APC Ta Yi Rashi a Kaduna, Hadimin Gwamna Ya Sauya Sheka zuwa ADC

APC Ta Yi Rashi a Kaduna, Hadimin Gwamna Ya Sauya Sheka zuwa ADC

  • Jam'iyya mai mulki ta APC na ci gaba da rasa masu 'ya'yanta yayin da ADC ke shirin tarkato kawunan 'yan adawa gabanin 2027
  • Daya daga cikin hadimin Uba Sani na Kaduna Hon. Yusuf Umar Garkuwa ya yi murabus daga mukaminsa na mai ba gwamna shawara
  • Garkuwa ya fice daga jam’iyyar APC tare da mika shaidarsa na zama dan jam'iyya yayin da ya ke shirin hade wa da 'yan adawa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna – Daya daga cikin jami'an gwamnatin jihar Kaduna ya ajiye mukaminsa tare da rabuwa da jam'iyya mai mulki.

Honarabul Yusuf Umar Garkuwa, wanda ke rike da mukamin Mai ba Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, shawara na musamman, ya sanar da yin murabus daga mukaminsa.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda da jami'an tsaro sun fafata ana shirin kama jagoran yan bindiga a Kano

ADC ta samu karuwa a jihar Kaduna
Honorabul Yusuf Umar Garkuwa, tsohon hadimin gwamna da ya bar APC Hoto; ADC Party
Source: Facebook

ADC Vanguard ta wallafa a shafin X cewa haka kuma Honorabul Yusuf Umar Garkuwa ya sanar da ficewa daga jam’iyyar APC.

Jami'in gwamnatin Kaduna ya bar APC

Sannan ADC Party ta wallafa a shafin Facebbok cewa rahotanni sun bayyana cewa Garkuwa ya dauki wannan mataki ne bayan dogon nazari da tuntuba da mabiyansa da na kusa da shi.

A cikin sanarwar da ya fitar, ya tabbatar da cewa ya mika takardar murabus dinsa ga gwamnatin jihar.

Sanarwar ta kara da cewa ya jaddada cewa matakin da ya dauka ba na gaggawa ba ne, illa dai sakamakon abin da ya kira bukatar sabuwar tafiyar siyasa.

Haka kuma, ya bayyana cewa ya mayar da katin shaidar kasancewarsa dan jam’iyyar APC, wanda ke nuna cewa ya kawo karshen duk wata alaka da jam’iyyar da ya dade yana cikinta.

Ana hasashen tshon hadimin zai koma ADC

Garkuwa na iya girgiza siyasar jihar Kaduna, musamman ganin kusancinsa da gwamnatin jihar da kuma irin rawar da ya taka a baya.

Kara karanta wannan

Kano: Hadimin Ganduje ya sauya sheka, ya bar ubangidansa a APC

Bayan ficewarsa daga APC, Hon. Garkuwa ya sanar da cewa ya shiga sabuwar hadakar jam’iyyar ADC.

A cewarsa, ya zabi shiga wannan hadaka ne saboda yadda yake ganin tana da manufofi da tsare-tsaren da suka dace da burinsa na ganin an kawo sauyi mai ma’ana a harkokin mulki da shugabanci.

Garkuwa ya bar gwamnatin Uba Sani
Gwamna Uba Sani yana jawabi a wani taro Hoto: Uba Sani
Source: Facebook

Ya kuma yi kira ga magoya bayansa da su biyo shi a wannan sabuwar tafiya, yana mai cewa lokaci ya yi da za a samar da sabbin hanyoyi da za su inganta rayuwar al’umma.

Sai dai har zuwa yanzu, babu wata sanarwa kai tsaye daga gwamnatin jihar Kaduna ko jam’iyyar APC dangane da murabus din.

Kwankwaso yana gana wa da ADC

A baya, mun wallafa cewa kungiyar Kwankwasiyya ta yi tsokaci kan tafiyar siyasar tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Kwankwasiyya ta bayar da tabbacin cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yana tattaunawa da wasu jam'iyyun siyasa a Najeriya gabanin zaben 2027.

Mai magana da yawun Kwankwasiyya ya bayyana cewa ana yin tattaunawar ne domin samo jam'iyyar da za a yi amfani da ita gabanin babban zaben shekarar 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng