Barau Jibrin Ya Fito da Alamun Nasarar Tinubu, Abba da Sauran 'Yan APC a 2027
- Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya yi magana game da makomar jam'iyyar APC a zaben 2027 mai zuwa
- Sanata Barau Jibrin ya magantu ne bayan nasarar da jam'iyyar ta samu a zabukan da aka yi a Rivers, Kano da birnin tarayya Abuja
- Ya bayyana cewa hakan alama ce da ke nuna cewa shugaba Bola Ahmad Tinubu, Abba Kabir Yusuf da 'yan APC za su yi nasara
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya yi magana bayan zaɓen ƙananan hukumomi a Abuja, da kuma zaɓen cike gurbi a Kano da Rivers.
An yi zaben cike gurbi ne a mazaɓun Ahoada ta Gabas II da Khana II a Jihar Rivers, tare da mazaɓun karamar hukumar Birni da Ungogo a Jihar Kano a ranar Asabar da ta wuce.

Kara karanta wannan
Dan Agundi: Adadin mutanen da za su mutu a zaben cike gurbi da Abba bai koma APC ba

Source: Facebook
A wani sako da ya wallafa a X, Barau Jibrin ya bayyana cewa sakamakon zaben babbar nasara ce kuma alama ce ta abin da ke tafe a babban zaɓen 2027.
Kujerun da jam'iyyar APC ta lashe a zabuka
Jam’iyyar APC ta lashe kujeru biyar daga cikin shida na shugabannin ƙananan hukumomi da aka fafata a zaɓen ƙananan hukumomin Abuja, yayin da PDP ta samu kujera ɗaya.
A Kano, INEC ta ayyana ’yan takarar jam’iyyar APC, Aliyu Nabil Daneji da Aminu Sa’ad Sa’ad, a matsayin waɗanda suka yi nasara a zaɓen cike gurbi.

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa ’yan takarar jam’iyyar APC, Ukalikpe Napoleon da Loolo Bulabari Henrietta, sun lashe kujerun mazaɓun jiha guda biyu a Rivers.
Barau Jibrin ya gode wa 'yan APC
Saboda nasara a zaben, Barau ya ce yana godiya ga masu zaɓe a Abuja bisa tsayawa tare da jam’iyyar su kamar yadda suka saba, tare da taya waɗanda suka yi nasara murna.
Ya ce:
"Ina taya mai girma shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu; shugaban jam’iyyarmu ta APC na kasa, Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda; Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.
"Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara; da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, murnar waɗannan nasarori."
Alamun nasarar jam'iyyar APC a 2027
Barau Jibrin ya bayyana cewa nasarar da suka samu a zabukan alama ce da ke nuna yadda sakamakon zabe zai kasance a 2027.
Ya ce:
"Insha Allah, wannan alama ce ta nasara yayin da ake shirin fuskantar babban zaɓen 2027.
"Jam’iyyarmu da dukkan ’yan takararmu, mai girma shugaba Bola Ahmed Tinubu, gwamna Abba Kabir Yusuf da mu duka za mu yi nasara."
Rabiu Kwankwaso ya hadu da jigon APC
A wani labarin, kun ji cewa Rabiu Musa Kwanwaso ya hadu da daya daga cikin manyan jam'iyyar APC a jihar Kano, Nasiru Yusuf Gawuna.
Rahotanni sun nuna cewa shugabannin sun hadu ne a filin jirgin saman Malam Aminu Kano yayin da suke shirin tafiya da sanyin safiya.
Kafin haduwarsu, Sanata Rabiu Kwankwaso ya sanar da cewa ya ziyarci tsohon gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
