Manyan Jam'iyyar APC da aka Gani Wajen Tarbar Gwamna Abba daga NNPP a Kano

Manyan Jam'iyyar APC da aka Gani Wajen Tarbar Gwamna Abba daga NNPP a Kano

Manyan shugabannin jam’iyyar APC ne suka hallara a Kano a ranar Litinin, 15 ga watan Fabrairu, 2026 inda suka karɓi gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf zuwa jam'iyya mai mulki.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Jam'iyyar APC ta yi maraba da Abba Kabir Yusuf a hukumance cikin jam’iyyar a wani babban gangami da aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano a ranar Litinin.

Manyan APC da suka zo tarbar Abba
Manyan APC da aka Gani Wajen Tarbar Gwamna Abba daga NNPP a Kano
Source: Facebook

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya shiga APC

Daily Trust ta wallafa cewa taron ya jawo dimbin magoya bayan jam’iyya da masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa daga sassa daban-daban na ƙasar nan.

Daga cikin wadanda suka halarci taron, akwai gwamnoni da sauran jiga-jigan APC da suka bayyana jin dadin sauya shekar gwamnan.

Kara karanta wannan

Kano: Sauya shekar Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jawo tarnaki a jam'iyyar APC

Legit ta tattaro sunayen wasu daga cikin manyan APC da suka halarci taron yi wa Gwamna Abba Kabir Yusuf lale zuwa jam'iyyar, sun hada da:

Kusoshin da aka gani wajen karbar Abba a APC

A taron an ga tsofaffin sanatoci irinsu Kabir Gaya, Omo Agege, akwai gwamnoni 4, an ga ministan kasafin kudi, Atiku Abubakar Bagudu.

Haka kuma taron ya samu halartar shugabann am'iyya na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda da tsohon Shugaban jam'iyya, Abdullahi Umar Ganduje.

Kusoshin da aka gani a wajen taron sun haɗa da:

1. Mataimakin Shugaban kasa, Kashim Shettima

2. Mataimakin Shugaban majalisar dattawa, Barau I Jibril

3. Shugaban APC, Farfesa Nentawe Yilwatda

4.Shugaban majalisar Wakilai, Rt. Hon. Tajudden Abbas

5. Gwamna Hope Uzodinma

6. Gwamna Nasir Idris

7. Gwamna Umar Namadi

8. Gwamna Uba Sani

9.Gwamna Ahmad Aliyu

10. Mataimakin Gwamnan Katsina, Farouk Jobe

11. Tsohon Shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje

12. Atiku Bagudu Abubakar

13. Tsohon dan takarar gwamnan Kano, Nasiru Gawuna

14. Tsohon dan takarar mataimakin gwamnan Kano, Murtala Garo

15. Tsohon dan takarar gwamnan Kano, A. A Zaura

Kara karanta wannan

Tinubu ya fusata kan kashe kashe a taron APC, ya dauki kwakkwaran mataki

16. Sanata Kabiru Gaya

17. Sanata Kawu Sumaila

18. Tsohon Shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo-Agege

19. 'Dan majalisar tarayya, Abba Bichi

20. Shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas

21. Baffa Babba Dan Agundi

22. Tsohon Gwamna Badaru Abubakar

Abin da Abba ya ce a taron APC

A yayin taron, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa sauya shekar zai taimaka wajen tabbatar da ci gaban Kano.

Ya bayyana cewa sauya shekarsa zai yi amfani, kuma a yanzu haka Kano ta shiga sahun masu fada a ji a gwamnatin tarayyar Najeriya.

Dangane da raba hanya da NNPP, Abba ya danganta ficewarsa daga jam'iyyar da rikice-rikicen cikin gida da kuma yawaitar shari’o’i.

Ya jaddada cewa da suka koma APC, Kano za ta ci gaba da samun tagomashi da ci gaba mai dorewa da za a samo daga gwamnatin tarayya.

An so samun hatsaniya a taron APC

Buhari Mamman, ɗaya daga cikin mahalarta taron ya shaida wa Legit cewa da kyar aka samu fita bayan taro ya watse.

Kara karanta wannan

ADC, kungiyoyi sun nuna damuwa kan gaggawar Tinubu na amincewa da dokar zabe

A kalamansa:

"Da muka ga an kusa gama taro, mun san lallai za mu sha wahala a wajen fitowa. Yan saba sun zo taron sosai, akwai wani ba takalmi ya iso har wajen shagon Jifatu."

Ya kara da cewa akwai jami'an tsaro, kuma kowa ya yi ta kansa kusan nan take bayan kammala taron.

Kashim ya fadi muhimmancin Kano ga APC

A wani labarin, kun ji cewa Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana jihar a matsayin muhimmin ginshiƙi ga nasarar jam’iyyar a matakin ƙasa da jiha.

Ya bayyana haka ne a ranar Litinin, 16 ga watan Fabrairu 2026 a lokacin da ya hadu da sauran shugabannin APC wajen karbar Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa jam'iyyar.

A wajen taron, ya yabawa gwamna Abba da sauran shugabannin siyasa da suka yi wa APC biyayya, ciki har da ‘yan majalisun jiha 22, ‘yan majalisar tarayya takwas.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng