Ta Faru Ta Kare: INEC Ta Sanar da Ranar Zaben Shugaban Kasa da na Gwamnoni a 2027

Ta Faru Ta Kare: INEC Ta Sanar da Ranar Zaben Shugaban Kasa da na Gwamnoni a 2027

  • Hukumar INEC ta bayyana cewa ta shirya tsaf domin gudanar da zaben shekarar 2027 kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya dora mata
  • INEC ta fitar da jadawalin babban zabe mai zuwa, wanda ya kunshe ranakun zaben shugaban kasa, gwamnoni da 'yan majalisa
  • Shugaban INEC na kasa, Farfesa Joash Amupitan ya ce matakin da INEC ta ɗauka ya yi daidai da sashe na 28(1) na Dokar Zaɓe ta 2022

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta fitar da jadawalin babban zaɓen 2027 a Najeriya.

Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ranar Juma’a, 13 ga watan Fabrairu, 2026.

Shugaban INEC.
Shugaban hukumar INEC na kasa, Farfesa Joash Amupitan yayin ganawa da kwamishinonin zabe Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Ranar zaben shugaban kasa da gwamnoni

Daily Trust ta rahoto cewa INEC ta shirya gudanar da zaɓen Shugaban Ƙasa da na 'yan Majalisar Tarayya a ranar 20 ga Fabrairu, 2027.

Kara karanta wannan

Ana neman sauke Amupitan, INEC ta gabatar da kasafin kudin N873bn don zaben 2027

Sai kuma zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisun dokokin jihohi, wanda INEC ta ce zai gudana ranar 6 ga Maris, 2027.

Hukumar INEC ta shirya tsaf

Farfesa Amupitan ya tabbatar da cewa hukumar INEC ta kammala shirye-shiryenta domin gudanar da zaɓen cikin nasara.

Ya ce:

“Bisa tanadin Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na 1999 (wanda aka yi wa gyara), wa’adin shugaban kasa, mataimakin shugaban jasa, gwamnoni da mataimakansu zai ƙare ranar 28 ga Mayu, 2027.”

Ya ƙara da cewa wa’adin ‘yan Majalisar Tarayya da na jihohi zai ƙare ranar 8 ga Yuni, 2027.

A cewarsa, sashe na 76(2), 116(2), 132(2) da 178(2) na Kundin Tsarin Mulki sun tanadi cewa dole ne a gudanar da zaɓe ba kafin kwanaki 150 ba kuma ba bayan kwanaki 30 ba, kafin karewar wa’adin masu riƙe da mukaman.

Ya ce matakin da INEC ta ɗauka ya yi daidai da sashe na 28(1) na Dokar Zaɓe ta 2022, wanda ya wajabta wa hukumar ta sanar da ranar zaɓe aƙalla kwanaki 360 kafin ranar zaɓen.

Shugaban INEC.
Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan yayin ganawa da jami'ai a Abuja Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

INEC kaɗai ke da ikon sanya ranar zaɓe

Kara karanta wannan

IFAD: Ministan Tinubu ya samu gagarumar nasara, an ba shi babban mukami a duniya

Shugaban hukumar ya sake jaddada ‘yancin kai na INEC, yana mai cewa ita kadai ke da ikon ayyana ranar zaɓe a Najeriya, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Ya ce zaɓen 2027 zai gudana a duk faɗin ƙasa domin zaɓar shugaban kasa da mataimakinsa, gwamnoni da mataimakansu (ban da jihohin da ke da jadawali na musamman), sanatoci, ‘yan Majalisar Wakilai da ‘Yan Majalisun Dokokin Jihohi.

Ya kuma ce cikakken jadawalin ayyukan zaɓen an ɗora shi a shafin yanar gizon INEC tare da aika wa dukkan jam’iyyun siyasa da masu ruwa da tsaki.

INEC ta mika kasafin kudin zaben 2027

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta gabatar da adadin kudin da ta shirya kashewa don gudanar da zaben shekarar 2027.

Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya gabatar da kasafin a gaban kwamitin hadin gwiwa na majalisar dattawa da na wakilai ranar Alhamis.

Farfesa Amupitan ya gabatar da kasafin kudi da ya kai Naira biliyan 873.78 tare da jero yadda za a yi amfani da kudin don tabbatar da zabe mai zuwa ya gudana cikin nasara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262