Oyegun ya ki goyon bayan Ize-Iyamu, ya bukaci mutanen Edo da su zabi son ransu

Oyegun ya ki goyon bayan Ize-Iyamu, ya bukaci mutanen Edo da su zabi son ransu

- Tsohon Shugaban jam’iyyar APC, John Oyegun ya bayyana matsayarsa kan zaben gwamnan Edo

- Oyegun ya bukaci mutanen jihar Edo da su fito su zabi son ransu

- Jigon na APC dai ya nuna rashin jin dadi a kan abunda aka yi wa Gwamna Godwin Obaseki wanda yayi sanadiyar barinsa jam'iyyar zuwa PDP

Tsohon Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, John Oyegun, ya ki nuna goyon bayansa ga Osagie Ize-Iyamu, dan takarar jam’iyyarsa a zaben gwamnan Edo.

A wani jawabi da ya saki a ranar Litinin, 14 ga watan Satumba, Oyegun ya yi watsi da abunda ya bayyana a matsayin “siyasar rashin wayewa”, inda yayi kira ga mutanen Edo a kan su zabi muradin ransu.

Ya caccaki tursasawar da aka yi wa Godwin Obaseki, gwamnan jihar Edo har sai da ya bar APC, cewa gwamnan ya fuskanci fushi da baya bisa ka’ida a yayinda ya tsayawa mutanensa.

“Ra’ayi da jawabaina kan lamarin siyasar jihar Edo yana nan yadda yake. Na bayar da shawara a kan muzgunawa Gwamna Godwin Nogheghase Obaseki da tsohuwar kwamitin uwar jam’iyyar APC tayi.

"Gwamna Obaseki ya tsaya tsayin daka saboda mutuncin mutanensa kuma a kan haka ne ya fuskanci muzanci,” in ji jawabin.

KU KARANTA KUMA: A cikin shekaru 6: Gwamnatin Katsina ta kashe N4bn wajen magance matsalar tsaro

Oyegun ya ki goyon bayan Ize-Iyamu, ya bukaci mutanen Edo da su zabi son ransu
Oyegun ya ki goyon bayan Ize-Iyamu, ya bukaci mutanen Edo da su zabi son ransu Hoto: PastorIzeIyamu
Asali: Twitter

“Kan lamarin wanda zai jagoranci jihar Edo, mutane na da yanci kuma babu wani mutum ko kungiya, duk kuwa matsayinsu da za su iya zartar da hukunci a madadinsu.

“Ina tare da mutanen jihar Edo kuma ina umurtansu da su fito kwansu da kwarkwatansu domin sauke hakkinsu na damokradiyya. Su zabi gwamnati mai nagarta, adalci, da shugaba mai manufa, musamman a bangaren siyasa da kare yancinsu na damokradiyya.

“Su nuna cewa yancinsu ne zabar shugabansu ba wai na wani ba. Wannan lamari ne na musamman kuma ya zama dole a ajiye dadadden akida na biyayya. Ku tuna gargadin Shugaban kasa a kalubale da aka samu na kafin zabe a jihar Imo, ‘ku zabi son ranku.”

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya yi sabbin nade-nade masu muhimmanci guda 4

A wani labarin, Gwamna Godwin Obaseki ya zargi wanda ya gada, Adams Oshiomhole, da saka jihar ciki matsanancin bashi sakamakon yadda ya dinga ciwo bashi babu tsagaitawa.

Obaseki ya sanar da wannan zargin a ranar Lahadi yayin da ake muhawara da shi na zaben gwamnan jihar Edo da ke gabatowa a gidan talabijin na Channels.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng