An Fara: Tsohon Gwamna Ya Shiga ADC bayan Kai Masa Hari da Kona Ofishinta

An Fara: Tsohon Gwamna Ya Shiga ADC bayan Kai Masa Hari da Kona Ofishinta

  • Tsohon gwamnan Rivers, Rotimi Amaechi, ya tabbatar da shiga jam’iyyar ADC a hukumance yayin da ake tunkarar zaben 2027
  • Rahotanni sun ce wasu da ba a san ko su waye ba sun kona ofishin jam’iyyar ADC a Ubima kafin rajistar tsohon Ministan sufuri
  • Amaechi ya roƙi magoya bayansa su guji tashin hankali, yana cewa babu wanda zai hana su taruwa a yankinsu, ya kuma yabawa jami’an tsaro

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Tsohon gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi ya tabbatar da shigar shi jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya.

Amaechi ya shiga jam’iyyar ADC a hukumance gabanin zaben 2027 da ake shirin gudanarwa a Najeriya wanda ake hasashen zai zama mai zafi

Rotimi Amaechi ya shiga jam'iyyar ADC a hukumance
Tsohon gwamnan Rivers, Roitmi Amaechi ya shiga jam'iyyar ADC. Hoto: Rt. Hon. Rotimi Amaechi.
Source: Facebook

Rotimi Amaechi ya yi rijistar zama dan ADC

Amaechi ya kammala rajistarsa a mazaba ta takwas da ke Ubima a karamar hukumar Ikwerre ta Rivers tare da magoya bayansa, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Ƴan bindiga sun farmaki ministan Buhari, sun kona ofishin jam'iyya

Wannan mataki na zuwa ne sa’o’i kadan bayan wasu da ba a san ko su waye ba sun banka wa ofishin jam’iyyar ADC da ke yankin wuta wanda ya tayar da hankula a yankin.

Rahotanni sun ce mazauna yankin sun tashi da safiyar ranar Juma’a suka tarar da gobara ta lalata wani bangare na ofishin jam’iyyar tare da jefa mutane cikin firgici.

Kafin haka, yan daban sun kai hari kan ayarin motocin Amaechi domin hana shi gudanar da taron siyasa da ya zo yi a yankin.

Yayin da yake magana ga magoya bayansa, Amaechi ya bukace su da su guji duk wani nau’in tashin hankali da zai iya jawo asarar rayuka.

Ya ce:

“Kada ku yi tashin hankali saboda tashin hankali na iya jawo mutuwar wani. Kada ku yi tashin hankali. Amma ba za su hana mu taruwa ba a yankinmu.”
Amaechi ya ba yan jam'iyyar ADC shawara
Tsohon minista a mulkin Muhammadu Buhari, Rotimi Amaechi. Hoto: Rt. Hon. Rotimi Chibuike Amaechi.
Source: Twitter

Amaechi ya yaba wa kwamishinan 'yan sandan Rivers

Amaechi ya kuma yabawa kwamishinan ‘yan sanda da daraktan DSS bisa kwarewar da suka nuna wajen kula da tsaro bayana barkewar rikicin da ya yi sanadin ofishin.

Ya ce bai yi tsammanin hakan daga gare su ba domin yana zaton za su kasance a bayan wadanda suka aikata wannan laifi.

Kara karanta wannan

Za a shiga takarar gwamna, ba a ga sunan jam'iyyun LP da PDP cikin masu fafatawa ba

Ya ce hakan ya nuna adalcinsu duk da cewa suna karkashin gwamnatin jam'iyyar APC da ake zargin tana mulkin zalunci da kama-karya.

Tsohon ministan sufurin ya kuma bukaci jami’an tsaro su gano tare da kama wadanda suka kona ofishin jam’iyyar ADC a Ubima domin su girbi abin da suka shuka tun da wuri, cewar rahoton Vangaurd.

Sanata ya bar PDP, ya shiga jam'iyyar NDC

Kun ji cewa tsohon gwamnan Bayelsa, Seriake Dickson, ya fice daga PDP a Najeria saboda rigingimu da suke damun jam'iyar mai adawa.

Dickson ya ce PDP ta lalace sosai, yana mai cewa “jam’iyyar na ci gaba da jinya ne" saboda rikicin cikin gida da ke damunta wanda ya zama mai wahalar magancewa.

Sabuwar jam’iyyar da ya shiga ta ba shi katin mamba mai lamba 001, alamar cewa yana cikin sahun farko na 'yan jam’iyyar da hukumar INEC ta yi mata rijista kwanan nan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.