"Ba Zan Zama Mataimakin Atiku ko Kwankwaso ba," Obi Ya Fadi Shirinsa kan 2027
- Peter Obi ya bayyana cewa babban kudurinsa shi ne ya tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027 bayan ya koma jam’iyyar ADC
- Tsohon gwamnan na Anambra ya yi watsi da kiraye-kirayen zama mataimakin Atiku Abubakar, ko Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
- Obi ya jaddada cewa kujerar shugaban kasa yake so yayin da ya fadi shirye-shiryen da yake yi don tabbatar da cikar wannan buri nasa
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar LP, Peter Obi, ya ayyana cewa zai fafata a zaɓen 2027 don neman kujerar da Shugaba Bola Tinubu yake a kanta yanzu.
Tsohon gwamnan na Anambra ya bayyana cewa ba shi da niyyar zama abokin takarar kowa a babban zaɓen ƙasar nan dake tafe.

Source: Facebook
Obi ya yi wannan bayanin ne yayin yakin neman zaɓen ɗan takarar ADC na shugabancin ƙaramar hukumar AMAC a birnin Abuja, in ji rahoton Daily Trust.
Sauya shekar Peter Obi zuwa jam'iyyar ADC
Kwanan nan ne tsohon gwamnan ya fice daga jam'iyyar LP ya koma jam'iyyar hadakar 'yan adawa ta ADC domin tunkarar zaɓen shekarar 2027.
Tun bayan hakan, magoya bayansa na Obidient Movement suka fara matsa lamba ga ADC domin ta ba shi tikitin takarar shugabancin ƙasa kai-tsaye.
Wasu daga cikin mambobin ƙungiyar sun nace cewa sai dai a tsayar da Obi, idan ba haka ba su janye goyon bayansu ga jam'iyyar.
Sakataren yaɗa labarai na ADC, Mallam Bolaji Abdullahi dai ya fito ya gargaɗi magoya bayan da su guji kalaman tunzuri dake raba kan jam'iyya.
Jita-jitar kawance da Atiku ko Kwankwaso
Akwai rahotannin cewa wasu jiga-jigan 'yan siyasa na shirin haɗa tikitin Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso a inuwar jam'iyyar ADC.
Haka kuma, ana rade-radin cewa za su iya komawa wata jam'iyyar idan har Atiku Abubakar ya samu nasarar karɓar tikitin ADC.
Kin komawar Kwankwaso jam'iyyar APC ya ƙara rura wutar jita-jitar cewa akwai wani kawance da ke shirin ƙulluwa tsakaninsa da Peter Obi.
A ɗaya ɓangaren, magoya bayan Atiku suna kira ga Obi da ya yarda ya zama abokin takarar Atiku kamar yadda aka yi a 2019.

Source: Facebook
'Shugaban kasa zan nema' - Peter Obi
A cikin wani faifan bidiyo da ya karade yanar gizo, Obi ya bayyana a fili cewa shi ne zai zama babban ɗan takarar shugaban kasa a 2027, in ji rahoton Reuben Abati.
Obi ya gaya wa magoya bayansa cewa:
“Ina nan daram kuma zan tsaya takarar shugaban kasa, kujera lamba ɗaya a kasar nan. Idan lokaci ya yi za ku gani.”
Ya ƙara da cewa:
“Goyon bayanku a AMAC yana da matuƙar muhimmanci ga tafiyarmu. Ina tabbatar muku zan tsaya takarar matsayin lamba ɗaya.”
Wannan furuci nasa ya nuna cewa Peter Obi ba zai amince da tayin zama mataimakin tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ba.
'Abin da zai faru da Obi a ADC' - Bwala
A wani labari, mun ruwaito cewa, Daniel Bwala, Mai ba shugaban kasa Bola Tinubu shawara na musamman kan yada manufofi, ya yi magana kan Peter Obi.
Daniel Bwala ya ce yana da yakinin cewa Peter Obi ba zai zama ɗan takarar shugaban kasa ko mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar ADC ba.
Hadimin shugaban kasan ya yi ikirarin cewa Peter Obi ba shi da karfin jagoranci da zai ba shi damar zama jagora na kowace haɗakar jam’iyyun siyasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


