Kano: Sauya Shekar Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Jawo Tarnaki a Jam'iyyar APC

Kano: Sauya Shekar Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Jawo Tarnaki a Jam'iyyar APC

  • Shigowar Gwamna Abba Kabir Yusuf APC ya haifar da ce-ce-ku-ce a Kano, musamman a batun rabon mukaman jam'iyya
  • Tsarin rabon mukamai na 60/40 ya jawo rashin jituwa a tsakanin ‘yan jam’iyya, inda aka a ce su gwamna Abba za su samu 60%
  • Rahotanni sun bayyana jiga-jigan APC da aka iske sun fara nuna damuwa kan makomar hadin kan jam’iyyar a jihar Kano

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Rahotanni sun bayyana cewa lokacin da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sauya sheka zuwa APC, an murna da hakan

Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, tare da shugabannin APC sun bayyana bayyana jin dadi da murnar sauya shekar.

Sauya shekar Gwamna Abba Kabir Yusuf na shirin raba kan 'yan APC
Abdullahi Abbas, Gwamna Abba Kabir Yusuf, tsohon Shugaban APC Abdullahi Umar Ganduje da AA zaura a wani taro Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa sai dai duk da shagalin bikin, akwai alamun rashin kwanciyar hankali a karkashin kasa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fusata kan kashe kashe a taron APC, ya dauki kwakkwaran mataki

Ana shirin samun matsala a jam'iyyar APC

Daily Post ta wallafa cewa bayan sauya shekar Gwamna, wasu yan Kwankwasiyya da 'yan APC sun koma zama a karkashin inuwar siyasa daya.

Shugaban APC na kasa, Nentawe Yilwatda ya tabbatar da cewa za a yi rabon mukamai a tsarin 60/40 da ya bai wa Gwamna Abba Kabir Yusuf rinjaye.

Duk da cewa shugabannin kasa na kokarin nuna hakan a matsayin hadin kai, a matakin jiha ana ganin akwai shakku.

Masana sun ce har yanzu bangarorin biyu na yi wa juna kallon-kallo, kuma har yanzu ba su zama tsintsiya madaurinki daya ba.

Yadda Kano za ta raba mukaman APC

A cikin tsarin rabon da APC ta tabbatar da cewa tsargin Gwamna Abba Kabir Yusuf zai kawo mutane 60% a kan mukaman.

Tsofaffin 'yan APC, daga ciki har da tsohon shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, za su samu ragowar kashi 40%.

Kara karanta wannan

ADC, kungiyoyi sun nuna damuwa kan gaggawar Tinubu na amincewa da dokar zabe

A cewar Yilwatda, an yi hakan ne domin sababbin 'yan jam'iyya su ji ana damawa da su, yana mai cewa gwamnonin da suka sauya sheka kan fi samun rinjaye.

Bangaren Gwamna Abba Kabir Yusuf na ganin tsarin ya yi dai-dai, amma tsofaffin 'yan jam'iyya na ganin hakan bai dace ba.

Hakan ya haddasa sabani, musamman rikicin da ya barke tsakanin Sanatan Kano ta Kudu, Abdulrahman Kawu Sumaila, da dan majalisar tarayya mai wakiltar Doguwa/Tudun Wada, Alhassan Ado Doguwa.

A wani bidiyo, Doguwa ya yi watsi da tsarin rabon 60/40 karbar Abba a mazabarsa, yana zargin ana kokarin danne su ta hanyar kakaba masu Sa'adatu Salisu Soja a T/Wada..

Shi kuwa Kawu ya mayar da martani da kalamai masu zafi, lamarin da ya girgiza magoya bayan jam’iyyar.

Haka zalika, a wasu kananan hukumomi kamar birnin Kano, an ga bangarorin biyu na gudanar da taruka daban-daban, abin da ke nuna rarrabuwar kai.

'Dan APC ya ja kunne shugabannin jam'iyya

A baya, kun ji labarin cewa wani babba a jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya, Alhaji Sani Shinkafi, ya yi tsokaci kan zaben shekarar 2027 da ke kara tunkaro wa.

Kara karanta wannan

Jihohin da suka rage lokacin tashi daga ofis alfarmar watan Ramadan a Najeriya

Alhaji San​i Abdullahi Shinkafi ya bayyana cewa idan har talakawa ba su gamsu da salon mulki ba, zai yi wuya kowace jam’iyya ta yi nasara a babban zabe mai zuwa.

Jagoran na APC ya bayyana cewa zaben 2027 zai kasance ne tsakanin talakawa da jam'iyyun siyasar da ake da su, kuma za a gani a a wurin kada kuri'a.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng