Kallo Ya Koma Sama: Magoya bayan Wike da Gwamna Makinde Za Su Yi Arangama Ofishin PDP

Kallo Ya Koma Sama: Magoya bayan Wike da Gwamna Makinde Za Su Yi Arangama Ofishin PDP

  • A yau Litinin ne ake sa ran tsagin Ministan Abuja, Nyesom Wike zai bude ofishin PDP da aka garkame na Wadata Plaza da ke Abuja
  • Wannan mataki ya biyo bayan tattauna wa da aka yi tsakanin tsagin Wike da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC
  • Sai dai tsagin Tanimu Turaki SAN ya yi gargadin cewa daukar wannan mataki ya saba doka, duk abin da ya faru na wuyan yan sanda

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Ana zaman dar-dar a kan yiwuwar samun sabani tsakanin manyan PDP masu adawa a juna.

Ana tsoron bangarorin da ke goyon bayan Gwamnan Oyo, Seyi Makinde, da Ministan Abuja, Nyesom Wike za su fafata a hedkwatar jam’iyyar ta Wadata Plaza, a Abuja, yau Litinin, 9 ga watan Fabrairu, 2026.

Kara karanta wannan

Hukumar INEC ta warware batun bangaren da ta aminta da shi a jam'iyyar PDP

Magoya bayan Wike za su bude sakatariyar PDP a Abuja
Ministan Abuja Nyesom Wike da Tanimu Turaki Hoto: Lere Olayinka/Tanimu Turaki
Source: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa rikicin ya barke ne bayan kwamitin rikon kwarya da bangaren Wike ke mara wa baya ya sanar da shirin karbe iko da sakatariyar jam’iyyar.

Ana tsoron arangama tsakanin 'yan PDP

Jaridar The Cable ta wallafa cewa tsagin Wike na jam'iyyar zai karbe sakatariyar ne da taimakon ‘yan sanda, abin da ya haifar da tsoro game da yiwuwar arangama.

Sakataren PDP na bangaren Wike, Sanata Samuel Anyanwu, ya bayyana hakan bayan wata ganawar sirri da hukumar INEC.

Ya bayyana cewa bangarensu zai bude sakatariyar jam’iyyar yau Litinin, 9 ga watan Fabrairu, 2026.

Rikicin dai ya samo asali ne bayan kokarin gwada iko a tsakanin bangaren Tanimu Turaki (SAN), Seyi Makinde da Bala Mohammed ke goyon baya, da kuma tsagin Wike.

PDP: Turaki na adawa da Wike

Bangaren Turaki na ganin shi ne halastaccen shugaban PDP bayan babban taron jam'iyya da aka gudanar a Ibadan ranar 15 ga Nuwamba, 2025, duk da kotu ta soke shi.

Kara karanta wannan

Saudiyya ta yi rangwame ga attajirai game da dokar hana sayan barasa

A kokarin da aka yi a baya na shiga Wadata Plaza, rikici ya barke tsakanin bangarorin biyu, inda ‘yan sanda suka shiga tsakani.

Tsagin Tanimu Turaki ya ce bude sakatariyar PDP ya karya doka
Shugaban PDP da Tanimu Turaki Hoto: Tanimu Turaki
Source: Facebook

Mai magana da yawun kwamitin rikon kwarya, Jogudo Mohammed, ya ce an umurci ‘yan sanda su bude sakatariyar bisa hukuncin kotu.

Ya ce:

“Da zarar an kammala feshi da tsaftace ofishin, za mu fara harkokin taron jam’iyya a nan."

Wata majiya daga kwamitin rikon kwarya ta kara da cewa INEC, Sufeto Janar na ‘yan Sanda, DSS da sauran hukumomi sun samu kwafin hukuncin kotun Ibadan.

Ta bayyana cewa don haka za a cire shingayen da ke Wadata Plaza kuma ayyuka za su koma daidai.

Sai dai sakataren yada labarai na kasa, Ini Ememobong, ya ce duk abin da ya faru yau, alhakin zai rataya a wuyan ‘yan sanda, ganin cewa shari’ar tana gaban kotu.

Tsagin Turaki ya dauki zafi a PDP

A wani labarin, mun wallafa cewa Kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) ta jam’iyyar PDP da Kabiru Tanimu Turaki ke jagoranta, ta soki hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC).

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya kausasa harshe kan harin 'yan ta'adda a Kwara, ya dauki mataki

Bangaren na Turaki ya yi sukar ne bisa amincewa da kwamitin rikon kwarya da Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ke mara wa baya.

Sakataren yada labarai na jam'iyyar PDP na kasa, Ini Ememobong ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, 5 ga watan Fabrairun 2026.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng