'Yar Tsohon Shugaban Kasa Ta Ayyana Shiga Takarar Gwamna bayan Komawa APC

'Yar Tsohon Shugaban Kasa Ta Ayyana Shiga Takarar Gwamna bayan Komawa APC

  • Farfesa Iyabo Obasanjo ta koma APC tare da bayyana aniyarta ta tsayawa takarar gwamna a zaɓen shekarar 2027 da ke tafe
  • Tsohuwar sanatar ta ce matsin lambar magoya baya ne ya sa ta dawo siyasa bayan kusan shekaru 15 da watsar da ita
  • Iyabo ta jaddada cewa APC ce 'gidanta na gaskiya', ta kuma yi watsi da komawa PDP ko ADC masu adawa a Najeriya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abeokuta, Ogun - Farfesa Iyabo Obasanjo, ’yar tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo, ta bayyana aniyarta ta tsayawa takarar gwamna.

Iyabo ta bayyana cewa za ta tsaya takara ne a zaben gwamnan Jihar Ogun a 2027 a ƙarƙashin jam’iyyar APC mai mulki.

Yar Obasanjo za ta tsaya takarar gwamna
Yar tsohon shugaban kasa, Iyabo Obasanjo. Hoto: Iyabo Obasanjo.
Source: Twitter

Iyabo Obasanjo ta bayyana haka ne a ranar Asabar 7 ga watan Faburairrun 2026 yayin wata tattaunawa kai tsaye a shirin rediyo na 103.7FM Eagle7 Sports, wanda Daily Trust ta bibiya.

Kara karanta wannan

Kalaman Kwankwaso na taimaka wa Abba Kabir a shari'ar 2019 sun jefa shi a matsala

Iyabo Obasanjo ta watsar da siyasa a baya

Majiyoyi sun ruwaito cewa Iyabo ta dawo harkar siyasa bayan kusan shekaru 15 da janyewa, inda ta shiga APC gabanin babban zaɓen 2027 a jihar Ogun.

Majiyoyi sun shaida cewa tsohuwar sanatar, wacce ta wakilci mazabar Ogun ta Tsakiya daga 2007 zuwa 2011, ta halarci shirin rajistar APC a Ibogun a karamar hukumar Ifo, wanda hakan ya tabbatar da shigarta jam’iyyar.

Iyabo Obasanjo, ƙwararriyar masaniya ce a fannin ilimin cututtuka kuma tsohuwar Kwamishiniyar Lafiya ta Jihar Ogun, ta sha kaye a yunƙurin sake zaɓe a 2011 a hannun Sanata Gbenga Obadara na jam’iyyar ACN a wancan lokaci.

Iyabo Obasanjo za ta yi takarar gwamna
Yar tsohon shuaban kasa a Najeriya, Iyabo Obasanjo yayin ganawa da manema labarai. Hoto: Osigwe Omo-Ikirodah.
Source: Facebook

Iyabo ta dawo siyasa, za ta yi takara

Da take magana a hirar, Iyabo ta ce dawowarta siyasa ta samo asali ne daga matsin lambar magoya bayanta.

Ta ce:

“Wata ƙungiya ce da ban kafa ba, ban tara su ba, amma sun shafe kusan shekaru biyu suna aiki. Daga baya suka fara ce min, ‘ke ce mafi dacewa, muna so ki dawo.’”

Kara karanta wannan

Shaidar EFCC ta yi bayani kan alakar Yahaya Bello da zargin almundahar N80bn

Tsohuwar kwamishinar ta ce ba za ta iya komawa jam’iyyar PDP ba saboda rikice-rikicen da ke addabar jam’iyyar.

Ta kuma bayyana cewa jam’iyyar ADC ta kasance wata hanya, amma ta ce har yanzu jam’iyyar ba ta shirya tsaf ba, cewar Vanguard.

Iyabo ta jaddada cewa duk mutanen da suka taimaka mata dawowa siyasa yanzu suna cikin APC, kuma bayan shawarwari, ta yanke shawarar shiga jam’iyyar.

Ta ce:

“APC ita ce gidana na gaskiya. Ba ni da wata gaba da kowa a jam’iyyar. Ina jin daɗi da kwarin gwiwa a cikinta.”

Game da burinta, Iyabo ta bayyana cewa ba za ta koma Majalisar Dattawa ba, inda ta ce kujerar gwamna kaɗai ce dalilin dawowarta siyasa.

Minista zai tsaya takarar gwamna a Bauchi

A wani labarin, yayin da ake tunkarar zaben 2027, 'yan siyasa a Bauchi sun fara neman hadin kan al'umma domin samun nasara a babban zaben mai zuwa.

A APC, ana hasashen Yusuf Tuggar da Ali Pate na iya tsayawa takarar gwamna, yayin da a PDP ake tunanin wasu yan takara da dama.

Ministan lafiya, Ali Pate, ya bayyana sha'awarsa ta tsayawa takarar gwamna a 2027, yana mai cewa ya shirya yi wa Bauchi hidima.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.