Sheikh Jingir Ya Fadi 'Hadarin' Ci gaba da Zaman Amupitan a matsayin Shugaban INEC

Sheikh Jingir Ya Fadi 'Hadarin' Ci gaba da Zaman Amupitan a matsayin Shugaban INEC

  • Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir ya ce naɗin Farfesa Joash Ojo Amupitan a matsayin shugaban INEC babban haɗari ne
  • Sheikh Jingir, wanda shi ne Shugaban JIBWIS ya ce Musulman Najeriya ba su aminta da nadin Amupitan ba saboda wasu dalilai
  • Fitaccen malamin addinin ya bukaci Majalisar Tarayya ta sa baki domin tabbatar da adalci da amincewar jama’a gabanin zaben 2027

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Plateau – Shugaban Majalisar Malamai na Ƙasa ta Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah (JIBWIS), Sheikh Sani Yahaya Jingir, yya soki nadin Shugaban INEC.

Malamin Musuluncin ya bayyana naɗin Farfesa Joash Ojo Amupitan a matsayin shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) a matsayin babbar barazana ga ƙasar nan.

Sheikh Yahaya Jingir ya soki nadi Amupitan a matsayin Shugaban INEC
Sheikh Sani Yahaya Jingir, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Shugaban INEC Amupitan Hoto: JIBWIS Nigeria/Bayo Onanuga/INEC
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Sheikh Jingir ya ce, dole ne a nada mai adalci da ba shi da tarihin kokarin raba kan ƙasa a matasayin shugaban INEC saboda muhimmancin hukumar.

Kara karanta wannan

INEC ta dauki bangare 1 a rikicin PDP, ta yi zama da shugabannin jam'iyyu a Abuja

Sheikh Jingir ya soki nadin Shugaban INEC

Jaridar Daily Post ta wallafa cewa Malamin ya yi wannan jawabi ne a ƙarshen taron ƙasa na shekara-shekara karo na 33 da JIBWIS ta shirya na tsawon kwanaki uku a cibiyar taro ta Saddeqa da ke Jos.

A cewarsa, Musulman Najeriya ba su aminta da naɗin Amupitan ba, ganin irin rubuce-rubucen da ake dangantawa da shi a baya na kokarin kakaba zargin kisan Kiristoci a Najeriya.

Sheikh Jingir ya ce duk da cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta sha musanta zarge-zargen, shiru da aka yi kan kiran a cire Amupitan daga muƙamin na ƙara tayar da hankalin jama’a.

Sheikh Jingir a dura kan Majalisar tarayya

Fitaccen Malamin ya jaddada cewa, idan har ana son a samu sahihin zaɓe da kowa za gamsu da shi, dole ne a guji duk wani abu da zai iya kawo rashin yarda da hukumar zaɓe.

A cikin jawabin nasa, Sheikh Jingir ya nuna damuwa kan yadda ’yan Majalisar Tarayya suka yi shiru kan batun.

Kara karanta wannan

Yadda Shugaba Tinubu ya yi wa gwamna abin da bai saba ba a fadar Aso Rock

Sheikh Jingir ya ce Musulmi ba za su aminta da Amupitan ba
Fitaccen Malamin addinun musulunci, Sheikh Sani Yahaya Jingir Hoto: JIBWIS
Source: Facebook

Ya nemi jin dalilin da zai sa wanda ake zargi da cin mutuncin Sheikh Usman Ɗanfodiyo da kuma zargin Musulmi da kisan kiyashi zai samu irin wannan muƙami mai matuƙar tasiri.

A cewarsa, INEC hukumar ce da ke buƙatar shugabanci na gari ba tare da son zuciya ko nuna wariya ba.

Malamin ya ce Musulmi ba za su amince da shugabancin wanda ake zargi da kiran ƙasashen waje su kai hari kan Najeriya ba.

Ya bayyana cewa irin wannan mutum bai dace ya riƙe muƙamin da ke da alhakin tafiyar da zaɓe a ƙasa mai yawan rikice-rikicen addini da ƙabila ba.

Sheikh Jingir ya kafa sharadin tallafa wa Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa Shugaban majalisar malamai ta Jama’atu Izalatil Bid’a Wa’ikamatis Sunnah (JIBWIS), Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya yi magana kan zaen 2027.

Ya bayyana matsayarsa kan zaɓen shugaban ƙasa na 2027, inda ya ce ba zai mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyar APC baya ba idan ba a cika wani muhimmin sharadi ba.

A wani jawabi da ya gabatar da Jos, Sheikh Jingir ya ce hakan zai faru ne idan har Shugaba Tinubu ya ƙi ci gaba da Sanata Kashim Shettima a matsayin mataimakin shugaban ƙasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng