Aiyedatiwa: Babbar Kotu Ta Hana Gwamna Mai Ci Ya Tsaya Takara a Zabe Mai zuwa
- Babbar Kotun Tarayya ta haramta wa Gwamna Lucky Aiyedatiwa tsayawa takara a shekarar 2028 don hana shi zarce shekaru takwas a kan mulki
- Kotun ta dogara ne da sashe na 182 na kundin tsarin mulkin Najeriya wanda ya kayyade wa'adin mulkin shugabanni bayan rantsar da su sau biyu
- Wani jigon APC ne ya shigar da karar inda kotu ta amince cewa rantsar da Aiyedatiwa a 2023 da 2025 sun sanya ba zai iya sake neman takara ba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Ondo - Babbar Kotun Tarayya dake zamanta a Akure, babban birnin jihar Ondo, ta yanke hukuncin cewa Gwamna Lucky Aiyedatiwa ba shi da ikon tsayawa takarar gwamna a zaɓen shekarar 2028.
Kotun ta bayyana cewa ba gwamnan damar sake tsayawa takara zai saba wa tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya, wanda ya kayyade cewa babu shugaban ƙasa ko gwamna da zai kwashe fiye da shekaru takwas a kan mulki.

Kara karanta wannan
Ganin fetur ya tashi a duniya, Tinubu ya bada umarnin gaggawa a kawo wa 'yan Najeriya sa'ida

Source: Twitter
Kotu ta hana Gwamnan Ondo sake takara
Alkalin kotun, Mai shari'a Adegoke, ta yi bayanin cewa Aiyedatiwa ya fara karɓar ragamar mulki ne a ranar 27 ga Disamba, 2023, bayan rasuwar tsohon Gwamna Rotimi Akeredolu, cewar rahoton Tribune.
Bayan haka, an sake rantsar da shi a ranar 24 ga Fabrairu, 2025, bayan ya lashe zaɓen gwamna na watan Nuwamba 2024.
Kotun ta dogara ne da hukuncin Kotun Ƙoli a shari'ar Marwa v. Nyako domin tabbatar da cewa ba za a ƙetare sharaɗin shekaru takwas ba.
Wani mamba na jam’iyyar APC, Dr. Akin Egbuwalo, ne ya shigar da ƙarar ta hannun lauyansa, Chief Adeniyi Akintola (SAN).
Abin da kotu ta ce kan wa'adin mulkin gwamna
Mai ƙara ya buƙaci kotun ta fassara Sashe na 137(3) da Sashe na 182(3) na Kundin Tsarin Mulkin 1999 (kamar yadda aka yi masa gyara), cewar rahoton Premium Times.
Waɗannan sassa sun tanadi cewa duk mutumin da aka rantsar domin ya ƙarasa wa'adin mulkin wani, to yana da damar sake tsayawa takara sau ɗaya ne kawai.

Kara karanta wannan
ICPC: Lauyan El Rufa'i ya yi martani kan 'gano' gidajen tsohon gwamna a kasar Masar
Mai shari'a Adegoke ta jaddada cewa wannan shari'ar ba ta da nasaba da yaudara kamar yaddda za a iya zata, domin kotu tana da hurumin fassara kundin tsarin mulki.
Ta bayyana cewa:
"Idan aka bar wanda ake ƙara na uku (Aiyedatiwa) ya tsaya takara kuma ya yi wasu shekaru huɗun, hakan zai saba wa matsayin doka... inda Kotun Ƙoli ta ce babu shugaba ko gwamna da zai yi aiki sama da shekaru takwas."

Source: Original
Wadanda ake kara tare da Gwamna Aiyedatiwa
Kotun ta yi watsi da dukkan hujjojin kariya daga ɓangaren gwamnan da jam'iyyar APC, tana mai cewa sun gaza gabatar da kwararan dalilai da za su iya yin nasara.
Wannan hukunci ya haifar da cece-kuce a fagen siyasar jihar Ondo, domin yana nufin Aiyedatiwa zai sauka daga mulki ne a ƙarshen wa'adinsa na yanzu ba tare da damar sake takara ba.
Wadanda aka sanya a cikin ƙarar sun haɗa da hukumar INEC, babban lauyan gwamnatin tarayya, jam'iyyar APC, da kuma mataimakin gwamna, Dr. Olayide Adelami.
Aiyedatiwa na tsirin tsige mataimakinsa?
A wani labari, mun ruwaito cewa, Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya musanta rade-radin da ake yadawa cewa ya fara yunkurin tsige mataimakinsa, Olayide Adelami.
Hakan na zuwa ne bayan hasashen da wani malamin coci ya yi cewa ya gano cewa mataimakin gwamnan jihar Ondo zai bar mukaminsa.
Gwamna Aiyedatiwa ya bayyana cewa wannan hasashe karya ce mara tushe, ana yada shi ne domin tayar da hankali da bata amincin tsakaninsu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
