‘Abin da Zai Hana Musulmi ’Yan Arewa Zaben Shugaban Kasa’: Jigon APC Ya Yi Gargadi
- Jigo a APC, Farouk Aliyu, ya bayyana abin da yake ganin zai zabe saboda rashin jin daɗin tikitin shugaban ƙasa
- Ya ce yawan Musulmi a Arewa ne ke yanke makomar siyasa, inda ya gargadi APC kan illar sauya Musulmi da Kirista
- Aliyu ya jaddada cewa rikicin tikitin Musulmi–Musulmi na 2023 ya lafa, kuma ba a nuna fifiko ga Musulmi a mulkin Bola Tinubu ba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja – Wani jigo a jam’iyyar APC, Farouk Aliyu, ya yi magana game da zaben 2027 da kuma tikitin Musulmi da Musulmi.
Kusa a APC ya ce yankin Arewa ba zai ji daɗin tikitin shugaban ƙasa da mataimaki Kirista da Kirista ba, yana mai gargadin cewa hakan na iya jefa jam’iyyar cikin matsala.

Source: Twitter
Jigon APC ya yi gargadi kan sauya Shettima

Kara karanta wannan
Buba Galadima ya kawar da NNPP, ya faɗi jam'iyyar da za ta kayar da Tinubu a 2027
Aliyu ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin wata hira da ya yi a gidan talabijin na ARISE TV da aka wallafa a Yutube inda yake mayar da martani kan muhawarar ko APC za ta ci gaba da tikitin Musulmi–Musulmi.
Da yake dogaro da yanayin yawan jama’a a Arewa, jigon na APC ya ce jam’iyyar za ta yi la’akari da ƙididdigar yawan masu zaɓe wajen yanke shawarar irin tikitin da za ta fitar.
Ya ce:
“A ganina, za a duba yawan mutane ne wajen tantance ko za a tsayar da Musulmi ko Kirista, lambobin suna nan a fili.”
Farouk Aliyu ya ƙara da cewa babu shakka Musulmi sun fi yawa a Arewa, inda ya ce duk jam’iyyar da ke son cin nasara dole ta yi la’akari da haka.
Ya gargadi APC cewa sauya ɗan takara Musulmi da Kirista a Arewa na iya janyo wa jam’iyyar ƙalubale a zaɓe.
“Ko a Arewa akwai Musulmi fiye da Kiristoci, babu shakka hakan gaskiya ne. Don haka jam’iyya na iya tsayar da Kirista, amma idan aka duba yawan jama’a, Musulmi sun fi yawa a Arewa, kuma hakan ne mafi alheri ga jam’iyyar ta tsayar da Musulmi.
“Tabbas, idan ka cire Musulmi ka saka Kirista a Arewa, za a shiga matsala."
- Farouk Aliyu

Source: Twitter
'Ba a yi wa Kiristoci wariya'
Aliyu ya kuma ce ce-ce-ku-cen da suka biyo bayan tikitin Musulmi–Musulmi a 2023 sun riga sun lafa, yana mai jaddada cewa Kiristoci ba sa fuskantar wariya a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Tinubu.
Ya ce:
“Wannan gwamnati ba ta da wani abin da za a nuna cewa tana fifita Musulmi a kan Kiristoci, don haka ina ganin tikitin Musulmi–Musulmi har yanzu na iya yin tasiri a APC.
“Dangane da Arewar da na sani, Arewa ba za ta ji daɗin tikitin Kirista–Kirista ba, domin idan aka yi haka, za a ware Musulmi gaba ɗaya a Arewa."
Yan APC sun gargadi sauya Shettima a 2027
A wani labarin, Kungiyar APC Youth Parliament North East ta yi karin haske game da jita-jitar da ake yadawa kan maganar sauya Kashim Shettima.
Shugaban kungiyar, Kabiru Garba Kobi daga Bauchi, ya zargi wasu 'yan siyasa da yada rade-radin saboda cimma burinsu.
Kabiru Kobi ya bayyana haka yayin da yake nuna damuwa game da jita-jitar sauya Shettima a ranar Lahadi 25 ga watan Janairun 2026 da muke ciki.
Asali: Legit.ng
