Fitaccen ɗan Kannywood da Ya Tallata APC a 2023 Ya Fara Neman Rusa Tinubu a 2027

Fitaccen ɗan Kannywood da Ya Tallata APC a 2023 Ya Fara Neman Rusa Tinubu a 2027

  • Fitaccen jarumin Kannywood, Sadiq Sani Sadiq, ya fara fafutukar wayar da kan jama’a game da alaƙar rashin tsaro da shugabanci
  • Ya zargi gwamnatin Bola Tinubu da rashin kulawa da yankin Arewa, inda ya jerin jihohin da ke cikin masifar ta'addanci
  • Jama’a sun fara bayyana ra’ayoyinsu mabambanta kan wannan kira ganin yawanci ƴan Kannywood na tare da gwamnati

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Jihar Kano – Fitaccen jarumin masana’antar Kannywood, Sadiq Sani Sadiq, ya fara wani gangami na wayar da kan jama’a a matakin ƙasa a kan tsaro

An hango jarumin a titunan kasar nan inda yake kira ga al’ummar Arewa da su tashi tsaye kan matsalar tsaro da ke ƙara ta’azzara.

An fara samun masu adawa da Tinubu a Kannywood
Shugaban Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Wani bidiyo da wani Sulaiman Uwais Kafin Hausa ya wallafa a shafin X ya nuna jarumin yana bayyana damuwarsa kan yadda matsalar rashin tsaro ke ƙara kamari a jihohin Arewa.

Kara karanta wannan

Kwalliyar Sallah ta jefa matasa a matsala, Hisbah kama sama da mutum 600 a Kano

Jarumin Kannywood ya sako Tinubu a gaba

A cikin jawabin nasa, Sani Sadiq ya yi zargin cewa Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu BA ya kaunar mutanen Arewa, shi ya sa na suke cikin tashin hankali.

Ya ce:

"Allah mun tuba wajen zaben wannan gwamnatin ta Tinubu. Mu kiyaye saboda karara ta nuna cewa ba masoyin al'ummar Arewa ba ne.
Sadik Sani Sadik zai yi adawa da Tinubu
Fitaccen jarumi a Kannywood, Sadik Sani Sadik Hoto: Manuniya
Source: UGC

Ya ƙara da cewa:

"Ga kwatance nan, ka duba abubuwan da suke faru wa a jihar Zamfara, ka duba abubuwan da suke faruwa a jihar Katsina , ka duba abubuwan da suke faru wa a Kebbi, Sakkwato, Neja, Kwara, Binuwai, Filato Borno, Yobe, Gombe ga shi Borno na ta dauka."

Jarumin ya kuma jaddada cewa lokaci ya yi da al’ummar Arewa za su farka su yi magana kan halin da suke ciki, yana mai cewa ba za su ci gaba da zama suna kallo ba yayin da matsalolin tsaro ke ƙaruwa.

Martanin jama’a ga kiran ɗan Kannywood

Kara karanta wannan

Faransa za ta bi sahun Amurka, za a kawo wa Najeriya agaji a kan rashin tsaro

Mutane da dama sun fara bayyana ra’ayoyinsu a kafafen sada zumunta, inda wasu ke goyon bayan wannan kira, yayin da wasu ke nuna shakku.

Wani mai amfani da X, @Jimada_Gana, ya ce:

"Kaji maganar gaskiya. Kun lura shi kadai ne ke wannan fafutuka? Abokan aikinsa sun sayar da ƙuri'arsu saboda buhun shinkafa da N20,000."

@Mustaphajibia ya yi addu’a ga jarumin, inda ya ce:

"Allah ya tsare shi."

A nasa bangaren, @mynameisada3 ya bayyana cewa matsalar tsaro ta shafi kowa, yana mai cewa:

"Matsalar tsaro ta shafi kowa ko kana Gabas, Yamma, Arewa ko Kudu. Ina alfahari da shi da wannan kira."

@SagirKabir32035 ya bayyana damuwa kan halin da ake ciki, inda ya ce:

"A cire azzalumi a zabi azzalumi, matsalar mu ba nan take ba ta wuce nan. Ta wuce duk inda muke tunani Allah Ya kawo muna dauki na gaggawa. Amin."

Bashin gwamnatin Tinubu zai jawo matsala

A baya, kun ji cewa ƙungiyar ƴan kwangila na cikin gida ta AICAN ta yi barazanar dirar mikiya a babban taron APC da aka shirya za a yi a Abuja.

Kara karanta wannan

Rabon shinkafar Tinubu: Yadda ake 'bambance' Kudu da Arewa wajen tallafa wa mutane

Ƴan kwangila sun bayyana takaici a kan yadda hakkokinsu ke neman shiga mawuyacin hali duk da sun kammala aikin da gwamnati ta ba su lafiya lau.

Ƙungiyar ta bayyana cewa ƴaƴanta na neman a biya su Naira biliyan 150 a cikin awa 48 daga bashin ayyukan gwamnati da suka aiwatar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng