'Masu Tunanin 'Yan Arewa ba Za Su Zabi Tinubu a 2027 ba Sun Tafka Babban Kuskure'
- Tsohon shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje ya ce babu wanda ya dace mutane su sake zaba a 2027 kamar Bola Ahmed Tinubu
- Ganduje ya ce masu tunanin cewa 'yan Arewa za su juyawa Shugaba Bola Tinubu baya a zabe mai zuwa sun tafka babban kuskure
- Tsohon gwamnan Kano ya fadi haka ne lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin matasa daga jihohin Arewa 19 a birnin tarayya Abuja
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa wadanda ke tunanin cewa 'yan Arewa ba za su sake zaben Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba a 2027 suna "tafka babban kuskure."
Ganduje ya fadi hakan ne a ranar Juma’a a birnin Abuja, lokacin da shugabannin matasan Arewa daga jihohi 19 suka kai masa ziyarar ban girma domin nada shi a matsayin uban kungiyarsu.

Source: Facebook
A rahoton Daily Trust, tohon gwamnan jihar Kano ya ce babu wani dan takara da ya fi dacewa ya mulki Najeriya bayan 2027 daga Kudancin Najeriya kamar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Ya kara da cewa Najeriya ta yi sa’ar samun "ainihin dan siyasa" mai kishin kasa a matsayin shugaba.
Jawabin Abdullahi Ganduje kan zaben 2027
Game da zabe mai zuwa na 2027, Ganduje ya ce:
"Dangane da zabe mai zuwa na 2027, wadanda ke raya wa kansu ko tunanin cewa Arewa za ta zabi wani dan takara daban ba Asiwaju ba, sun tafka babban kuskure."
"Wannan ne karon farko da Najeriya ta yi sa’ar samun dan siyasa nagari a matsayin Shugaban Kasa. Siyasa ce tushensa, kuma a cikinta aka raine shi saboda ya yi imani da hadin kan kasar nan.
"Ma'ana dai ya sha gwagwarmaya, har gudun hijira ya tafi domin ganin dorewar dimokuradiyya a Najeriya. Don haka, babu wanda ya fi dacewa a zaba a 2027 sama da Bola Ahmed Tinubu."
Yarjejeniyar da aka yi kafin zaben Buhari
Ganduje ya tunatar da cewa an yi yarjejeniya tun kafin zaben marigayi Shugaba Muhammadu Buhari cewa bayan shekaru takwas na mulkinsa, mulki zai koma Kudu, in ji Vanguard.
Ya bayyana cewa ko da yake Asiwaju bai kai shekaru hudu a kan mulki ba, an ga matakan garambawul da ya dauka domin inganta tattalin arziki da jin dadin jama'a.

Source: Twitter
Ganduje ya kuma jinjina wa shugabannin matasan Arewan saboda jajircewarsu, ba wai kawai wajen tara kuri’u ba, har ma da shirin tara kudi domin sayan fom din takarar Asiwaju.
"Babu wata sadaukarwa da ta wuce wannan; kuna ba da kudi, kuna ba da tunaninku, kuna ba da karfinku, sannan kuna ba da lokacinku domin tabbatar da tazarcen Asiwaju. Dole ne mu gode muku kan wannan aiki," in ji Ganduje.
Matasan Arewa na tare da Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa Kungiyar Matasan Arewa (NYF) ta yi magana kan tazarcen shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaben shekarar 2027.
Kungiyar ta bayyana cewa Arewa za ta mara wa Shugaba Tinubu baya domin ya sake samun wa’adi na biyu a zaben shugaban kasar 2027.
Matasan sun danganta matsayar ta da sauye-sauyen da Shugaba Tinubu ke aiwatarwa da jajircewarsa wajen tabbatar da haɗin kan ƙasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


