Kwankwaso Ya Yi Magana kan Shirin Hada Tafiya da Nasiru Gawuna a Kano

Kwankwaso Ya Yi Magana kan Shirin Hada Tafiya da Nasiru Gawuna a Kano

  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya fito ya yabawa dan takarar gwamnan Kano a karkashin jam'iyyar APC a zaben 2023, Nasiru Yusuf Gawuna
  • Jagoran NNPP a Najeriya ya yi bayani ne yayin da wata tawaga ta musamman da ta kai masa ziyara a gidan shi da ke Miller Road a jihar Kano
  • Hakan na zuwa ne bayan gwamna Abba Kabir Yusuf da ya lashe zabe a NNPP ya koma APC, ya raba hanyar siyasa da Rabiu Kwankwaso

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Siyasar Kano ta fara daukan sabon salo yayin da aka ji Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya fito yana yabon Nasiru Yusuf Gawuna.

A zaben 2023, Nasiru Gawuna ne ya yi wa APC takarar gwamna a Kano, inda ya fafata da dan takarar da Kwankwaso ya tsayar a NNPP, wato Abba Kabir Yusuf.

Kara karanta wannan

An zo wajen: Gwamna Abba ya yi magana kan lokacin cire jar hular Kwankwasiyya

Rabiu Musa Kwankwaso da Nasiru Yusuf Gawuna
Rabiu Kwanwaso da Nasiru Gawuna sun hadu a filin jirgin sama. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Legit ta tattaro bayanan da Kwankwaso ya yi ne a wani bidiyo da hadiminsa na musamman, Saifullahi Hassan ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Rabiu Kwankwaso ya yabawa Nasiru Gawuna

Madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Kwankwaso ya yabawa na hannun daman Abdullahi Ganduje, Nasiru Yusuf Gawuna a wani taro a Kano.

Da ya ke jawabi, Kwankwaso ya bayyana cewa:

"Gawuna yana ɗaya daga cikin kwamishinoni na masu daraja."
"Na ji kuna an cire bulo takwas aka kwashe ku aka kawo ku, dama katanga ɗaya ce. Wannan Allah ne kaɗai ya san dalilin abin da ya kawo shi nan, ya kawo ni nan har muka zama maƙwabta."

Dangane da rade-radin cewa Gawuna zai koma tafiyar Kwankwasiyya, Rabiu Kwankwaso ya ce:

"Kuma tunda na soma fara jin wannan zancen na yi farin ciki."

Alakar Kwankwaso da Gawuna

Sanata Rabiu Kwankwaso ya bayyana cewa duk da sabanin da suka samu a siyasance, Gawuna bai taba wata magana ta batanci ba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta fadi abin da ya hana Abba tarbar Sarki Sanusi a hawan Nasarawa

Kwankwaso ya kara da cewa Gawuna bai canja yadda ya ke girmama shi ba tun shekarun baya har zuwa yanzu, inda ya ce sun hadu a wurare.

Ya ce:

"Ban taɓa jin ya yi wata magana ta batanci ba, yana girmama ni sosai."
Rabiu Musa Kwankwaso
Jagoran NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso na jawabi a Kano. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Magana kan shari'ar zabe a Kano

Da ya ke tsokaci kan abubuwan da suka faru a baya, Kwankwaso ya nuna cewa Nasiru Gawuna ya nuna dattaku sosai a lokutan da suka dace.

Ya kara da cewa ko a lokacin shari'ar bayan zabe an matsa lamba ya saka hannu kan wata takarda amma ya ki, ya ce hakan abu ne da ya nuna nagartarsa.

"Ba yadda ba a yi da shi ba, ya sa hannu amma ya ce ba zai yi ba."

Ga bidiyon Kwankwaso da Abdulaziz Na'ibi ya saka a X:

Maganar cire jar hula a Kano

A wani labarin, mun kawo muku cewa Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta bayyana cewa har yanzu lokacin cire jar hula bai yi ba duk da sauya sheka.

Mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya sanar da haka bayan sanya hoton Abba Kabir ba tare da jar hula ba.

Sanya jar hula alama ce ta tafiyar Kwankwasiyya da Rabiu Kwankwaso ke jagoranta wanda Abba Kabir ya ki cire ta duk da raba hanya da shi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng