Shettima Ya Fadi Muhimmancin Kano ga APC bayan Karbar Gwamna Abba zuwa Jam'iyyar

Shettima Ya Fadi Muhimmancin Kano ga APC bayan Karbar Gwamna Abba zuwa Jam'iyyar

  • Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya jagoranci karbar Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano zuwa APC a hukumance
  • Sanata Kashim Shettima ya bayyana cewa jihar Kano na da matukar muhimmanci ga jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya
  • Mataimakin shugaban kasar ya yabawa Gwamna Abba kan shawarar da ya yanke ta sauya sheka daga NNPP zuwa APC mai rike da mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya bayyana jihar Kano a matsayin mai muhimmanci ga jam'iyyar APC.

Sanata Kashim Shettima ya bayyana cewa jihar ba za ta iya ci gaba da zama a gefe ba a harkokin siyasar kasa.

Kashim Shettima ya karbi Gwamna Abba zuwa jam'iyyar APC
Kashim Shettima tare da Gwamna Abba Kabir Yusuf a wajen bikin karbarsa zuwa APC Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta ce Kashim Shettima ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wurin taron karɓar Gwamna Abba Kabir Yusuf a hukumance zuwa APC ranar Litinin, 16 ga watan Fabrairun 2026.

Kara karanta wannan

Shettima ya fadi sakon Tinubu da manyan jiga jigai suka tarbi Gwamna Abba zuwa APC a Kano

Shettima ya jaddada cewa jihar "ba za ta zauna a gefe ba" a cikin lissafin siyasar kasa, jaridar Daily Trust ta kawo rahoton.

Jiga-jigan APC sun halarci bikin karbar Abba

Taron, wanda aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar Mata a Kano, ya hada da sauya shekar mambobin majalisar dokokin jiha 22, ’yan majalisar tarayya takwas da shugabannin kananan hukumomi 44 zuwa jam’iyyar APC.

Manyan baki da suka halarci taron sun haɗa da shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, tsohon shugaban jam'iyyar na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

Gwamnonin jihohin Sokoto, Kebbi, Katsina, Kaduna, Jigawa, da Imo, mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, da sauran manyan jiga-jigai.

Me Shettima ya ce kan Kano?

Yayin da yake jawabi ga magoya baya, Shettima ya bayyana Kano a matsayin "jihar da ke kan gaba" wadda haɗewarta da jam'iyya mai mulki yake da muhimmanci ga nasarar zaɓe a matakin jiha da na ƙasa.

Jam'iyyar APC ta rasa jihar Kano a zaɓen shugaban ƙasa da na gwamna a hannun NNPP a shekarar 2023.

Kara karanta wannan

Kano: Manyan mutane da suka ziyarci kasuwar Singer bayan mummunar gobara

Shettima ya jinjina wa Gwamna Abba Kabir Yusuf kan barin jam'iyyar NNPP, yana mai cewa matakin nasa na shiga APC zai ƙarfafa haɗin kai da ci gaba a jihar Kano.

“Kano tana da matuƙar muhimmanci ta yadda ba za mu bari ta ci gaba da zama a gefe ba."

- Kashim Shettima

Ya taya gwamnan murna, tare da ’yan majalisar jiha 22, mambobin majalisar tarayya, da shugabannin ƙananan hukumomi 44 da suka biyo bayansa zuwa APC.

Gwamna Abba ya yi jawabi

Tun farko a nasa jawabin, Gwamna Abba ya ce shawararsa ta komawa APC ta samo asali ne daga sadaukarwar da ya yi wa ci gaban jihar Kano.

Gwamna Abba ya yi jawabi wajen karbarsa zuwa APC
Gwamna Abba Kabir Yusuf a wajen bikin karbarsa zuwa jam'iyyar APC Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook
“Mutanenmu ba su da sha’awar rigingimun siyasa marasa karshe. A maimakon haka, suna sha’awar kyawawan hanyoyi, asibitoci, makarantu, da sauran ayyukan da za su inganta yanayin rayuwarsu."

- Gwamna Abba Kabir Yusuf

Ya nuna godiyarsa ga Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da shugabannin jam'iyyar da suka halarci taron.

Gwamnatin Tinubu ta tallafa wa 'yan kasuwar Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta ba da tallafi ga 'yan kasuwar da gobara ta shafa a Kano.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Tinubu ya kama hanyar zuwa Adamawa, Shettima ya tafi jihar Kano

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa gwamnati ta ba da tallafin N5bn ga 'yan kasuwar da gobara ta ritsa da su a kasuwar Singer.

Ya yi wa waɗanda abin ya shafa addu’a tare da roƙon Allah da ya kiyaye aukuwar irin wannan masifa a nan gaba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng