An Fara Nuna Yatsa ga Tinubu da 'Yan Bindiga Suka Farmaki Peter Obi, Tsohon Shugaban APC

An Fara Nuna Yatsa ga Tinubu da 'Yan Bindiga Suka Farmaki Peter Obi, Tsohon Shugaban APC

  • Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi, da John Odigie-Oyegun tare da shugabannin ADC sun sha da kyar daga harin ‘yan bindiga
  • Dr Yunusa Tanko ya ce maharan sun bi su daga sakatariyar jam'iyyar ADC zuwa gidan Odigie-Oyegun, inda suka harbe ƙofa tare da lalata motoci
  • Wasu yan Najeriya da 'ya'yan jam'iyyar mai adawa a Najeriya suna zargin gwamnatin Najeriya da neman rufe bakin yan adawa gabanin yin zabe

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Edo - Yan bindiga sun kai hari kan tsohon dan takarar shugaban kasa a 2023, Peter Obi da wasu jigaj-jigan jam'iyyar hamayya ta ADC a jihar Edo.

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi, da tsohon shugaban APC na ƙasa, John Odigie-Oyegun, tare da wasu shugabannin ADC suka gamu da harin.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta tanka bayan 'yan adawa sun yi matsaya kan dokar zabe

Yan ADC sun soki gwamnatin Tinubu game da hari kan Obi
Tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi bayan kai musu hari a Edo. Hoto: ADC News.
Source: Twitter

'Yan bindiga sun kai hari kan tawagar Peter Obi

Tsohon mai magana da yawun kamfen Obi kuma mai kula da Obidient Movement, Dr Yunusa Tanko, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da Punch ta samu.

An yi ta maganganu kan harin inda wasu ke zargin akwai hannun gwamnati mai ci da bunkasar jam'iyyar adawa ke tayar mata da hankali.

Sanarwar ta ce:

“Peter Obi da shugabannin ADC na cikin hatsarin hari a Benin, Edo, a lokacin shigar Olumide Akpata ADC, wasu dauke da makamai sun bi mu.”
Yan bindiga sun farmaki Obi da tsohon shugaban APC
Tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi. Hoto: Mr Peter Obi.
Source: Twitter

Ana zargin ana neman dakile yan adawa

Mutane da dama sun nuna damuwa kan yadda ake kai hare-hare ga jiga-jigan adawa a kasar ta hanyar yan daba ko jami'an tsaro.

Wani shafin jam'iyyar ADC ya fitar da sanarwa game da harin a dandalin Facebook inda take zargin wasu a cikin gwamnatin Bola Tinubu.

A rubutun mai taken 'zargin cin zarafin yan adawa', jam'iyyar ta koka kan yadda magoya bayan Tinubu ke kokarin sauya labarin harin da aka yi.

Kara karanta wannan

Atiku da jagororin adawa a Najeriya sun cimma matsaya kan sabuwar dokar zabe ta 2026

Tanko ya ce sun bi tawagar daga sakatariyar ADC zuwa gidan John Odigie-Oyegun, inda suka harbe ƙofa tare da lalata motoci da dama a harin.

Ya bayyana lamarin a matsayin yunƙurin kashe su da bai yi nasara ba, yana mai cewa dimokuraɗiyya na cikin haɗari a ƙasar.

Hotuna da bidiyo da aka aiko sun nuna gilasan motocin SUV sun farfashe, yayin da ƙofar gidan Odigie-Oyegun ta cika da ramukan harsashi.

An ce harin ya faru ne yayin harkokin siyasa na shigar Olumide Akpata ADC, abin da ya ƙara tada hankali a siyasar Edo, cewar TheCable.

Dan jam'iyyar ADC ya yi magana

Wani masoyin ADC a Gombe ya bayyana takaici kan yadda ake addabar yan adawa gabanin zaben shekarar 2027.

Aliyu Abubakar ya ce ana zargin gwamnatin Bola Tinubu da murkushe yan adawa da kuma cafke manyansu.

Ya ce:

"Ko ma yaya ne, za mu ci gaba da zargin gwamnatin nan duba da yadda suka taso adawa a gaba."

Karin haske kan jita-jitar DSS za su kama Obi

A wani labarin, wasu na ta yada jita-jitar cewa hukumomin tsaro da na yaki da cin hanci na iya farautar tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Peter Obi.

Kara karanta wannan

Yadda Peter Obi da jiga jigan ADC suka tsallake rijiya da baya a harin 'yan bindiga a Edo

Hadimin Peter Obi, ya fito ya yi magana kan jitar-jitar wadda ke cewa hukumomin na iya kirkirar tuhume-tuhume kan tsohon gwamnan na Anambra.

Yunusa Tanko wanda babba ne a kungiyar Obidient ya bayyana cewa a shirye suke da duk wani irin shiri da gwamnati mai mulki za ta yi a kansu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.