'Tinubu Ya Fara Yi wa Godiya, ba Allah ba': Naja'atu Mohammed Ta Dura kan Abba Kabir
- Hajiya Naja’atu Mohammed ta soki rikicin siyasar Kano, tana sukar 'butulce' wa Rabi'u Kwankwaso da Abba Kabir ya yi
- Ta ce abin mamaki ne yadda Abba ya yi hakuri tsawon shekaru yana tare da Kwankwaso har ya samu mukamai daban-daban
- Naja’atu ta kuma ce Abba ya manta da Allah bayan nasarar kotu, inda ta soki yadda ya fara godewa Bola Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Fitacciyar yar siyasa a jihar Kano, Hajiya Naja'atu Mohammed ta yi magana game da siyasar Najeriya baki daya.
'Yar siyasa ta kuma tabo batun rikicin siyasar Kano musamman tsakanin Abba Kabir da tsohon mai gidansa, Rabiu Musa Kwankwaso.

Source: Facebook
Naja'atu ta soki Abba kan 'butulce wa' Kwankwaso
Hajiya Naja'atu ta bayyana haka a wani bidiyo yayin hira da mawaki a Arewacin Najeriya, Ali Jita wanda ya wallafa a YouTube.
Naja'atu ta nuna damuwa game da halayen Abba Kabir inda ta ke kalubalantar cin amanar Kwankwaso da ya yi.
Ta ce abin tambaya a nan shi ne meyasa duk tsawon shekaru da suka dauka Abba bai juya wa Kwankwaso baya ba sai yanzu.
Ta ce:
"Subhanallah, ban so na shiga cikin rigingimunsu ba amma zan iya fadan abu guda, Kwankwaso da Abba sun dade tsawon lokaci wasu har suna cewa sun kusa shekara 40.
"Tambaya ce tawa, a tsawon wannan lokaci da Abba ke tare da Kwankwaso, ya yi masa hadimi, ya yi masa Kwamishina har ya zama gwamna.
" Tambaya ta ita ce, me yasa Abba ka yi ta hakuri tsawon wannan lokaci ba ka taba cewa Kwankwaso azzalumi ba ne sai da ya daura ka Gwamna, sai da Allah ya ba ka dama ka zama kana samansa sai yanzu ka san azzalumi ne."

Source: Facebook
Mamakin da Abba Kabir ya ba Naja'atu
Naja'atu ta ce Abba Kabir ya fito daga gidan malamai amma sai dai bai yi amfani da halayen yan gidan ba.

Kara karanta wannan
Maharan da suka kashe musulmai fiye da 100 a Kwara sun shiga uku, Sojoji sun fara cika umarni
Kwararriyar 'yar siyasar mara tsoro ta ce Abba ya manta Allah a lokacin da ya yi nasara a kotu saboda Bola Tinubu ya fara godewa a jawabinsa.
"Abba daga gidan malamai ya fito, ya san Allah, amma akwai bambanci da sanin Allah da amfani da abin da Allah ya ce.
"Inda na fara sanin Abba na da matsala shi ne lokacin da kotu ta tabbatar da shi a matsayin gwamna, bai godewa Allah ba sai ya fara godewa Tinubu.
"Ya manta cewa Allah ne cikin hikimarsa ya sa aka bar masa, daga ranar da ka bar Allah, shi ma ya bar ka."
- Naja'atu Mohammed
Abba bai ci amanar Kwankwaso ba
Kun ji cewa tsohon kwamishina a Kano, Yusuf Bello Danbatta ya bayyana cewa Gwamna Abba Yusuf bai ci amanar Sanata Rabiu Kwankwaso ba da ya koma APC.
Tsohon kwamishinan ya ce Kwankwaso ne ma ya kafa al'adar sauya sheka lokacin da ya bar PDP ya koma APC da ya na kan kujerar gwamna.
Dr Yusuf Danbatta ya jaddada cewa Gwamna Abba kwararren ma'aikaci ne wanda yake da ikon zabar jam'iyyar da yake so domin cigaban Kano.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
