Ministan Buhari, Dalung Ya Fadi Manyan ADC da za Su Iya Kifar da Tinubu a 2027
- Tsohon ministan matasa da wasanni, Solomon Dalung, ya ce jam’iyyar ADC na da fitattun 'yan siyasa da za su iya kalubalantar Shugaba Bola Tinubu
- Dalung ya bayyana cewa jam’iyyar ba ta rasa ‘yan takara masu nagarta ba, tare da cewa ko shi kansa na iya tsayawa takara ya kifar da Tinubu
- Ya ce jam'iyyar ADC ta riga ta cimma matsaya kan gudanar da sahihin zaben fitar da gwani da kuma mara wa duk wanda ya yi nasara baya a 2027
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Tsohon ministan matasa da wasanni, Solomon Dalung, ya ce jam’iyyar ADC na da fitattun mutane da za su iya kalubalantar shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben shugaban kasa na 2027.
A cewar Dalung, jam’iyyar ADC ba ta dogara da mutum daya tilo ba domin fuskantar siyasar 2027, ya ce suna kan manufa ta bai daya da ke da nufin kalubalantar jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya.

Source: Facebook
Dalung ya fadi hakan ne yayin da yake jawabi a shirin Sunday Politics da tashar Channels Television ke yi duk ranar Lahadi, inda ya tattauna kan makomar 'yan adawa a 2027.
ADC za ta kalubalanci jam'iyyar APC inji Dalung
Yayin jawabin da ya yi, Dalung ya ce akwai mutane da dama a jam'iyyar ADC da za su iya tsayawa takara su yaki shugaba Tinubu.
Ya ce:
“Muna da mutane da yawa da za su iya kalubalantar Tinubu,”
Tsohon ministan ya kara da cewa ko shi kansa yana iya tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027 idan bukatar hakan ta kama.
Manyan ‘yan siyasa da ke cikin tafiyar ADC
Dalung ya danganta kwarin gwiwarsa lura da da irin mutanen da suka rungumi jam’iyyar a matsayin babban dandalin hada kan 'yan adawa.
Vanguard ta rahoto ya yi nuni da cewa ADC ta samu karbuwa daga manyan ‘yan siyasa da suka hada da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi.
Sauran jiga-jigan ADC sun hada da tsohon gwamnan jihar Rivers kuma tsohon minista, Rotimi Amaechi, da tsohon gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola.

Source: Facebook
Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, John Odigie-Oyegun da tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark na cikin manyan ADC.
Ya za a yi zaben fitar da gwanin ADC?
Da yake amsa damuwar jama’a kan yiwuwar barkewar rikici sakamakon yawan manyan ‘yan siyasa a jam’iyyar, Dalung ya ce ADC ta riga ta cimma matsaya a kan yadda za a kauce wa irin hakan.
Ya bayyana cewa jam’iyyar za ta gudanar da sahihin zaben fitar gwani, inda duk wanda ya yi nasara zai samu goyon bayan kowa da kowa.
Gudaji Kazaure zai yi takara a 2027
A wani labarin, mun kawo muku cewa tsohon dan majalisar wakilai daga jihar Jigawa, Gudaji Kazaure ya ce zai yi takarar shugaban kasa a 2027.
'Dan siyasar ya bayyana cewa ya zabi fitowa ya yi siyasa a jam'iyyar hadaka ta ADC ne a 2027 domin ya kawo sauyi a Najeriya.
Hon. Gudaji ya kara da cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da Peter Obi sun zama 'iyaye' saboda haka ya kamata su ja da baya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

