Muhimman abubuwa 6 da Iyabo Obasanjo ta fadi ma babanta a sabuwar wasikarta gareshi
Tsohuwar Sanata kuma diya ga tsogon shugaban kasa Obasanjo, Dr. Iyabo Obasanjo ta rubuta wasikar mayar da martani ga Obasanjo kan wasikun daya rubuta inda yake sukar shugaba Muhammadu Buhari. Ga wasu muhimman abubuwa guda shida da wasikar ta kunsa kamar yadda muka samo daga jaridar Daily Trust.
1) Kamar sauran yan Najeriya, na yarda cewa akwai matsalolin da ke adabar kasar amma ba kaine ya dace ka fade su ba don ba zan manta ba lokacin da nake kwamishinan lafiya a jihar Ogun nayi tattaki zuwa Abuja inda na bukaci kayi watsi da neman zarcewa karo na uku amma baki saurareni ba.
2) Na sake bijiro da batun hana ka zarcewa amma 'yan korar ka sukayi kunnen uwar shegu da maganata kuma ka biye musu. Abin mamaki ne kuma wai kaine yanzu saboda son kai kuma kake kushe wani don yana son zarcewa mulki.
DUBA WANNAN: Sojin Amurka 12 da suka horas da sojin Najeriya sun bayar da labarin zaman su a Jaji
3) Duk wanda ya zauna da kai koda na lokaci kadan ne zai gane cewa abinda kafi kauna a rayuwarka shine kaji ana yabon ka. Hakan yasa mutane suke rudarka ta hanyar yaba maka don su samu abinda suke so. Mu kuma iyalan ka da bamuyi maka irin yabon da suke maka, kayi watsi da mu sai yan kalilan cikinmu da suka gano hakan kuma suke maka dabara kamar sauran al'umma.
4) Mafi yawancin 'yan Najeriya suna tunanin komi aka shirya akwai wata makarkashiya ko mumunan nufi cikin ta saboda suna tunanin kowa daya yake dasu. Ban rubuta wannan wasikar don goyon bayan Jonathan, APC ko wata kungiya ba kawai na rubuta ne saboda in bayyana wa Ubangiji abin da ke zuciyata. Bana mamakin yadda kake ta tsula tsiyarka kuma babu wanda ya taka maka birki, 'yan Najeriya sun sami shugabani dai-dai da irin halayensu ne.
5) Abin takaici ne yadda kake sukar shugaban kasa Muhammadu Buhari don yana aikata irin abin da kayi lokacin da kake mulkin Najeriya.
6) Ina cikin jirgin sama a hanya ta na zuwa Abuja daga Lagos a lokacin da ake batun zarcewar ka karo na uku, sai wani daga cikin magoya bayan ka yace min "Obasanjo ne kadai zai iya mulkin Najeriya". Sai na amsa shi da cewa: "Allah bai hallici wata kasa da mutum daya ne kawai zai iya mulkinta ba domin hakan ba abu mai dorewa bane saboda wata rana zai mutu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng