Jerin Laifuffukan Zabe 10 da Hukuncinsu da Ya Kamata Ku Sani kafin Zaben 2027 a Najeriya

Jerin Laifuffukan Zabe 10 da Hukuncinsu da Ya Kamata Ku Sani kafin Zaben 2027 a Najeriya

Abuja, Nigeria - Yayin da zaɓen 2027 ke ƙaratowa, akwai bukatar 'yan Najeriya su san abubuwan da suke laifi ne a harkokin zabe da hukuncin da aka tanada ga duk wanda ya taka doka.

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Tuni dai duk wasu masu ruwa da tsaki a harkokin shirya zabe a Najeriya, jam'iyyun siyasa da hukumomin tsaro suka fara shirin tunkarar babban zaben 2027 mai zuwa.

Hukumar INEC.
Tambarin hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) Hoto: INEC Nigeria
Source: Twitter

INEC ta fara shirye-shiryen zaben 2027

Hukumar Zaben Najeriya (INEC) ta fitar da jadawalin zaben 2027 a shafinta na Facebok, wanda ya kunshi ranakun da za a yi zabukan shugaban kasa, gwamnoni da 'yan Majalisar tarayya da na jihohi.

A cikin wannan yanayi, yana da kyau a sani cewa zaɓukan Najeriya na gudana ne karkashin kundin tsarin mulki, dokar zaɓe (wadda aka yi wa gyara), da kuma ƙa'idojin hukumar INEC.

Kara karanta wannan

Rabon shinkafar Tinubu: Yadda ake 'bambance' Kudu da Arewa wajen tallafa wa mutane

Duk da cewa waɗannan dokoki sun ba kowa damar kafa ƙungiya, jefa ƙuri'a, da shiga harkokin siyasa, sun kuma tanadi tsauraran hukunci ga duk wanda ya keta su, wanda ya haɗa da tara, ɗaurin kurkuku, ko duka biyun.

Wasu laifuffukan zabe da hukuncinsu

Legit Hausa ta tattaro cewa duk wanda aka samu da karya waɗannan dokoki, jami'an tsaro za su iya kama shi, su gurfanar da shi, kuma a hukunta shi bayan gudanar da bincike.

Hukumar INEC ta wallafa wadannan laifuffuka da hukuncin da aka tanadar ga duk wanda ya aikata su a shafinta na yanar gizo. Ga su kamar haka:

1. Laifuffukan katin zabe (PVC)

A tanadin dokar zaben Najeriya, yin rajista fiye da sau ɗaya ko mallakar katin zaɓe ba bisa ƙa'ida ba laifi ne da ka iya janyo tarar N100,000 ko ɗaurin shekara ɗaya, ko duka biyun.

Ha zalika, bayar da bayanan ƙarya yayin rajistar zabe shi ma laifi ne, kuma duk wanda aka kama zai fuskanci hukuncin tarar N500,000 ko watanni 12 a gidan yari.

Sannan hana wani yin rajista bayan ya cika sharudda na janyo tarar N500,000 ko ɗaurin shekaru biyar. Sai kuma yin sojan gona a matsayin jami'in rajista ko yin jabun katin zaɓe na iya janyo tarar N1,000,000 ko watanni 12 a gidan yari.

Kara karanta wannan

"Yan ta'adda na amfani da bidiyon azabtarwa don firgita al’umma": Masani ya bayar da mafita

Katunan zabe.
Wasu daga cikin katunan zabe (PVC) da INEC ta ba wadanda suka yi rijista Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

2. Laifuffukan neman takara

Hada jabun takardun neman takara, takardun sakamakon zaɓe, da mika takardar neman takara a mazabu daban-daban fiye da daya laifi ne bisa tanadin dokokin Najeriya.

Duk wanda aka kama ya aikata daya daga cikin wadannan laifuffuka, zai iya fuskanci hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari.

3. Takardun zaɓe da akwatuna

Mallakar takardar jefa ƙuri'a ba bisa ƙa'ida ba, buga takardun zaɓe na jabu, ko satar akwatun jefa kuri'u manyan laifuffuka ne a tsarin zaben Nanjeriya.

Dokar zabe ta tanadi hukuncin tarar N50m ko aƙalla ɗaurin shekaru 10, ko duka biyun ga duk wanda aka kama ya aikata daya daga cikinsu.

4. Amfani da katin zaben wani

A tanadin dokar zaben Najeriya, haramun ne wani ya yi amfani da katin zaben wani daban, haka nan ba a amince mutum ya mallaki katin zabe guda biyu ba.

Aikata daya daga cikin wadannan na iya jawo wa mutum tarar N1m ko daurin watanni 12 a gidan yari idan har aka gurfanar da shi a gaban kotu.

Kara karanta wannan

Ana shagulgulan Sallah, ƴan ta'adda sun sace jami'in gwamnatin jihar Kano

5. Dokar cancantar kada kuri'a

Dokar zaben Najeriya ta tanadi cewa duk wanda zai mallaki katin zabe sai ya zama cikakken 'dan kasa kuma ya kai shekaru 18 ko sama da haka.

Saboda haka, duk wanda ya yi zaɓe alhali bai cika wadannan sharudda ba, ko ya tunzura wani wanda bai cancanta ba ya yi zaɓe, zai fuskanci hukuncin tarar N500,000 ko watanni 12 a gidan yari.

Jami'an zabe.
Matasa yan bautar kasa (NYSC) da ake dauka su gudanar da zabe Hoto: @INECNigeria
Source: Twitter

6. Shirya sakamakon zabe na bogi

Jami'an zaben wucin gadi da INEC ke dauka a kowane zabe dole ne su sauke nauyin da aka dora masu, duk wanda ya gaza ba tare da kwakkwarar hujja ba zai iya fuskantar tarar N500,000 ko ɗaurin watanni 12.

Haka zalika, an tanadi hukuncin daurin shekaru uku ko zabin tara ga duk jami'in INEC da aka kama ya shirya sakamako na karya.

7. Cin hanci da sayen kuri'u

Sayen kuri'u, wanda ya zama ruwan dare a harkokin zaben Najeriya, ya saba wa dokar Najeriya kuma akwai hukunci mai tsanani da aka tanada ga wanda ya yi da wanda ya sayar da kuri'a.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta bullo da shirin ba da rancen kudin hawa jirgin sama a Najeriya

A dokar, bayarwa ko karɓar kuɗi ko kyaututtuka domin canza ra'ayin mai jefa ƙuri'a na iya jawo hukuncin tarar N500,000 ko watanni 12 a gidan yari.

8. Laifuffukan yakin neman zabe

Yin kamfe bayan lokacin da aka kayyade ya cika, amfani da kayan gwamnati ba daidai ba, ko mallakar makami a wurin taro ko rumfar zaɓe na iya janyo tarar N500,000 zuwa N2m ko ɗaurin shekaru biyu.

Bayan haka, doka ta tanadi hukuncin tarar N1m ko daurin shekara guda a gidan yari kan duk wanda aka kama da laifin yin barazana a lokacin yakin neman zabe.

9. Barazana ko tursasawa

Tursasa mutum ta hanyar amfani da maki ko jikkatawa domin tilasta masa ya kada ƙuri’a ko kuma ya ƙi kaɗa ƙuri’a, ko yi wa dan takara barazana duk laifi ne a dokar Najeriya.

Duk wanda ya aikata hakan zai iya fuskantar hukuncin biyan tarar N1m ko daurin shekaru uku a gidan gyaran hali.

10. Karya dokar kashe kuɗin kamfe

A dokar zaben Najeriya, an kayyade adadin kudin da kowane dan takara zai iya kashewa a kamfe da sauran harkokin neman kujerar mulki.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Gagarumar matsala ta tunkaro Isra'ila ana tsaka da yaki da Iran

An kuma tanadi cewa duk ɗan takarar da ya kashe kuɗi fiye da ƙa'idar da dokar zaɓe ta gindaya, zai biya tara tsakanin N100,000 zuwa N1m ko ɗaurin kurkuku.

Jam'iyyun siyasa da suka gaza mika rahoton kashe kudadensu ga hukumar zabe watau INEC za su biya tarar N1m, tare da ƙarin N200,000 a kowace rana da suka kara jinkiri.

Shugaba Tinubu
Shugaba Bola Ahmed Tinubu a wurin yakin neman zabe kafin 2023 Hoto: @OfficialAPCNig
Source: Twitter

Legit Hausa ta tuntubi wani masanin doka, Barista Tukur Badamasi, wanda ya shaida mana cewa aiwatar da wadannan dokokin zai kawo sauyi a tsarin zaben Najeriya.

"A bisa doka, duk wanda aka kama da laifi kuma aka gurfanar da shi, za a hukunta shi daidai da laifin da ya aikata, kuma wadannan tanade-tanaden za su tsaftace harkar zaben Najeriya.
"Matsalar kawai muna sanya siyasa ne a komai, amma laifi laifi ne, duk wanda ya taka doka to bai fi karfin doka ba," in ji shi.

Za a yi amfani da sojojin sama a 2027

A wani rahoton, kun ji cewa Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) na shirin amfani da jirage da fasahar leƙen asiri domin tallafa wa a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Ana neman karawa ma'aikatan Najeriya karin albashin sama da N150,000

Daga cikin ayyukan da rundunar za ta taimaka da su akwai jigilar kayayyakin zaɓe gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Hafsan Rundunar Sojin Saman Najeriya, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke, ya bayyana hakan yayin wata ziyarar girmamawa da ya kai hukumar INEC.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262