Obasanjo: Na kamu da COVID-19 amma ban ji alamar komai ba a jikina har na warke

Obasanjo: Na kamu da COVID-19 amma ban ji alamar komai ba a jikina har na warke

- Tsohon shugaban kasar Najeriya Obasanjo ya bayyana yadda ya kamu da cutar COVID-19

- Tsohon shugaban yace tun daga kamuwarsa, bai ji alamar yana dauke da wata ctar ba a jikinsa

- Ya kuma tabbatar da cewa a halin yanzu ya warke, amma bai ji a jikinsa ya alamun cutar take ba

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a ranar Juma’a ya bayyana cewa ya yi gwajin kwayar cutar Coronavirus, Daily Trust ta ruwaito.

Ya sanar da labarin ne a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, yayin da yake magana a wani taron tattaunawa da aka shirya don bikin cikawarsa shekaru 84 da haihuwa.

Shirin an gudanar dashi ne a cikin dakin karatun shugaban kasa na Olusegun Obasanjo (OOPL), Abeokuta.

Obasanjo, wanda ya ce ya ɗan damu game da hakan, ya kara da cewa dole ne ya yi kira ga 'yarsa, Dokta Iyabo Obasanjo-Bello, masaniyar annoba.

KU KARANTA: Gwamnan jihar Gombe ya rantsar da dan marigayi Mai Tangale a matsayin kwamishina

Obasanjo: Na kamu da COVID-19 amma ban ji alamar komai ba a jikina har na warke
Obasanjo: Na kamu da COVID-19 amma ban ji alamar komai ba a jikina har na warke Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Obasanjo ya ce, “Zai ba ku mamaki cewa na yi gwajin cutar COVID-19. Na kira su su zo su gwada ni, sun zo ranar Asabar, ban samu sakamakon gwajin ba har zuwa ranar Laraba kuma ya fito tabbatacce cewa na kamu amma ban ga wata alama ba.

“Lokacin da suka zo kwana uku bayan haka, sai suka gwada ni suka ce ba ni da cutar, wato kwana uku bayan na yi gwajin cewa na kamu da cutar.

“Diyata, Iyabo masaniyar cututtukan annoba ce kuma na kira ta don ta yi min bayani, ta ce watakila sun gwada ni ne a matakin baya na kasancewa na kamu.

“Na fada mata bani jin wata alamar cuta kuma ta ce hakan na iya zama mummunan sakamako. Amma tabbas na kamu. Tun daga wannan lokaci an gwada ni sau uku kuma gwajin ya dawo cewa bani dashi. Don haka, idan kuna so ku zo kusa da ni, kuna iya zuwa kusa da ni.

"Ba wani abin damuwa ba ne, lokacin da na tabbatar da na kamu, sai iyalina suka guje ni, na ce musu su zauna a wurinsu yayin da ni kuma na kasance a kebe."

KU KARANTA: Buhari ga sabbin Hafsoshin tsaro: Kwanakin kadan gareku ku daidaita kasar nan

A wani labarin, Shugaban jami’ar Adeleke, Farfesa Solomon Adebiola, ya bayyana cewa riga-kafin kwayar cutar COVID-19 da masana kimiyya na Najeriya suka kirkiro a halin yanzu tana matakin gwaji na asibiti, Vanguard News ta ruwaito.

Ya kara da cewa allurar, wacce Hukumar Lafiya ta Duniya ta amince da ita kuma ta sami goyon bayan Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya ta samu ne daga wani masanin kimiyya daga Jami’ar Adeleke, Dokta Oladipo Kolawole, tare da hadin gwiwar wasu daga wasu jami’o’i biyar na kasar.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel