"Abin Takaici ne": Kwankwaso Ya Sake Magana a kan Sauya Shekar Abba zuwa APC
- Tsohon dan takarar Shugaban kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya nuna takaicin sauya shekar gwamnatin Kano zuwa APC
- Ya ce Allah ne kaɗai Ya san dalilin da ya sa gwamnati ta janye jikinta daga da tafiyar Kwankwasiyya, sai dai abin bai yi dadi ba
- Ya jaddada cewa ƙofar Kwankwasiyya a buɗe ga dukkanin wadanda suka bi gwamnati a kowane lokaci idan akwai bukatar haka
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, ya sake bayyana takaicin yadda gwamnatin Kano da suka taimaka aka kafa ta ta koma ƙarƙashin APC da Gandujiyya.
Bayaninsa na zuwa ne bayan jam’iyya mai mulki ta karɓi gwamna Abba Kabir Yusuf da mukarrabansa zuwa jam'iyya mai mulki ta APC a hukumance.

Source: Twitter
A wani bidiyo da aka wallafa a shafin Facebook na Premier Radio, Kwankwaso ya ce ba a san dalilin da ya sa aka ɗauke gwamnatin da Kwankwasiyya ta kafa aka mayar da ita Gandujiyya ba.
Kwankwaso ya yi takaicin rasa gwamnatin Kano
A bidiyon, an ji Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yana bayyana cewa Allah SWT ne Ya san dalilan da suka jawo gwamnatin Kano ta rabu da Kwankwasiyya.
Ya bayyana cewa:
"Wannan gwamnati da aka sha wahala aka kafa ta, amma ba tare da wani dalili wanda mu muka sani kwakkwara ba, aka ɗauke ta, aka kai ta daga wannan tsari namu na Kwankwasiyya, suka koma Gandujiyya."
"Wannan abu ne na takaici, abu ne wanda yake mara daɗi, amma Allah Shi Ya bar wa Kansa sani, amma muna addu'a Allah Ya sa abin ya zama mana alheri, amin."

Source: Twitter
Ya yi fatan alheri ga ’yan majalisar jiha da suka ci zaɓen Ungogo da ƙaramar hukumar Birni, tare da bayyana cewa an san jama'a ba su fito zaɓe ba, amma duk da haka yana taya su murna.

Kara karanta wannan
Kurunkus: Gwamna Abba ya bayyana ainihin dalilinsa na komawa APC a gaban Shettima
Kwankwaso ya ƙara da fatan alheri ga dukkanin ’yan Kwankwasiyya, tare da bayyana cewa dukkanin waɗanda suka bi gwamnati za su iya sake waiwayar Kwankwasiyya domin ƙofa a buɗe take.
Alkawarin Rabiu Kwankwaso ga Kanawa
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa a jam’iyyarsa ta NNPP da tafiyar Kwankwasiyya, ba za su yi ƙasa a gwiwa ba wajen taimakon jama'a ta hanyoyin da ake da buƙata.
Ya ce:
"Mu a cikin wannan tafiya tamu ta Kwankwasiyya, da wannan jam’iyyarmu ta NNPP, za mu ci gaba da yin abubuwan da jama'a za su ci gaba da alfahari da mu, musamman kula da harkar ilimi, musamman inganta rayuwar mata da matasa da sauran jama'a waɗanda suke mabukata a wannan jiha da ma Najeriya gaba ɗaya."
Kwankwaso ya kuma gode wa dukkanin ’yan jam’iyyar, musamman waɗanda ke addu'a da aiki ba dare ba rana domin tabbatar da cewa an kai ga nasara.
A kalaman Kwankwaso:
"A nan na ke gode wa dukkanin ’yan Kwankwasiyyarmu, waɗanda suke wajen Najeriya, waɗanda suke aiki ba dare ba rana a ƙasashe daban-daban, waɗanda suke mana addu'o'i, musamman ’yan Kwankwasiyyarmu na Saudiyya."
"Ina sane cewa a kullum suna tafiya Ka’aba domin yi mana addu'o'i da ma manyan masallatai da ke Saudiyya."
Ya yi fatan za su ci gaba da aiki wajen yada manufar Kwankwasiyya, musamman ganin ƙasashe da dama na amfani da akida da kayan da darikar siyasar ke amfani da ita.
Sanata Kwankwaso ya hadu da Nasiru Gawuna
A baya, mun wallafa cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya hadu da tsohon dan takarar Gwamnan Kano a jam'iyyar APC a zaben 2023, Nasiru Yusuf Gawuna.
Hakan na zuwa ne bayan Madugun Kwankwasiyya ya kai ziyara gidan tsohon gwamna Malam Ibrahim Shekarau bayan rashi da aka masa a makon da ya gabata.
An ga Gawuna a cikin wani bidiyon ya na risunawa Kwankwaso duk da ya yi kokarin ba shi hannu su gaisa, sannan ya gabatar da wasu mutane suka gaishe da tsohon gwamnan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

