Duniya Labari: Sanata a Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya, Ana Ta Rasa 'Yan Majalisa
- Majalisar dattawan Najeriya ta sake shiga jimami bayan rasa daya daga cikin mambobinta da ya yi bankwana da duniya
- Majiyoyi sun tabbatar da cewa Sanatan Rivers ta Kudu maso Gabas ya rasu yana da shekaru 64 a duniya bayan ya yi jinya
- An sanar da rasuwarsa a zaman kwamitin majalisar dattawa a yau Alhamis 19 ga watan Fabrairun shekarar 2026 da muke ciki
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Port Harcourt, Rivers - Majalisar dattawan Najeriya ta sake yin rashi bayan sanar da rasuwar daya daga cikin mambobinta.
An tabbatar da cewa sanatan da ke wakiltar mazabar Rivers ta Kudu maso Gabas a Majalisar Dattawa, Barinada Mpigi, ya rasu.

Source: Twitter
An sanar da rasuwar sanata a Najeriya
Rahotanni sun ce Mpigi, wanda shi ne shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Ayyuka, ya mutu yana da shekaru 64 bayan ya sha fama da rashin lafiya na wani lokaci, cewar Punch.
A watannin baya-bayan nan, mataimakin shugaban kwamitin ayyuka, Rufai Hanga, ne ya rika jagorantar wasu tarukan kwamitin ciki har da zaman kare kasafin kudi.
An sanar da rasuwar tasa ne a ranar Alhamis 19 ga watan Fabrairun 2026 yayin zaman kare kasafin kudin Kwamitin Majalisar Dattawa kan Al’adu, Fasaha da Tattalin Arzikin Kirkire-kirkire.
Shugaban kwamitin, Ogwoshi Onawo, ne ya bayyana labarin rasuwar a gaban ‘yan kwamitin inda suka nuna damuwa kan rashin da aka yi.
Bayan sanarwar, mambobin kwamitin sun yi shiru har na tsawon minti guda domin karrama marigayin da ya bar duniya yayin da ake matukar bukatarsa.

Source: Original
Tasirin da marigayin ke da shi a Rivers
An san Mpigi a matsayin daya daga cikin manyan ‘yan siyasa masu tasiri a jihar Rivers, musamman saboda kusancinsa da jama’a da kuma gina karfin siyasa daga tushe.
Kafin rasuwarsa, yana daga cikin sanatocin Rivers da suka sauya sheka daga jam’iyyar adawa ta PDP zuwa jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya.
Kwanaki an ji yadda aka yi ta rade-radin cewa yana cikin sanatocin da za su iya neman gwamna.
'Dan majalisa ya yi jimamin rashin Sanatan
'Dan majalisar tarayya daga jihar Oyo, Oloye Akin Alabi ya tabbatar da labarin rasuwar sanata a wani rubutu da ya yi a shafin X.
Alabi, a cikin wani sako da ya rubuta a kafar sada zumunta, ya yi alhinin rasuwar sanatan Rivers tare da tuna cewa “shi ne Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Ayyuka.”
Wasu ‘yan Najeriya sun yi tururuwa zuwa sashen sharhi na sakon dan majalisar wakilan domin nuna alhininsu tare da yi wa marigayin addu’a.
Sanatan Najeriya ya rasu a Birtaniya bayan jinya
A wani labarin, Najeriya ta yi babban rashi bayan da aka sanar da mutuwar sanata mai ci wanda ya bar duniya bayan fama da jinya a kasar Birtaniya.
Sanata Okey Ezea daga Enugu ta Arewa ya rasu a Birtaniya lamarin da ya girgiza jam’iyyar LP da mutanen yankinsa duba da gudunmawar da yake ba su.
Ezea shi ne ɗan majalisa guda kaɗai da ya ragewa LP daga Enugu, abin da ya sa rashin nasa ya fi ɗaga hankalin jama’a da yan mazabarsa baki daya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

