Zance Ya Kare: Kotun Daukaka Kara Ta Raba Gardama kan Rikicin Shugabancin PDP
- Rikicin shugabanci na jam'iyyar PDP ya sanya an shigar da kararraki daban-daban a gaban kotun daukaka kara
- Kotun daukaka kara ta yanke hukunci kan shari'ar da ke kalubalantar soke babban taron jam'iyyar PDP na kasa da aka yi
- Hukuncin da babbar kotun daukakar ta yanke a ranar Litinin, 9 ga watan Maris 2026, ya zo ne a karkashin kwamitin alkalai mai mutum uku
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Kotun daukaka kara da ke Abuja ta yanke hukunci kan karar da ke gabanta kan rikicin jam'iyyar PDP.
Kotun ta yi watsi da ƙarar da jam’iyyar PDP ta shigar na ƙalubalantar hukuncin ranar 31 ga Oktoban 2025.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce kotun daukaka karar ta yanke hukuncin ne a ranar Litinin, 9 ga watan Maris 2026.
Wane hukunci kotun daukaka kara ta yanke?
Kotun ta yi watsi da shari'ar da ke kalubalatar hukuncin da mai shari’a James Omotosho na babbar kotun da ke Abuja ya yanke, wanda ya hana hukumar INEC amincewa da sakamakon babban taron PDP na kasa da aka gudanar a Ibadan, jihar Oyo, ranar 15 da 16 ga Nuwamban 2025.
A cikin wani hukunci na bai-ɗaya a ranar Litinin, kwamitin alkalai mutum uku na kotun ɗaukaka ƙarar ya warware batutuwa huɗu da aka gabatar domin yanke hukunci a kan jam’iyyar PDP, jaridar The Punch ta kawo labarin.
Kotun ta yanke cewa karar da PDP ta shigar ba ta da tushe, kuma babbar kotun tarayya tana da gaskiya wajen yanke hukuncin ranar 31 ga Oktoba da kuma ba da dukkan abubuwan da masu shigar da karar suka nema.
PDP ta kai kara bayan hukuncin babbar kotu
Wata babbar kotun tarayya a Ibadan, jihar Oyo, ta soke babban taron PDP na ƙasa na PDP da aka gudanar a Ibadan ranar 15 ga Nuwamba, 2025.
Sai dai, jam’iyyar ƙarƙashin jagorancin Tanimu Turaki, SAN, ta yi watsi da hukuncin, inda ta bayyana shi a matsayin mara inganci
Waɗanda ake ƙara su tara su ne hukumar INEC, PDP, sakataren PDP na kasa, Samuel Anyanwu, sakataren shirye-shirye na kasa, Umar Bature, kwamitin NWC da NEC na jam’iyyar, Ambasada Umar Iliya Damagum, Ali Odefa da Emmanuel Ogidi.
Kotun daukaka ta amince da soke taron PDP
Yayin da yake yanke hukuncin, Mai Shari’a Onyemenam ya bayyana cewa PDP ta saba wa tanade-tanaden kundin tsarin mulki da ake buƙata kafin irin wannan taron ya zama sahihi.
Daga cikin wasu abubuwan, Mai Shari’a Onyemenam ya ce ba a aika wa hukumar INEC, sahihiyar takardar sanarwar taron ba kamar yadda doka ta tanada.
Kotun ɗaukaka ƙarar ta kuma yanke cewa ba a gudanar da sahihan tarurrukan zaben shugabanni a jihohi fiye da 14 ba kamar yadda doka ta tanada kafin shirya babban taron na 2025.

Source: Instagram
Mai Shari’a Onyemenam ya kuma yanke cewa ƙarar da mambobin PDP suka shigar ba ta shafi harkokin cikin gida na jam’iyyar ba kamar yadda aka yi kuskuren gabatarwa.
Ya ce karar, tana nufin tilasta wa INEC bin ayyukanta na doka dangane da tarurrukkan gangamin jam’iyyu ne.
Bayan gaza bin dokokin da suka dace, Kotun daukaka kara ta yanke cewa babbar kotun tarayya ta yi daidai wajen bayar da umarnin hana INEC karɓa ko amincewa da sakamakon taron na PDP na 2025.
Kotu ta amince da babban taron PDP
A wani labarin kuma, kun ji cewa babbar kotun jihar Oyo ta tabbatar da sahihancin babban taron jam'iyyar PDP da aka gudanar a birnin Ibadan a shekarar 2025.
Alkalin kotun, Fadiran Akintola ya amince da gyaran da aka yi a takardar shigar da kara da Musibau Adetunmbi (SAN) ya gabatar a madadin mai kara, Folahan Malomo Adelabi.
Mai shari’a Akintola ya amince da dukkanin bukatu 13 da aka gabatar, inda ya yanke hukuncin cewa taron ya gudana daidai da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na 1999.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


