Wata Sabuwa: An Yi Musayar Kalamai Rigima Ta Barke tsakanin APC da Tsohon Shugabanta na Kasa

Wata Sabuwa: An Yi Musayar Kalamai Rigima Ta Barke tsakanin APC da Tsohon Shugabanta na Kasa

  • An yi musayar yawu tsakanin jam'iyyar APC reshen jihar Edo da tsohon shugabanta na kasa, Cif John Odigie-Oyegun
  • Shugaban jam'iyyar APC reshen jihar Edo ya yi zargin cewa Oyegun wanda yanzu ya koma ADC, ya ki biyan basussukan da jam'iyyar ta biyo shi
  • Sai dai, wannan zargin ya jawo Oyegun ya fito ya mayar da martani mai zafi ga jam'iyyar wadda a baya ya kasance shugaba a cikinta

​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Edo - Jam’iyyar APC a jihar Edo ta buƙaci tsohon shugabanta na na ƙasa kuma tsohon gwamnan jihar Edo, Cif John Odigie-Oyegun, da ya biya bashin da ake zargin an biyo shi.

APC ta jihar Edo ta ce bashin ya samo asali ne daga lamuni da kuma kuɗaɗen rajista da kuɗin zama mamba da suka taru tsawon shekaru, a lokacin da Oyegun yake matsayin mamba na jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Ta fashe: An cafke malaman Musulunci 2 kan zargin jibgar almajiransu har da makami

APC ta yi musayar yawu da John Odigie-Oyegun
Tsohon shugaban APC na kasa kuma jigo a ADC, John Odigie-Oyegun Hoto: @DeeOneAyekotoo
Source: Twitter

Jaridar Leadership ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban APC na jihar Edo, Emperor Jarrett Tenebe, ya sanya wa hannu a ranar Alhamis, 5 ga watan Fabrairun 2026.

APC ta yi zargi kan tsohon shugabanta

Jam’iyyar ta yi ikirarin cewa Oyegun ya ki ba da amsa kan bukatun biyan bashi da dama da aka tura masa a hukumance, inda ta ce jimillar bashin ya haura Naira miliyan 150.

"Jam’iyyar APC a jihar Edo na sanar da al’umma cewa, a matsayin jam’iyya mai bin doka kuma mai kula da muradun jama’a, mun buƙaci a hukumance a biya bashin da ake bin jagora a ADC, Cif John Odigie-Oyegun."

- Jarrett Tenebe

A cewar Tenebe, bashin ya haɗa da lamunin da ake zargin an ba Oyegun a lokacin da yake shugaban APC na ƙasa, da kuma kuɗaɗen zama mamba da aka ce bai biya ba tsawon lokacin da yake cikin jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Bangaren Turaki ya yi bambami bayan INEC ta watsa musu kasa a ido

Wane martani John Oyegun ya yi?

Da yake mayar da martani kan zargin, John Odigie-Oyegun ya musanta dukkanin ikirarin, yana mai bayyana su a matsayin tuhume-tuhume marasa tushe da ke nuna firgici da fargaba a cikin APC mai mulki.

Odigie-Oyegun, wanda ya taɓa zama gwamnan farar hula na jihar Edo, ya ce zargin ya samo asali ne daga damuwar da ta kama APC sakamakon fitowar ADC a matsayin jam'iyyar siyasa mai karfi a kasa, jaridar The Nation ta kawo labarin.

"Mutane za su yi dariya. Abin da zan iya faɗa kawai shi ne, duk da rashin kyawun abin da suke yi, hakan ya nuna cewa sun fahimci suna da matsala tun bayan bayyanar ADC.”

- John Odigie-Oyegun

Oyegun ya yi jam'iyyar APC martani
John Odigie-Oyegun a wajen taron jam'iyyar ADC Hoto: @ADCVanguard
Source: Twitter

Oyegun ya ce APC na tsoron ADC

Tsohon gwamnan ya zargi APC da mayar da martani ga bunƙasar ADC da ƙiyayya da tashin hankali, maimakon mu’amalar siyasa mai ma’ana da gasa ta gaskiya.

"Yanzu sun san suna cikin matsala. Mun shirya musu. Duk abin da za su yi, mun shirya. A karshe sun amince cewa akwai barazana gare su a Najeriya.”

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya girgiza kan harin 'yan ta'adda a Kwara, ya ba gwamnati mafita

John Odigie-Oyegun

APC ta kafa babban kwamitin taron jam'iyya

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta fara shiri domin gudanar da babban taronta na kasa.

Jam'iyyar APC ta kafa kwamiti domin shirye-shiryen babban taronta na kasa wanda aka shirya gudanarwa a ranakun 27 da 28 ga watan Maris na shekarar 2026.

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, wanda ya taba jagorantar APC shi ne ya zama sakataren kwamitin da ke shirya babban taron.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng