Awanni da Raka Mahaifinsa Kotun, Bello El-Rufai Ya Ziyarci Babban Dan Siyasa a Kaduna

Awanni da Raka Mahaifinsa Kotun, Bello El-Rufai Ya Ziyarci Babban Dan Siyasa a Kaduna

  • Ɗan tsohon gwamnan Kaduna, Bello El-Rufai ya ziyarci Sanata Lawal Adamu Usman yin kaɗan bayan raka mahaifinsa kotu
  • A ranar Talata, 24 ga watan Maris, 2025 ne hukumar yaki da rashawa mai zaman kanta ta ƙasa, ICPC ta gurfanar da El-Rufa'i a gaban kotun Kaduna
  • Sai dai rahotanni sun nuna cewa duk da Sanatan ya nufi kotun domin nuna goyon bayansa ga El-Rufa'i, bai samu dama ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna –Ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kaduna ta Arewa, Hon. Mohammed Bello El-Rufai, ya kai ziyara gidan Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya,Lawal Adamu Usman.

Ya bayyana cewa ya kai ziyara ga Sanata da aka fi sani da Mr. LA, domin nuna masa godiya da kuma jinjina kan goyon bayan da ya nuna yayin da aka kai mahaifinsa, Nasir El-Rufa'i kotu.

Kara karanta wannan

Makaman da Iran ta harba sun gigita Isra'ila, an ji barnar da suka yi

Bello El-Rufa'i ya ziyarci Sanatan Kaduna ta Tsakiya
Sanatan Kaduna ta Tsakiya Lawal Adamu Usman tare da Bello El-Rufa'i Hoto:@B_ELRUFAI
Source: Twitter

A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, Bello El-Rufai ya jinjina wa Sanatan bisa tsaya wa da ya yi tare da iyalan El-Rufa'i duk da halin da ya shiga da ICPC.

Nasir El-Rufa'i ya yaba wa Sanatan Kaduna

Bello El-Rufa'i ya ce ayyukan tallafawa al’umma da Sanatan ke aiwatarwa sun amfani jama’a da dama, yana mai cewa.

Ya bayyana cewa:

"Ayyukan tallafa wa da ya yi sun kai ga mutane da dama a shiyyar Kaduna ta Arewa."

Bello El-Rufai ya bayyana cewa ya kai ziyarar ne bayan ya raka mahaifinsa, Malam Nasir El-Rufai, zuwa babbar kotun Kaduna.

Ya ce ya kai ziyarar domin godewa Sanatan bisa matsayinsa na gaskiya da kuma goyon bayan da ya nuna ga iyalinsu. A cewarsa, Sanata Lawal Adamu Usman ya yi ƙoƙarin zuwa kotu domin nuna goyon baya kai tsaye, amma hakan bai yiwu ba saboda an rufe hanya.

Kara karanta wannan

Yadda matan El Rufai suka fuskanci turjiya wajen jami'an tsaro a kotu

Rokon El-Rufa'i ga kamar Kaduna

Hon. Bello El-Rufai ya kuma roƙi al’umma da su taya shi godewa Sanatan tare da yi masa addu’a, domin cikakken haɗin kai da ya ke ba su.

Bello El-Rufai ya gode wa Sanatan da ke tare da mahaifinsa
Hon Bello El-Rufa'i a zauren majalisa Hoto: Bello El-Rufa'i
Source: Twitter

Haka kuma ya bayyana matuƙar godiya ga shawarwari da goyon bayan da Sanatan ke ba su cikin shekaru uku da suka gabata.

Bello El-Rufai ya gode wa duk waɗanda ke nuna goyon baya ga mahaifinsa, yana mai cewa, ba za su manta da wannan alheri ba.

Alkali ya dauki mataki kan shari'ar El-Rufa'i

A baya, mun wallafa cewa babbar Kotun Tarayya ta dage sauraron bukatar belin Nasir El-Rufai zuwa karshen watan Maris bayan ICPC ta gurfanar da shi kan zargin cin hanci.

An haramta wa manema labarai shiga cikin zauren kotun a Kaduna yayin da jami'an tsaro suka mamaye ko'ina domin hana barkewar tarzoma a ranar Talata 24 ga watan Maris, 2026.

Tsohon gwamnan yana fuskantar zarge-zargen almundahana da dukiyar kasa da kuma halatta kudaden haram a gaban kotuna daban-daban yayin da ya sha bayyana cewa zai kare kansa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng