Jigon APC Ya Tono Abin da Aka Rufe, Ya Fadi Abin da Tinubu ke Tsoro game da Zaben 2027

Jigon APC Ya Tono Abin da Aka Rufe, Ya Fadi Abin da Tinubu ke Tsoro game da Zaben 2027

  • Wani jigo a jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, Cif Eze Chukwuemeka Eze ya yi ikirarin cewa Shugaba Bola Tinubu na fargabar zaben 2027
  • Eze ya yi zargin cewa Tinubu ya yi kokarin hada kai da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio domin shirya magudin zabe
  • Ya kuma jinjina wa manyan jagororin adawa, Atiku, Peter Obi da Amaechi bisa yadda suka tsaya tsayin daga kan dokar tura sakamako ta intanet

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Wani jigo a jam’iyyar APC, Cif Eze Chukwuemeka Eze, ya yi zargin cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na cikin fargaba game da zaɓen 2027

Eze ya yi ikirarin cewa da alamun Shugaba Tinubu na fargabar a gudanar sahihin zabe a 2027 duk da cewa yana da mafi yawan gwamnoni a ɓangarensa.

Kara karanta wannan

"Sai mun tashi tsaye," Abin da El Rufai ya fadawa Atiku game da Tinubu a Abuja

Shugaba Bola Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yayin wata ganawa a fadarsa da ke Abuja Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Jigon APC ya yabi Atiku da Peter Obi

A rahoton Leadership, Eze ya yaba wa jagororin jam’iyyar ADC, ciki har da tsohon Ministan Sufuri, Rt. Hon. Chibuike Rotimi Amaechi bisa yadda suka tashi tsaye kan batun gyaran dokar zabe.

Sauran wadanda dan siyasar ya jinjinawa a ADC sune tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar; da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Mista Peter Obi.

Mista Eze ya yabawa jagororin hadakar ne kan abin da ya kira ƙin amincewa da shirin da ake zargin Tinubu da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ke yi na kawo cikas ga zaɓen 2027.

Abin da Bola Tinubu ke fargaba a 2027

A cikin wata sanarwa da ya fitar a Fatakwal, Eze ya ƙalubalanci Shugaba Tinubu da ya goyi bayan tura sakamakon zaɓe ta na’ura idan har yana ganin kansa a matsayin ɗan dimokuraɗiyya kuma mai farin jini da zai iya cin zaɓe ba tare da maguɗi ba.

Kara karanta wannan

Bayan ziyartar El Rufai, Atiku ya tona shirin da APC ke yi kan jam'iyyar ADC

Ya ce:

“Shugaba Bola Tinubu na cikin fargaba kuma a ruɗe yake, hakan ya sa ya fara kokarin kauce wa ƙa’idojin duniya da suka dace wajen gudanar da zaɓe mai gaskiya da adalci a 2027.”

Eze ya ƙara da cewa tilasta wa wasu gwamnoni da ‘yan siyasa su shiga APC ba zai tabbatar wa Tinubu nasarar wa’adi na biyu ba, cewar rahoton Daily Post

“A ce Tinubu na cikin fargaba ma bai isa ba, gaskiyar ita ce ya riga ya hango shan kaye a 2027, shi ya sa yake ƙoƙarin kawo cikas ga gudanar da zaɓe na gaskiya,” in ji shi.
Tutar APC.
Tutar jam'iyyar APC mai alamar tsintsiya a Najeriya Hoto: @OfficialAPCNig
Source: Getty Images

Ya tunatar da shugaban kasa da majalisar dattawa ƙarƙashin jagorancin Akpabio cewa zaɓen 2027 yana da matukar muhimmanci, don haka ya kamata su guji duk wani yunkuri na maguɗin zaɓe.

APC ta cika baki kan tazarcen Tinubu a 2027

A wani rahoton, kun ji cewa Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya kara bayyana gwarin gwiwa kan tazarcen Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

'Abin da ya sa dole Arewa ta zabi Tinubu a 2027'; Shugaban APC

Nentawe ya jinjina wa Shugaba Tinubu kan abin da ya kira ƙoƙarin kai Najeriya zuwa matsayi mai girma tun bayan karbar mulki a shekarar 2023.

Ya kuma bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta fi fifita yankin Arewa fiye da kowane yanki na kasar nan ta fuskar ayyukan ci gaba da ƙarfafa gwiwar al’umma.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262