"Ƙila don Ya Ƙi APC ne": El Rufa'i Ya Yi Tir da kai Sunan Kwankwaso Majalisar Amurka
- Tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya ce bai dace a ware Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso kaɗai ba kan batun ƙaddamar da shari’ar Musulunci
- Yana wannan batu ne a lokacin da wasu 'yan Majalisar Dokokin Amurka ke ƙoƙarin kakaba wa Kwankwaso takunkumi a kan zargin take hakkin kiristoci
- Tsohon Gwamnan Kaduna ya tunatar da cewa jihohin Arewa 12 ne suka aiwatar da Shari’a Musulunci, tare da bayyana cewa akwai lauje cikin nadi
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna – Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi tsokaci kan cece-kuce da ke tattare da rahotannin wani kudiri da wasu ‘yan Majalisar Dokokin Amurka suka gabatar.
'Yan majalisar sun gabatar da kuduri da ya ambaci sunan tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, cikin jerin mutanen da za a iya kakaba wa takunkumin kan zargin take ‘yancin addini.

Source: Twitter
Jaridar Punch ta wallafa cewa El-Rufa'i ya bayyana cewa ba daidai ba ne a ware Kwankwaso shi kaɗai, alhali jihohi da dama a Arewa sun aiwatar da tsarin Shari’a a lokuta daban-daban.
Nasir El-Rufa'i ya kare Rabiu Kwankwaso
Ita kuwa jaridar Vanguard ta wallafa cewa El-Rufa'i ya ce Jihohin Arewa da dama sun kaddamar da tsarin shari'ar Musulunci a yankunan su.
Ya ce:
"Jihohin 12 na Arewa ne suka aiwatar da Shari’a. Jiha ta farko da ta fara ita ce Zamfara. Ina ganin kamata ya yi a fara ambaton Zamfara idan har za a dora wa wani laifi kan wannan lamari.”
Ya kara da cewa aiwatar da Shari’a ya fara ne a jihar Zamfara kafin daga bisani sauran jihohi, ciki har da Kano, su bi sahu.
El-Rufai ya ce Kwankwaso bai yi wani abu na daban ba a yadda Kano ta aiwatar da Shari’a idan aka kwatanta da sauran jihohin Arewa.
Ya ce:
“Kwankwaso ya bi sawun sauran gwamnoni. Kano ba ta aiwatar da Shari’a ta wata hanya ta daban ba. Ba ma ta kasance mai tsauri sosai ba."
El-Rufa'i ya ƙaryata zargin ƴan majalisar Amurka
Nasir El-Rufa'i ya musanta zargin da ke nuna Kwankwaso a matsayin mai tsattsauran ra’ayi a batun Shari’a.

Source: Twitter
A cewarsa
"Ba ya cikin mutanen da za ka kira masu tsattsauran ra’ayi a wannan batu.”
Tsohon gwamnan ya kuma tambayi dalilin da ya sa ba a ambaci wasu tsofaffin gwamnoni da suka aiwatar da Shari’a ba, daga ciki har da Abdulaziz Yari.
Ya ce:
"Babu wanda yake ambaton mutane kamar Abdulaziz Yari da sauran gwamnoni da suka kare da kuma inganta Shari’a, amma ana mai da hankali kan Kwankwaso. Wannan yana jefa ayar tambaya a kan batun."
Yari ya zama gwamna ne a 2011, shekaru fiye da 10 bayan Ahmad Sani Yariman Bakura ya kaddamar da shari'ar Musulunci a jihar Zamfara.
Kwankwaso da zargin 'yan majalisar Amurka
El-Rufai ya danganta batun da siyasa, musamman dangane da kin amincewar Kwankwaso ya shiga jam’iyyar APC mai rike da shugabanci.
A cewarsa, akwai yiwuwar wasu dalilai na siyasa ne ke janyo hankalin da ake mayar wa Kwankwaso, saboda ya yi watsi da shiga jam'iyya mai mulki.
A maganganun da ya yi, an ji ya tabo zancen wasu makudan dalolin kudi da ake zargin an kashe domin a wanke gwamnatin Najeriya a idon Amurka.
Tsohon ministan na Abuja ya bukaci ‘yan Najeriya da su rika nazarin labarai da idon basira, su guji daukar kowanne zargi ba tare da tantancewa ba.
Ina tsorata ƴan adawa - El-Rufa'i
A baya kun ji cewa tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa masu mulki a yanzu ba sa jin daɗin dawowarsa gida Najeriya daga Cairo.
El-Rufai ya ce dawowarsa ta firgita gwamnati, yana jaddada cewa an shiga sabon mataki na gwagwarmayar siyasa domin sauya Bola Ahmed Tinubu
'Dan adawar ya yi wannan bayani ne bayan wani yunƙuri da aka ce an yi na kama shi a filin jirgin saman Abuja a lokacin da ya dawo Najeriya a makon da ke ƙarewa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


