai ƙarfi daga Zamfara tare da mai ba shugaban ƙasa shawara domin jagorantar wannan yunƙuri.

Haka kuma, ana tunanin ba shi tikitin takarar Sanatan Kano ta Tsakiya kai tsaye a 2027 idan ya amince ya ci gaba da zama a APC.

Shugaban ƙasa na damuwa cewa ficewar Gawuna ba wai kawai za ta shafi burin wa’adin mulki na biyu na gwamna Abba Yusuf ba, har ma da ƙarfin APC a Kano gaba ɗaya.

Kwankwaso ya magantu kan Gawuna

A baya, mun wallafa cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya fito ya yabawa dan takarar gwamnan Kano a karkashin jam'iyyar APC a zaben 2023, Nasiru Yusuf Gawuna.

Kara karanta wannan

Awanni da raka mahaifinsa kotu, Bello El-Rufai ya ziyarci babban dan siyasa a Kaduna

Jagoran NNPP a Najeriya ya yi bayani ne yayin da wata tawaga ta musamman da ta kai masa ziyarar gaisuwar Sallah a gidan shi da ke Miller Road a jihar Kano.

Hakan na zuwa ne bayan gwamna Abba Kabir Yusuf da ya lashe zabe a NNPP ya koma APC, ya raba hanyar siyasa da Sanata Rabiu Kwankwaso a baya-bayan nan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng