Ministoci 6 da Ka Iya Murabus daga Gwamnatin Tinubu domin Takara a Zaɓen 2027

Ministoci 6 da Ka Iya Murabus daga Gwamnatin Tinubu domin Takara a Zaɓen 2027

Akalla ministoci shida ne a gwamnatin Tinubu ake sa ran za su iya yin murabus kafin ranar 31 ga Maris domin shiga takarar zaben 2027 kamar yadda doka ta tanada.

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Gwamnatin Bola Tinubu ta fitar da umarni ga masu neman takara daga ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, tana bukatar duk masu mukaman siyasa su sauka kafin shiga zaben fidda gwani na jam’iyyunsu.

Ministocin da ake sa ran za su yi murabus domin neman takara
Ministan kasashen waje, Yusuf Tuggar, ministan sufuri, Saidu Alkali da ministan noma, Abubakar Kyari. Hoto: Federal Ministry of Foreign Affairs, Federal Ministry of Transportation.
Source: Facebook

Ministocin da ake ganin za su yi murabus

Wannan mataki ya biyo bayan umarnin shugaban kasa ga dukkan mukarraban siyasa da ke da niyyar tsayawa takara a zaben 2027, cewar rahoton Punch.

Sanarwar ta shafi dukkan mukarraban shugaban kasa, ciki har da ministoci, masu ba da shawara da shugabannin hukumomi.

Legit Hausa ta duba ministocin da ake tsammanin za su ajiye aiki domin neman takara daban-daban a zaben 2027.

Kara karanta wannan

Zai shiga APC ne? Sule Lamido ya bude kofar ganawa da Shugaba Bola Tinubu

1. Ministan lafiya, Muhammad Ali Pate - Bauchi

Ministan lafiya da walwalar jama’a, Muhammad Ali Pate, kwararre ne a fannin kiwon lafiya wanda ke da gogewa a matakin kasa da na duniya.

A baya ya taba rike mukamin karamin ministan lafiya na Najeriya daga Yuli 2011 zuwa Yuli 2013 a karkashin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.

Pate ya taba tsayawa takarar gwamnan Bauchi a baya, kuma har yanzu yana da tasiri sosai a siyasar jihar, wanda ke sanya shi cikin jerin wadanda ake ganin za su iya sake tsayawa takara.

Majiyoyi sun nuna cewa wasu kungiyoyi na ci gaba da bayyana shi a matsayin babban dan takara mai karfi a zaben gwamnan Bauchi na 2027.

Pate zai nemi takarar gwamna a Bauchi
Ministan lafiya a Najeriya, Mohammed Ali Pate. Hoto: Federal Ministry of Health.
Source: Getty Images

2. Ministan noma, Abubakar Kyari - Borno

An fara zaben ministan noma da samar da abinci, Abubakar Kyari a majalisar wakilai a shekarar 1998 a lokacin mulkin soja na Sani Abacha.

A 'yan shekarun bayan nan, ya yi fice a cikin jam’iyyar APC, inda ya rike mukamin mataimakin shugaban jam’iyya na kasa (Arewa).

Kara karanta wannan

Kwana ya kare: Hadimin gwamna ya yanke jiki ya fadi, ya mutu a wurin taro

An zabe shi sanata a shekarar 2015 karkashin APC da kuma 2019, inda ya yi aiki har zuwa Afrilu 2022 lokacin da ya yi murabus domin karbar mukamin mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa.

Ya kuma rike mukamin mukaddashin shugaban APC na kasa bayan murabus din Abdullahi Adamu, kafin Bola Tinubu ya nada shi a matsayin ministan noma da samar da abinci a watan Agustan 2023, cewar rahoton Tribune

Duk da cewa bai bayyana aniyarsa a hukumance ba, kungiyoyi da dama ciki har da Borno Social Media Frontiers (BSF) sun nuna shi a matsayin wanda zai iya tsayawa takarar gadon gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum.

Ana sa ran Kyari zai maye gurbin Zulum a Borno
Ministan noma a Najeriya, Abubakar Kyari. Hoto: Bank of Agriculture Ltd.
Source: Facebook

3. Ministan sufuri, Saidu Ahmed Alkali - Gombe

Ministan sufuri, Saidu Alkali, tsohon sanata ne da ya wakilci Gombe ta Arewa a majalisun dattawa na 6, 7 da 9, kuma ana ganin yana aiki daga Abuja domin samun tikitin gwamnan APC a Gombe.

Rayuwar siyasarsa ta hada da aiki a bangaren majalisa da na zartarwa, a Ana baya ya taba zama kwamishinan yada labarai a Gombe, sannan daga bisani ya shugabanci kwamitin majalisar dattawa kan rundunar sojin sama ta Najeriya.

Kara karanta wannan

Juyin mulki: Tinubu ya tsallake rijiya, an gano wani mugun shiri da sojoji suka yi na kwace Aso Rock

Kwarewarsa da kuma alakar siyasa da ya gina sun sanya mutane da dama ke ganin yana da karfin samun tikitin gwamnan APC a jihar, cewar Daily Trust.

Saidu Alkali na daga cikin wadanda ke son kujerar gwamnan Gombe
Ministan sufuri a Najeriya, Sanata Saidu Ahmed Alkali. Hoto: Federal Ministry of Tranportation.
Source: Facebook

4. Ministan harkokin waje, Yusuf Tuggar - Bauchi

Ana sa ran ministan harkokin waje, Yusuf Maitama Tuggar, zai yi tunanin barin mukaminsa domin neman zama gwamnan Bauchi, lamarin da zai iya haifar da gasa a cikin jam’iyyar APC.

A baya ya taba zama dan majalisar wakilai daga 2007 zuwa 2011, inda ya wakilci mazabar Gamawa, kuma ya taba tsayawa takarar gwamna sau biyu, cewar BusinessDay.

Burinsa na zama gwamna ya fara tun 2011 lokacin da ya tsaya karkashin jam’iyyar CPC, sannan ya sake gwadawa a 2015 amma bai samu nasara ba a zaben fidda gwani na APC.

Wata kungiya a Bauchi mai suna 'Bauchi South Concern Citizens Movement' ta bukace shi da ya tsaya takarar gwamna a 2027, tana mai cewa lokaci ya yi da mulki zai koma Bauchi ta Arewa bayan shekaru na shugabanci daga Bauchi ta Kudu.

Tuggar ka iya ajiye mukamin minista domin siyasa a Bauchi
Ministan harkokin kasashen waje, Yusuf Tuggar. Hoto: Yusuf Maitama Tuggar.
Source: Twitter

5. Ministan sadarwa, Bosun Tijani - Ogun

An san Ministan sadarwa, kirkire-kirkire da tattalin arzikin zamani, Bosun Tijani sosai da gogewarsa a fannin fasaha.

Kara karanta wannan

Seyi Tinubu ya fadi abin da mahaifinsa ke yi wa Najeriya da ba a sani ba

Tun bayan nadinsa, ya mayar da hankali kan inganta kayayyakin sadarwa na zamani, tallafawa sababbin kamfanoni da kuma bunkasa tattalin arziki ta hanyar fasaha.

Ko da yake bai bayyana aniyarsa a hukumance ba na tsayawa takara, ana danganta Tijani da yiwuwar tsayawa takarar gwamnan Ogun a shekarar 2027, kamar yadda ThisDay ta ruwaito.

Ana sa ran Tijani zai nemi takara a Ogun
Ministan sadarwa a Najeriya, Bosun Tijani. Hoto: Ministry of Communication and Digital Economy.
Source: Twitter

6. Ministan makamashi, Bayo Adelabu - Oyo

Bayo Adelabu na daga cikin mutane da ake ganin suna shirin ficewa daga mukamin minista.

Adelabu tsohon mataimakin gwamnan Babban Bankin Nigeria ne, kuma ya gina karfin siyasarsa a Oyo cikin shekaru 10 da suka wuce.

Adelabu ya tsaya takarar gwamna a 2019 karkashin APC sannan ya sake tsayawa a 2023 karkashin jam’iyyar Accord, amma ya sha kaye a hannun gwamna Seyi Makinde sau biyu.

Rahoton Legit Hausa ya nuna cewa Adelabu ya bayyana a watan Oktoba 2025 cewa lokaci ya yi da zai zama gwamnan Oyo a 2027.

Adelabu ya nuna sha'awar neman gwamnan Oyo
Ministan makamashi a Najeriya, Adebayo Adelabu. Hoto: Bayo Adelabu.
Source: Twitter

Ministocin da aka rasa a gwamnatin Tinubu

A baya, an ji cewa tun bayan darewa karagar mulki a 2023, Shugaba Bola Tinubu ya sallami ministoci biyar a gwamnatinsa.

Kara karanta wannan

Zaɓen 2027 ya matso: Shugaba Tinubu ya umarci ministoci, hadimai su yi murabus

Majiyoyi sun tabbatar da cewa akwai wasu daga ministoci da suka yi murabus a karan kansu saboda dalilai daban daban.

A ranar Talata 7 ga watan Oktobar 2025, an samu karin minista daya, Uche Nnaji da ya yi murabus daga gwamnatin Tinubu tun kafin a dakatar da shi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.